Abubuwan da suka faru a Najeriya da Nijar da sassan duniya

Wannan shafin yana kawo muku labarai da rahotannin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma wasu sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Nabeela Mukhtar Uba

  1. Hanyoyi 4 na kare kai daga Coronavirus

    Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana matakan da mutane za su dauka domin kauce wa kamuwa da cutar numfashi ta coronavirus.

    Yaya zan kare kaina daga cutar?

    Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce:

    ■ Ku wanke hannayenku da sabulun gargajiya ko sabulun ruwa da ake wanke hannu da shi, wato hand gel, wanda zai iya kashe kwayoyin cuta

    ■ Ku rufe hanci da bakinku lokacin da kuke yin atishawa da kyallen fyace majina - sannan ku wanke hannayenku bayan kun yi atishawa domin hana kwayoyin cutar yaduwa.

    ■ Ku guji taba idanunku, ko hanci ko bakinku- idan hannunku ya taba wurin da cutar ta shafa, za ta iya yaduwa zuwa sauran sassan jikinku.

    ■ Kada ku rika matsawa kusa da mutanen da ke yawan atishawa ko tari da masu fama da zazzabi - za su iya watsa cutar cikin iska ta yadda ku ma za ku iya kamuwa da ita. - akalla ku matsa nesa da su ta yadda tazarar da ke tsakanin ku za ta kai kafa uku.

    Bayanan sautiDr. Nasir Sani Gwarzo, ya fadi yadda za a kare kanku daga kamuwa da coronavirus.
  2. Yadda Coronavirus ta bulla a Lagos

    Hukumomi a Najeriya sun ce wani dan kasar Italiya ne ya shigo da cutar coronavirus.

    A sanarwar da ya fitar, ministan lafiya na Najeriya Dr Osagie Ehanire ya ce wani dan Italiya ne da ke aiki a kasar ya shigo da cutar bayan ya dawo daga Milan zuwa Lagos.

    "Sakamakon gwaji da aka gudanar a asibitin koyarwa na jami'ar Lagos ya tabbatar da yana dauke da cutar."

    "Ana duba lafiyarsa a asibitin kula da cutuka masu yaduwa a Yaba, kuma marar lafiyar bai nuna alamomi masu muni ba," in ji shi.

    Ya kuma ce gwamnati ta kara tsaurara matakai domin tabbatar da dakile yaduwar cutar.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  3. Barkan mu da warhaka

    Da fatan za ku kasance tare da mu tsawon wannan rana ta Juma'a domin sanin abubuwan da ke wakana a Najeriya da Nijar da sassan duniya. Za mu kawo muku karin bayani kan bullar cutar coronavirus da irin matakan da ake dauka don dakile ta. Mun gode

  4. Rufewa

    A nan muka zo karshen labarai da rahotannin da muke kawo muku a wannan shafin. Ku ci gaba da karanta sauran labaran a bbchausa.com ko a shafukanmu na sada zumunta da muhawara.

    Za ku iya duba kasa domin karanta labaran da muka kawo muku tun da safe. Ku kasance tare da mu ranar Juma'a. Mun gode

  5. 'Lassa ta kashe mutum 118 a Najeriya'

    Hukumar dakile yaduwar cututtuka a Najeriya ta ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon barkewar cutar zazzabin Lassa daga farkon shekarar nan ya karu zuwa 118.

    Hukumar ta bayyana haka cikin rahoton da take fitarwa kan halin da ake ciki game da cutar a kasar.

    Ta ce rahoton daga 1 ga Janairu zuwa 23 ga Fabrairun bana ne.

    Akalla mutum 2,633 ne ake zargi sun kamu da Lassa tun farkon 2020 daga cikinsu mutum 689 aka tabbatar sun kamu da cutar.

    Mutanen sun fito ne daga kananan hukumomi 115 daga jihohi 27 na kasar.

    Ta ce rahoton daga 1 ga Janairu zuwa 23 ga Fabrairun bana ne.

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Ta ce rahoton daga 1 ga Janairu zuwa 23 ga Fabrairun bana ne.
  6. Me ya sa coronavirus ba ta bulla a Indonesia ba?

    Rahotanni na cewa ana samun fargaba kan yadda Indonesia take gwajin coronavirus.

    Ya zuwa yanzu ba a samu bullar cutar ba duk da kusancinta da China inda cutar ta samo asali.

    ''Akwai alaka tsakanin China da Indonesia kuma idan muka duba sauran kasashen da ke da kusanci da ita, duk sun fitar da rahoto kan bullar cutar,'' a cewra Dr Isaac Bogoch kwararre kan cututtuka masu yaduwa kuma malami a jami'ar Toronto da ke Canada.

    ''Indonesia a baya-bayan nan ta samar da hanyar gano cutar kuma ina ganin idan muka duba taswira da kuma yanayin tafiye-tafiye, akwai daya daga cikin yankunan da muke kallo.''

    Mutum biyu a kasar sun mutu da alamun coronavirus, a cewar rahotanni daga Strait Times.

    Amma babu wanda ya kamu da sabuwar cutar ta numfashi.

    Akwai alaka tsakanin China da Indonesia

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Akwai alaka tsakanin China da Indonesia
  7. An yi kutse a wayar ministar leken asiri a Afirka ta kudu

    An yi kutse a wayoyin ministar leken asiri a Afirka ta kudu, Ayanda Dlodlo, da mataimakinta Zizi Kodwa.

    Masu bincike na duba ta yadda aka yi kutse a wayoyinsu da kuma wayoyin wasu jami'an leken asiri, a cewar ma'aikatar tsaron.

    Sai dai babu masaniya kan wanda yake da hannu a lamarin ko kuma an yi kutse kan mahimman bayanai, in ji ma'aikatar.

    Mai magana da yawun Dlodlo ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa an gano kutsen lokacin da mutane da dama suka ga sakon karta-kwana daga Kodwa.

    Lamarin dai na zuwa ne 'yan makonni bayan an kutsa cikin hedkwatar hukumar tsaron kasar da ke Pretoria babban birnin kasar.

    Barayi sun shiga wajen ajiyar mahimman bayanai a ofishin tare da tafiya da wasu takardu da kudade da ba a san yawansu ba kamar yadda aka wallafa a shafin IOL da ke intanet.

    Afirka ta kudu

    Asalin hoton, Getty Images

  8. Bazuwar farin dango na barazana a gabashin Afirka

    Kungiyar agaji ta Mercy KO ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar shigar farin dango a gabashin Afirka ya iya jefa yankin cikin mummunan matsin rayuwa.

    Kungiyar ta sanar da cewa a makonni masu zuwa ne ake sa ran farin su dira yankin.

    Masana sun sanar da cewa farin na haihuwa da hakan ke ninka yawansu kusan sau biyar a lokaci daya.

    Sai dai suna fatan samun sauyin yanayi da gaggawa wanda hakan zai takaita yaduwar farin.

  9. Najeriya na shirye-shiryen tunkarar coronavirus

    Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya ta fara shiryen-shirye kan yadda za ta tunkari coronavirus idan ta bulla a kasar.

    A wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter, hukumar ta ce tawagar da ke shirye-shirye kan coronavirus bisa tallafin hukumar lafiya ta duniya a kasar na karbar bakuncin wani taron yini biyu domin tunkarar cutar.

    An tsara taron ne domin karfafa matakan kariya idan aka samu bullar cutar a Najeriya.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  10. An gudanar da taron habaka tattalin arzikin Najeriya

    Mataimakin Shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranci zaman majalisar habaka tattalin arzikin kasar da aka gudanar yau Alhamis.

    An gudanar da taron ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja babban birnin kasar.

    Mataimakin shugaban kasar ne ke jagorantar majalisar sannan kuma akwai gwamnonin jihohi 36 da ministan babban birnin kasar da kuma gwamnan babban bankin kasar a matsayin mambobi.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  11. 'Yan Nijar sun nemi gwamnati ta sa baki kan rufe shagunansu a Cote d'Ivoire

    Wasu al'ummar Jamhuriyar Nijar mazauna Abidjan sun koka kan rufe shagunansu da suka ce hukumomin kasar Cote d'Ivoire sun yi tsawon kwana 28, lamarin da har ya janyo tunzuri.

    Sun ce dambarwa ta taso ne tun lokacin da sabon magajin birnin Abidjan ya fara aikin rushe shaguna a kokarinsa na yi wa birnin gyaran fuska, abin da su kuma ya jefa harkokin kasuwancinsu cikin mawuyancin hali.

    Jagoran mutanen Abdussalam Sha'aibu Akunu ya shaida wa BBC cewa akwai bukatar gwamnati ta yi kokari ta kai musu dauki.

    Bayanan sautiLatsa alamar lasifikar domin sauraron hirar Mukhtar Adamu Bawa da Jagoran 'yan Nijar a Cote d'Ivoire Abdussalam Sha'aibu Akunu
  12. 'Yaki da cutar TB a Najeriya ya ja baya'

    Gwamnatin Amurka ta ce ta tallafa wa jami’an lafiya wajen kubutar da rayukan ‘yan Najeriya fiye da dubu dari biyar da tamanin da daya da suka kamu da cutar tarin TB, ta hanyar shirin raya kasashe na USAID.

    Sai dai kuma wata kungiyar masu fama da cutar Sida a Najeriya ''Network of people living with HIV and Aids'' ta koka kan abin da tace yaki da cutar ta TB ya ja baya.

    Kungiyar ta ce ana ci gaba da fama da cutar a kasar a don haka ta ce akwia bukatar gwamnati ta kara zage damtse wajen zuba kudade domin yaki da cutar.

    Bayanan sautiShiga nan domin sauraron rahoton Zahraddeen Lawan
  13. Coronavirus ta sake kama dan majalisar Iran

    Shugaban kwamitin tsaron kasa da manufofin kasashen waje a majalisar dokokin Iran ya zamo babban dan siyasa na uku a kasar da ya kamu da cutar coronavirus.

    ''Gwajin da aka yi mani na coronavirus ya nuna ina dauke da ita.....babu abin damuwa. Ina killace. Da yardar Allah za mu yi nasara kan corona,'' in ji Mojtaba Zolnour.

    A baya ma an tabbatar karamin ministan lafiya a kasar da wani dan majalisa sun kamu da cutar.

  14. Kun san abin da ya fi bai wa Rikadawa dariya?

    Latsahoton sama donkallon bidiyon:

    Daga bakin mai ita wani shiri na BBC Hausa da ke kawo muku hira da fitattun mutane kan wasu abubuwan da suka shafi rayuwarsu zallah.

    A wannan kashi na 15, shirin ya tattauna da fitaccen tauraron fina-finan Hausa Rabi'u Rikadawa, inda ya amsa tambayoyin da za su saku dariya.

    Da muka tambaye shi game da irin son da yake yi wa matarsa, inda ya amsa cewa tana a cikin zuciyarsa kamar kudin haya, sai muka tambaye shi ko zai yi mata kishiya?

    Sai ya ce da ya samu kudi zan kara aure.

    Bayanan bidiyo, Da na samu kudi zan yi wa matata kishiya - Rikadawa
  15. Mexico ta mayar wa Najeriya kayan tarihi

    Gwamnatin Mexico ta mayar wa Najeriya wani kayan tarihi na sassaka na tagulla bayan da jami'an kwastam suka kwace a filin jiragen sama na babban birnin kasar.

    Kamfanin dillacin labaran AFP ya rawaito cewa an sassaka kayan tarihin na tagulla ne a karni na shida a birnin Ife.

    An ambato wani jim'in ma'aikatar harkokin wajen Mexico yana cewa an kai kayan tarihin kasar ne ta haramtacciyar hanya.

    Hukumar kula da kayan tarihin kasar ta wallafa batun a shafinta na Twitter:

    An ambato wani jim'in ma'aikatar harkokin wajen Mexico yana cewa an kai kayan tarihin kasar ne ta haramtacciyar hanya.

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, An ambato wani jim'in ma'aikatar harkokin wajen Mexico yana cewa an kai kayan tarihin kasar ne ta haramtacciyar hanya.
    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  16. Ana kokawa kan daukewar lantarki a Ghana

    Bayanan sautiLatsa alamar lasifikar domin sauraren cikakken rahoton Muhammad Fahd Adam

    Al'ummar Ghana na kokawa kan matsalar daukewar lantarki a wasu sassan kasar, musamman wadanda kasuwancinsu ya dogara da lantarkin.

    Ma'aikatar makamashi a kasar ta ce an samun matsala ne saboda gyaran da ake yi wa bututun iskar gas da ke Najeriya, sai dai wasu kwararru kan sha'anin makamashi da wasu 'yan adawa na zargin gwamnatin da gazawa.

    Sun ce ana neman koma wa gidan jiya a matsalar wutar lantarkin da aka fi sani da DUM-SOH.

  17. Shugaban Guinea ya ki ganawa da shugabannin ECOWAS

    Shugaban Guinea, Alpha Conde, ya ki ganawa da shugabannin kungiyar kasashen yammacin Afirka yayin da kasar ke tunkarar zaben raba gardama da zai ba shi damar ci gaba da mulki karo na uku.

    An shirya tawagar shugabbannin yammacin Afirka za su je Guinea ranar Juma'a kamar yadda gidan rediyon RFI ya sanar.

    Tawagar za ta samu jagorancin shugaban Nijar Mahamadou Issoufou sannan tawagar za ta kunshi Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya da takwaransa na Ghana Nana Akufo-Addo da na Burkina Faso Roch Marc Christian Kaboré.

    Guinea ta fada cikin rikicin siyasa sakamakon yunkurin da shugaban ke yi na yi wa tsarin mulkin kasa garambawul ta hanyar zaben raba gardama da za a gudanar ranar 1 ga watan Maris.

    Amma 'yan hamayya sun ce za su kaurace wa zaben.

    Guinea

    Asalin hoton, gETTY

  18. Labarai da dumi-dumi, Za a rufe makarantun Japan saboda coronavirus

    Firai Ministan Japan Shinzo Abe ya yi kira a rufe dukkan makarantun kasar saboda fargabar ci gaba da barkewar cutar coronavirus.

    Ya bukaci a rufe makarantun daga ranar biyu da watan Maris zuwa wasu 'yan makwanni.

  19. Sojan Najeriya ya kashe kansa da abokan aikinsa hudu

    Wani sojan Najeriya da ke aiki da rundunar Lafiya Dole wacce ke yaki da Boko Haram a arewa maso gabashin kasar, ya kashe abokan aikinsa hudu, sannan ya harbe kansa.

    Wata sanarwa da mukaddashin kakakin rundunar sojin kasar, Kanar Sagir Musa, ya aike wa manema labarai ranar Laraba da almuru ta ce sojan, wanda ba a bayyana sunansa ba, ya kuma jikkata wasu abokan aikin nasa biyu.

    Sanarwar ta kara da cewa rundunar sojin tana kokarin tuntubar iyalan sojojin da aka kashe.

    A cewar Kanar Musa, rundunar sojin Najeriya ta fara gudanar da bincike kan lamarin domin gano abin da ya haddasa shi.

    Sojojin Najeriya dai na aiki tukuru wajen yaki da Boko Haram, inda masana harkokin lafiya ke cewa hakan yana shafar yanayin tunaninsu da lafiyar kwakwalwarsu.

    rundunar sojin Najeriya ta fara gudanar da bincike kan lamarin domin gano abin da ya haddasa sh

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Rundunar sojin Najeriya ta fara gudanar da bincike kan lamarin domin gano abin da ya haddasa lamarin
  20. Kasashen da coronavirus ta afkawa a Turai

    Kasashen da ke fama da coronavirus a nahiyar Turai da adadin mutanen da suka kamu da ita:

    ·Italiya- 400

    ·Jamus - 21

    ·Birtaniya - 13

    ·Faransa - 12

    ·Austria - 2

    ·Croatia - 2

    ·Spain - 2

    ·Rasha - 2

    ·Denmark - 1

    ·Belgium - 1

    ·Finland - 1

    ·Sweden - 1

    ·Switzerland - 1

    ·Girka- 1

    ·Norway - 1

    ·Georgia - 1

    ·North Macedonia - 1