Taragon farko na
miliyoyin kayayyakin gwaji da na kariya daga cutar Coronavirus wadanda attajirin nan dan kasar China, Jack Ma ya yi alkawarin bai wa kasashen Afirka - sun iso kasar
Habasha.
Ana sa ran za a yi amfani da kayayyakin wajen yaki da
cutar coronavirus a kasashe Afrika 54.
Kayayyakin sun iso Habasha ne daga
birnin Guangzho na China.
Mista Ma wanda shi ne ya kafa kamfanin Ali Baba, ya yi
alkawarin bai wa kowacce kasa a Afrika rigar kariya guda dubu daya, da injinan
gwaji guda dubu 20 da kuma abin kare fuska guda dubu 100,000 a matsayin
gudunmuwarsa wajen yaki da Covid-19.
A yanzu haka a nahiyar Afirka akwai mutane fiye da
1,000 dauke da cutar a kasashe 43.
Tuni Mista Ma ya bada gudunmuwa irin haka ga Amurka da
wasu kasashen Turai da na Asiya domin kawo karshen yaduwar cutar Coronavirus.