Abubuwan da suka faru a Najeriya da Nijar da sassan duniya
Wannan shafin yana kawo muku labarai da rahotannin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma wasu sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Nasidi Adamu Yahaya and Nabeela Mukhtar Uba
Za a gudanar da sabon zabe a Malawi
Majalisar dokokin Malawi ta amince da dokar da ta sanya 19 ga Mayun 2020 a matsayin ranar gudanar da sabon zaben shugaban kasa.
A farkon watan nan kotun kundin tsarin mulkin kasar ta soke zaben da aka gudanar a watan Mayu wanda ya bai wa Shugaba Peter Muthirika nasara saboda zargin magudin zabe.
Wasu 'yan takara biyu - Lazarus Chakwera da Saulos Chilima wadanda lauyoyinsu suka ce an yi magudi sannan kuma jami'an da ke aikin zaben sun yi kuskure wajen aike kwafin takardar sakamakon zaben zuwa ga cibiyar tattara sakamakon.
Sabuwar dokar da aka amince da ita ranar Litinin ta kunshi gudanar da zagaye na biyu na zaben idan babu dan takarar da ya samu kashi 50.
Asalin hoton, AFP
Sojojin Turkiyya biyu sun yi 'shahada a Libya'
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce sojin kasarsa biyu sun mutu a yakin da ake yi a Libya, inda sojin suka je domin tallafa wa gwamnatin da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin duniya.
Gwamnatin tana yaki da dakarun da Janar Khalifa Haftar ke jagoranta a gabashin Libya.
Janar Haftar yana samun goyon bayan kasashen Masar, Russia, Saudi Arabia, hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Jordan, yayin da gwamnatin kasar ke samun taimakon Turkiya da Qatar.
"Sojojinmu biyu sun yi shahada a Libya," a cewar Shugaba Erdogan.
Tun 2011 ke cikin yaki bayan tumbuke shugabanta Muammar Gaddafi daga kan mulki.
Shugaban Faransa ya “ci mutuncin” shugaban Kamaru
Matasa da dama ne suka yi zanga-zanga a wajen ofishin jakadancin
Faransa da ke, Yaoundé, babban birnin Kamaru sabodakalaman "muzantawa" da shugaban
Faransa Emmanuel Macron ya yi kan Shugaba Paul Biya.
Hakan ya faru ne
bayan wani bidiyo da ya watsu a shafukan sada zumunta a karshen mako ya nuna
Shugaba Macron yana shaida wa wani mai fafutuka dan kasar a Paris cewa ya matsa
lamba kan Mr Biya domin sako shugaban ‘yan
hamayyar kasar Maurice Kamto – wanda aka sako shi daga kurkuku wata tara bayan
an kama shi a watan Oktoba na 2019.
A cikin bidiyon, an ji Shugaba Macron yana cewa “akwai hakkokin dan
adam” da ake takawa fiye da misali a kasar
Kamaru – ya yi kalaman ne kwanaki kadan bayan ‘yan bindiga sanye da kakin soji
sun kasha mutum 22 a kauyen Ngarbuh da
ke Arewa maso Yammacin kasar.
Mr Macron ya shaida
wa mai fafutukar cewa "Zan kira Shugaba Biya makon gobe kuma zan matsa
masa lamba sosai ta yadda za a kawo karshen wadannan matsaloli." .
Sai dai kalaman basu
yi wa gwamnatin Kamaru dadi ba.
Wani mai zanga-zanga ya ce "Muna
kaunar shugabanmu. Mutum ne mai son zaman lafiya."
Babu wani darasi da
Faransa za ta koya wa Kamaru kuma dole Macron ya nemi afuwa saboda cin mutuncin
da ya yi cewa shugabanmu dan barandarsa ne," a cewar wani mai zanga-zangar.
Wani kuma ya rike kwalin da aka rubuta cewa ya kamata Macron ya
rika girmama dattawa, yana mai cewa Kamaru kasa ce mai cin gashin kanta.
Mai fafutukar, Yvone Mumah Biya, ya ce gwamnatin Kamaru ce ta
daukki nauyin masu zanga-zangar.
Bayanan hoto, Wani mai zanga-zanga ya ce "Muna kaunar shugabanmu. Mutum ne mai son zaman lafiya."
Farawa
Da fatan kuna nan cikin koshin lafiya. Muna kuma fatan za ku kasance tare da mu domin sanin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da makwabtansu, har da da wasu sasssan duniya.
Rufewa
A nan muka kawo karshen labarai da rahotanni da muke kawo muku daga kasashen Najeriya da Nijar da makwabtansu, da ma wasu sassan duniya. Sai kuma gobe idan Allah a kai mu.
Ku duba kasa domin karanta labaran da muka wallafa. Kazalika za ku iya karanta sauran labaran a babban shafinmu: bbchausa.com ko kuma shafukan sada zumunta.
Buhari ya nada kwamitin sa ido kan ayyukan jinkai
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada kwamitin da zai rika sanya ido kan ayyukan jinka a kasar.
Wata sanarwa da ya wallafa a shafin Twitter, shugaban kasar ya ce kwamitin zai shige gaba wajen tsara ayyukan jinkai, da tsaron masu bayar da jinkai da kuma sulhunta rashin jituwar da ka iya tasowa tsakanin jami'an tsaro da kungiyoyin bayar da jinkai a kasar.
A cewar shugaban kasar, kwamitin zai tsara yadda za a bayar da jinkai ga al'umomin da suka fuskanci matsalolin da ke bukatar samun agajin.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Farashin gwal ya tashi saboda coronavirus
Farashin gwal ya yi tashin da bai taba yi ba cikin shekara bakwai saboda masu zuba jaria a gwal suna janye wa daga China suna zuwa inda ba za su fuskanci matsala game da lafiyarsu ba.
Farshin gwal ya tashi da kashi biyu cikin dari, a karon farko tun watan Fabrairu na 2013.
Farashin gwal daya ya kai $1,678.58 kafin ya sake saukowa.
Asalin hoton, AFP
Bayanan hoto, Farashin gwal daya ya kai $1,678.58 kafin ya sake saukowa.
Za a samar da wuraren gwajin ingancin kayayyaki a Najeriya
Hukumar kula da ingancin kayayyaki a Najeriya ta ce ta kammala tsare-tsare na gina wuraren gwajin ingancin kayayyaki da tabbatar da nagartarsu a shiyyoyin kasar guda shida.
Ta ce za ta yi haka ne domin tabbatar da cewa kayayykin sun cika duk wata ka'ida da aka gindaya kafin ba da tkardar shaidar ingancinsu.
Hukumar ta kuma ce makasudin gina wuraren shi ne a tabbatar da cewa kayayyakin da ake samar wa sun karbu a fadin duniya.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Firai ministan Malaysia mai shekara 94 ya yi murabus na ba-zata
Firai ministan Malaysiar, mai shekara 94, Mahathir Mohamad, ya mika takardar murabus dinsa ga sarkin kasar.
Murabus din Mr Mahathir, wanda ya girgiza 'yan kasar, ya faru ne a yayin da ake rade radin cewa zai kafa gwamnatin hadaka ba tare da mutumin da ake tunanin zai gaje shi ba, Anwar Ibrahim.
Shi ne firai minista mafi yawan shekaru a duniya kuma ya hau kan mulki ne a 2018.
A nasarar zaben da ya samu mai cike da ban mamaki, ya kawar da firai minista na wancan lokaci Najib Razak, wanda aka zarga da almundahanar biliyoyin dala.
Ofishin firai ministan ya ce Mr Mahathir ya mika takardar murabus din ne da misalin karfe shida na safe a agogon Najeriya da Nijar.
Ba a yi cikakken bayani kan abin da takardar ta kunsa ba.
Ba a san mutumin da zai gaje si ba, ko kuma za a sake gudanar da zabe.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Ba a yi cikakken bayani kan abin da takardar ta kunsa ba.
BBC za ta bude kyautar Komla Dumor ta 2020
BBC na neman 'yan jarida masu tasowa 'yan Afirka domin bayar da lambar girmamawa ta Komla Dumor kan aikin jarida karo na shida.
Ana gayyatar 'yan jarida a fadin Afirka su nemi damar shiga gasar wadda ke fatan zakulowa da kuma tallata sabbin masu basira daga Afirka.
Wanda ya yi nasara zai yi aikin wata uku a hedikwatar BBC da ke Landan, inda zai yi kwas din sanin sabbin makamar aiki.
Za a rufe karbar bukatar neman damar a ranar 16 ga Maris din 2020, da karfe 11:59 na dare agogon GMT.
An fara bayar da kyautar ne domin karrama Komla Dumor dan kasar Ghana, kwararren mai gabatar da shirye-shirye a BBC, wanda ya rasu a 2014 yana da shekara 41.
Bayanan hoto, Komla Dumor ya rasu a 2014 yana da shekara 41.
Sojin Isra'ila sun kai hari kan Palasdinawa
Rundunar sojin Isara'ila ta ce dakarunta sun kai hari ta sama kan mayakan kungiyar Palasdinawa da ke Gaza da Syria domin ramuwar harin rokar da aka kai musu.
Sojin kasa na Isra'ila sun ce sun kai harin kan kungiyar Islamic Jihad targets a kudancin Damascus da Zirin Gaza ranar Lahadi.
A wani batu na ba-sa-ban-ba game da hari a kan Syria, sojin Isra'ila sun ce sun kai hari a kan "dandazon 'yan kungiyar Islamic Jihad."
Syria ta ce makamanta sun kakkabe akasarin makamai masu linzami da sojin Isra'ila suka harba mata.
Jami'an lafiya sun ce mutum hudu ne suka jikkata, ko da yake ba a san illar da harin ya yi ga bangaren Isra'ila ba.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Syria ta ce makamanta sun kakkabe akasarin makamai masu linzami da sojin Isra'ila suka harba mata.
Batan kudaden ma'aikatar tsaro ya janyo ce-ce-kuce a Nijar
Jama'a a jamhuriyar Nijar na ci gaba da mayar da martani kan wasu bayanai na ministan tsaron kasar kan binciken da aka yi na salwantar da wasu makudan kudi a ma'aikatar tsaron kasar.
Al'ummar kasar, sun kuma bayyana farin cikinsu bisa nasarar da dakarun kasar suka samu na kashe sama da 'yan bindiga 100 a yankin Tillabery.
Ministan tsaron ya ce za su mika sakamakon binciken da suka gudanar kan kudaden tare da mika wa shugaban kasa don a san matakin da za a dauka.
Mutanen Borno sun soma azumi da addu'o'i kan Boko Haram
Ranar Litinin al'ummar jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya suka tashi da azumi da addu'o'i da zummar neman saukin masifar da mayakan kungiyar Boko Haram suka jefa su a ciki.
Mayakan na Boko Haram sun kwashe fiye da shekara goma suna kai hare-hare a arewacin Najeriya, musamman a jihohin Borno da Yobe da kuma Adamawa.
Hare-haren sun yi sanadin mutuwar dubban mutane kana suka raba miliyoyin jama'a da gidajensu.
Malam Abdulmumin Yunus, wani malamin addinin Musulunci a Maiduguri, ya shaida wa BBC muhimmancin yin azumin da addu'o'i.
"Da ma ya tabbata a cikin addinin Musulunci cewa duk lokacin da wata matsala ta taso, mutane suna iya tawassuli da ayyuka na alheri da nufin Allah ya dauke wannan masifa da ake ciki.
Dangane da azumin da mai girma Gwamna ya ce a yi, abu ne da lallai mutane sun karbe shi kwarai da gaske. Akwai wadanda ba Musulmi ba ne wadanda muka tattauna da su suka ce za su yi irin nasu nau'in na ibada" in ji shi.
A makon jiya ne gwamnan jihar ya bukaci a tashi da azumi da addu'o'i ranar Litinin 24 ga watan Fabrairun 2020, domin neman sauki kan Boko Haram.
Asalin hoton, Twitter/@govborno
Bayanan hoto, A makon jiya ne Gwamnan Zulum ya bukaci a tashi da azumi da addu'o'i ranar Litinin 24 ga watan Fabrairun 2020
Shugaban da ake zargi da kashe matarsa ya gurfana a gaban kuliya
Firai ministan Lesotho Thomas Thabane - wanda ake zargi da kashe tsohuwar matarsa - ya gurfana a gaban kotu da ke Maseru, babban birnin kasar.
Bai je gaban kotun ranar Juma'a kamar yadda ak bukace shi ya yi ba domin fuskantar tuhuma kan zargin kashe Lipolelo Thabane, wacce aka harbe har lahira kwana biyu kafin ya sha rantsuwar kama aiki a shekarar 2017.
Ranar Juma'a, dansa da kuma mai magana da yawunsa sun ce ya tafi Afirka ta Kudu inda za a duba lafiyarsa.
Asalin hoton, Reuters
Bayanan hoto, Thomas Thabane ya bayyana kisan matar tasa a matsayin wani "rashin hankali"
Mata sun shiga sana'ar damben gargajiya a Najeriya
An dambata a wasanni da dama a gidan wasa na Idris Bambarewa da ke Marabar Nyanya a jihar Nasarawa a Najeriya, ciki har da damben mata.
Baby da Ramsy sun bukaci yin dambe don kashin kansu, inda Baby ta wakilci jihar Nasarawa, ita kuwa Ramsy tana bangaren Kano.
Ko da yake turmi biyu suka yi babu kisa aka raba su.
Bayanan bidiyo, Damben mata tsakanin Baby da Ramsy
‘Yan hamayya sun yi zargin tafka magudi a zaben Togo
Akalla 'yan hamayya uku ne a zaben shugaban kasar Togo suka yi zargin tafka magudu.
Kwarya-kwaryan sakamako ya nuna cewa shugaban kasar, Faure Gnassingbé ne ya lashe zaben, inda zai yi wa'adi na hudu.
Hukumar zaben kasar ta ce sakamakon zaben ya nuna cewa Mr Gnassingbé ya samu kashi 72, yayin da mutumin da ya zo na biyu, Agbéyomé Kodjo, ya samu kashi 18 na kuri'un da aka kada.
Tun da farko, Mr Kodjo ya ce an tafka magudu yana mai ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben.
Wani dan takarar, Jean-Pierre Fabre ya amince da shan kaye ta hannun shugaban yakin neman zabensa Patrick Lawson-Banku.
"Sakamakon zaben farko ya nuna cewa dan takarar jam'iyyar MPDD [Mr Kodjo leads] da na jam'iyya mai mulki UNIR su ne kan gaba," in ji Mr Lawson-Banku.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Shugaba Faure Gnassingbé ya fara mulkin Togo a 2005
Gwamnatin Najeriya ta musanta sanya ido kan shafukan zumunta
Ma’aikatar sadarwa
da tattalin arzikin intanet ta Najeriya ta musanta rahotannin da ke cewa ana
sanya ido kan wayoyin da mutane ke yi da kuma yadda suke amfani da shafukan
sada zumunta.
Ma’aikatar ta bayyana haka ne bayan wata sanarwar bogi da ta
karade shafukan sada zumunta wacce kuma ta sanya fargaba cewa an hada dukkan wayoyin
salular mutane da na’urorin ma’aikatar kuma jami’an gwamnati na sauraren dukkan
maganganun da ‘yan kasar ke yi a waya.
Sai dai mai Magana da yawun minista Isa Ali Pantami, Mrs Uwa
Suleiman, ta fitar da sanarwar da ke cewa labarin na kanzon kurege ne sannan ta
bukaci ‘yan Najeriya su yi watsi da shi.
Sanarwar, wacce ma’aikatar sadarwar ta wallafa a shafinta na
Twitter, ta kara da cewa “Tun da fari, ofishin minister ya yi watsi da wannan
sakon wanda ake ta watsawa, domin ba ma so mu mayar da hankali kan masu yada
shi. Amma yadda labarin ke watsuwa da kuma burinmu na wayar da kan ‘yan
Najeriya, ya sa mun fito mun yi watsi da batun.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.
Karshen labarin da aka sa a X
Barkan mu da warhaka
Barkan mu sake saduwa a wannan rana ta Litinin, inda za mu kawo muku labara da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar, da makwabta, har ma da wasu sassan duniya.