Abubuwan da suka faru a Najeriya da Nijar da sassan duniya

Wannan shafin yana kawo muku labarai da rahotannin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma wasu sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Nabeela Mukhtar Uba

  1. Saudiyya ta dakatar da masu zuwa Umrah saboda Coronavirus

    Saudiyya ta sanar da hana maniyatta aikin Hajji da Umrah shiga biranen Makkah da Madina, a wani matakin hana yaduwar cutar coronavirus mai shafar numfashi.

    Ma'aikatar harkokin waje ta Saudiyya ta kuma ce za ta hana 'yan kasashen da aka tabbatar akwai cutar ko tana barazana ga kiwon lafiyar al'umma zuwa kasar.

    Sanarwar da ma'aikatar harkokin wajen ta wallafa a Twitter ta kuma ce ta dakatar da amfani da katin shaidar dan kasa maimakon fasfo lokacin shiga da fita daga Saudiyya.

    Dakatar da mahajjata zuwa Saudiyya na zuwa ne kwana 60 kafin a soma azumin watan Ramalana

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Dakatar da mahajjata zuwa Saudiyya na zuwa ne kwana 60 kafin a soma azumin watan Ramalana
    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  2. Barkanmu da sake saduwa

    Muna yi muku barka da warhaka. Da fatan za ku bibiye mu domin sanin halin da duniya ke ciki musamman a kasashen Najeriya da Nijar da makwabtansu, har ma da wasu sassan duniya.

  3. Rufewa

    Masu bin mu a wannan shafi a nan muka kawo karshen labarai da rahotanni kai tsaye na yau, sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu.

  4. Mai dakin Riek Machar ta mayar da martani kan takunkumin da aka sa wa mijinta

    Mai dakin tsohon shugaban 'yan tawaye, wato sabon mataimakin shugaban kasa na daya na Sudan ta Kudu, Angelina Teny, ta ce mijin nata Riek Machar, wanda aka rantsar a wannan matsayi yana jin tamkar dan fursuna ne.

    Ms Teny ta fada wa BBC cewa takunkumin da kungiyar kasashen Gabashin Afirka, IGAD ta sanya wa mijin nata na tafiye-tafiye zuwa wajen Sudan ta Kudu da rashin damar magana da 'yan jarida ko jama'a har yanzu duka suna nan.

    A ranar Asabar ne aka rantsar da Mista Machar a kan mukaminsa na da na mataimakin shugaban kasa na daya, a matsayin wani mataki na kafa gwamnatin hadin-kai da nufin kawo karshen yakin basasar 'yar autar kasashen duniyar na shekara shida.

    Sai dai wakilin musamman na kungiyar ta kasashen Gabashin Afirka a Sudan ta Kudun ya ce, an cire dukkanin wadannan takunkumi bayan rantsar da Mista Machar.

  5. Hukumar Tarayyar Afirka na son yakar ta'addanci

    Hukumar tarayyar Afirka ta bukaci rundunar G5 Sahel ta yi gagarumin garambawul kan yadda take gudanar da ayyukanta don yaki da masu ta-da-kayar-baya a yankin Sahel.

    Yayin wani taro da shugabannin kungiyar suka gudanar da yammacin jiya a birnin Noukchott, babban birnin Mauritania, shugaban Hukumar Tarayyar Afrika Moussa Faki Mahamat ya ce dole ne kasashen Afirka su tallafa wa rundunar don sauke nauyin da aka dora mata na yaki da ta'addanci a Sahel.

    Majalisar Dinkin Duniya a baya-bayan nan ta bayyana fargaba kan karuwar ayyukan ta'addanci a yankin na Sahel.

  6. Yara miliyan hudu na tsananin bukatar abinci a Zimbabwe

    Kusan kananan yara miliyan hudu ne ke neman agajin abincin da gaggawa a dalilin tsananin fari da matsin tattalin arziki a Zimbabwe.

    Kungiyar ba da jin kai ga kananan yara ta Save the Children ta ce tun yanzu yunwa ta fara kama yara da dama, kuma akwai barazanar mace-mace nan gaba idan har ba a dauki mataki ba a yanzu.

    Kungiyar ta kuma bayyana cewa yara maza da mata na cin abinci sau daya a rana su kuma yi tafiyar awanni kafin su samu ruwan sha.

    Rahotanni sun ce iyaye na aurar da kananan 'ya'yansu mata ga masu hannu da shuni don kawai su samu abinda za su ci.

    Hauhawar farashin kayan abinci a Zimbabwe ya kara dagula al'amura a yankuna da dama.

  7. An gargadi 'yan Kenya kan coronavirus

    Ma'aikatar lafiya ta kasar Kenya ta gargadi 'yan kasar kan tafiye-tafiye zuwa kasashen da aka samu bullar cutar coronavirus a cikinsu matukar tafiye-tafiyen basu zama dole ba.

    Hukumar ta kuma shawarci jama'a da su yi taka-tsan-tsan saboda yi wuwar kamuwa da cutar na ci gaba da karuwa sannan su ci gaba da daukan matakan kariya musamman wanke hannu da kuma kula da tsafta.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  8. Coronavirus ta bulla a Girka

    Ma'aikatar lafiya a Girka ta tabbatar da bullar coronavirus a kasar.

    Matar da ta kamu da cutar mai shekara 38 ta shiga kasar daga arewacin Italiya, a cewar wani jami'in ma'aikatar lafiya.

    Kafofin watsa labaran kasar sun ce an gano matar na dauke da coronavirus bayan da aka lura ta na nuna wasu alamu na kamuwa da cutar.

    Ma'aikatar lafiyar ta bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ta na cikin koshin lafiya amma ana ci gaba da lura da ita.

    Hukumomi kuma suna ci gaba da kokarin zakulo mutanen da suka yi mu'amala da ita sannan an kebe wasu, in ji hukumar.

    coronavirus

    Asalin hoton, Getty Images

  9. Iran ta kama mutum 24 saboda yada jita-jita

    'Yan sanda a Iran sun kama mutum 24 da ake zargi da yada jita-jita game da coronavirus ta intanet, a cewar kamfanin dillancin labaran AFP.

    An gargadi wasu masu amfani da intanet 118, in ji shugaban 'yan sandan da ke sa ido kan intanet Vahid Majid.

    An kirkiri wani sashe na musamman domin magance masu yada jita-jita kan coronavirus kamar yadda Majid ya fada.

  10. 'Coronavirus ta fi yaduwa a wasu kasashe fiye da China'

    A karon farko an samu bullar coronavirus a wasu kasashen fiye da China, a cewar shugaban hukumar lafiya ta duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus.

    A China, adadin mutanen da aka ce sun sake kamuwa da cutar a rnar Talata sun kai 411 yayin da a sauran kasashen duniya, aka samu mutum 427.

    A jumulla, yawan mutanen d suka kamu da cutar a duniya yanzu sun doshi 80,980.

    Shugaban WHO ya ce karin da aka samu a yawan mutanen da suka kamu da cutar a Italiya da Iran da Koriya ta kudu abin damuwa ne matuka amma za a iya magance cutar sannan bata kai a kira ta annoba ba.

    WHO

    Asalin hoton, Reuters

  11. 'Yan majalisa na yunkurin sauya fasalin 'yan sandan Najeriya

    An yi wa kudirin soke dokar rundunar 'yan sanda a Najeriya karatu na biyu a zauren majalisar wakilan kasar.

    Kudirin kuma na neman a samar da kudirin rundunar 'yan sandan Najeriya domin samar da tsari ga rundunar don tabbatar da hadin kai da kawance tsakanin 'yan sanda da al'umomi wajen samar da zaman lafiya da kuma yaki da laifuffuka.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  12. An zargi sojin Kamaru da kashe farar hula 21

    Kungiyar Human Rights Watch ta zargi sojojin Kamaru da hannu a kisan akalla farar hula ashirin da daya a wannan watan.

    Lamarin ya faru ne a Arewa maso Yammacin kasar inda sojojin suke yaki da 'yan a-waren yankin rainon Ingila.

    Human Rights Watch ta ce dakarun sojin tare da hadin bakin mayakan Fulani sun kai wa kauyen Ntumbo hari.

    A baya dai, rundunar tsaron Kamarun ta musanta cewa da hannunta, amma daga baya ta ce farar hula biyar ne suka mutu lokacin da gwamnati ta kai hari kan wani sansani.

    Dubban mutane ne rikicin ya daidaita kuma an fara yakin ne shekaru hudu da suka gabata, tsakanin rundunar soja da 'yan a-ware masu amfani da harshen Ingilishi.

    Lamarin ya faru ne a Arewa maso Yammacin kasar

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Lamarin ya faru ne a Arewa maso Yammacin kasar
  13. Kenya ta kwace ragamar gwamnatin Nairobi

    Shugaban Kenya Uhuru Kenyatta ya karbe ragamar wasu muhimman ayyukan gundumar Nairobi a abin da ofishinsa ya bayyana da wata "muhimmiyar yarjejeniya''.

    Dokar za ta ba da damar yin musayar ayyuka tsakanin gwamnatin kasar da kuma gwamnatocin gundumomi bayan cimma yarjejeniyar.

    Gwamnan Nairobi, Mike Sonko, ranar Talata ya mika ragamar ma'aikatun sufuri da lafiya da ayyuka da tsare-tsare.

    Ya kuma sa hannu kan yarjejeniyar a gaban Shugaba Kenyatta a fadar shugaban kasar.

    Gwamna Sonko na fuskantar tuhume-tuhumen cin hanci sannan an haramta masa shiga ofishinsa har sai an saurari karar da aka shigar a kansa.

    Ana zarginsa da bai wa makusantansa kyauta ba bisa ka'ida ba da yin jabun takardu da kuma wawure kudade.

    Sai dai ya musanta zarge-zargen.

    Ana kuma fatan 'yan majalisar dokokin gundumar su tafka muhawara kan kudirin tsige shi wanda aka gabatar wa majalisar a makon jiya.

    Yarjejeniyar da ta bai wa gwamnatin kasar karbe ragmar ayyukan gundumar ya janyo ce-ce-ku-ce inda wasu ke cewa lamarin ba ya bisa tsarin doka.

    Uhuru Kenyatta

    Asalin hoton, State House Kenya

  14. Kenneth Kaunda ya bukaci a kawo karshen hare-haren iskar gas, Daga Kennedy Gondwe BBC News, Lusaka

    Shugaban Zambia na farko Kenneth Kaunda ya yi kira da a kawo karshen hare-haren iskar gas kan gidaje da gine-gine a kudancin kasar.

    Ana zargin kimanin mutum 50 da hannu a kai hare-haren tun bayan da aka kai harin farko a watan Disamba.

    ''Ina kara jaddada wannan abu: dole a kawo karshen hare-haren sinadari mai guba da hare-hare kan wasu jama'a da ake zargi'', kamar yadda Kaunda mai shekara 96 ya fada wa kamfanin dillancin labaran kasar.

    A daya daga cikin harin da wasu batagari suka kai a makon da ya gabata, wani mutum ya shiga cikin taron jama'a da suke dukan wani da ake zargi, ba tare da sanin cewa kawunsa ba ne.

    Batagarin sun kashe mutumin da ake zargi.

    Kaunda ya ce hare-hare kan gidaje da makarantu da kwalejoji da gidajen yari abin damuwa ne saboda Zambia kasa ce da aka santa da zaman lafiya.

    Zambia

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Kenneth Kaunda
  15. EFCC ta kama tsohon shugaban majalisar dokokin Kano

    Hukumar yaki da masu yi wa arzikin kasa ta'annati a Najeriya, EFCC, ta ce ta kama tsohon shugaban majalisar dokokin jihar Kano kuma shugaban marasa rinjaye a majalisar yanzu Isiyaku Ali Danja.

    Wata sanarwa da hukumar ta aike wa BBC mai dauke da sa hannun mukaddashin shugaban sashen yada labaranta, Tony Orilade, ta ce an kama shi ne bisa zarginsa da yin amfani da ofishinsa ba yadda ya kamata ba da kuma sace wasu kudade da aka ware don ayyukan mazabu.

    Hukumar ta dauki matakin ne sakamakon wata takardar korafi da aka shigar cewa an karkatar da wasu kudaden haraji da suka kai sama da N1.5b daga asusun gwamnatin jihar Kano.

    Binciken da EFCC ta gudanar ya nuna cewa Danja ya sha cirar kudaden lokacin da shi kadai ne zai iya cewa ko an gudanar da ayyuka kafin biyan kudi.

    EFCC ta ce za ta shigar da kara gaban kotu da zarar ta kammala bincike.

    Ko a baya-bayan nan ma EFCC ta kama kwamishinan ayyuka na musamman a Kano Mukhtar Ishaq bisa karkatar da wasu kudaden karamar hukumar birni lokacin da yake shugaban karamar hukumar.

    Ganduje

    Asalin hoton, Facebook/Salihu Tanko Yakasai

  16. Za a hana yanka jakai a Kenya

    Ministan harkokin noma a Kenya ya ce za a hana mahautu yanka jakuna daga watan gobe.

    A shekarar 2012 kasar ta amince a rika yanka jakuna da sayar da nama da fatunsu domin biyan bukatar kasar China wadda ta fi amfani da su a duniya.

    Minista Peter Munya ya ce matakin da aka dauka a wancan lokaci bai dace ba saboda ya sa jukanan na karewa.

    Galibin 'yan kasar da ke zaune a karkara suna amfani da jakuna wurin debo ruwa da itace, lamarin da ya sa ake fargabar cewa raguwarsu za ta sa ayyukan mata a gida su karu.

    A yanzu Kenya na da jakuna 600,000, idan aka kwatanta su da yawan jakuna 1.8 m da kasar ke da su shekara goma da suka wuce, a cewar wasu alkaluma da aka fitar a bara.

    Kenya na da jakuna 600,000, idan aka kwatanta su da yawan jakuna 1.8 m da kasar ke da su shekara goma da suka wuce

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Kenya na da jakuna 600,000, idan aka kwatanta su da yawan jakuna 1.8 m da kasar ke da su shekara goma da suka wuce
  17. Iran na zargin Amurka da sanya tsoro a zukata

    Shugaban Iran Hassan Rouhani ya zargi Amurka da sanya tsoro a zukatan al'ummar kasar saboda bullar coronavirus.

    Mutum 19 ne suka mutu sannan mutum 139 suka kamu da ita tun bayan barkewarta.

    ''Bai kamata mu bar Amurka ta dasa wata sabuwar kwayar cuta a kan coronavirus da ake kira .......matsanancin tsoro ba,''

    Rouhani ya fada wa taron majalisar ministoci hakan ne kwana guda bayan sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya bayyana cewa Iran ta na kin ba da bayanai kan cutar

    Rouhani

    Asalin hoton, Reuters

  18. Buhari ya kaddamar da hukumar gudanarwar majalisar dokokin Najeriya

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rantsar da Shugaban hukumar gudanarwa ta majalisar dokokin kasar, Injiniya Ahmad Amshi da mambobin hukumar.

    Mai taimaka wa Buhari a kan shafukan sada zumunta Bashir Ahmad ne ya bayyana haka a shafinsa na Twitter.

    Ya ce an rantsar da su ne kafin fara gudanar da taron majalisar zartarwa da ake yi duk mako a fadar shugaban kasar da ke Abuja.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  19. An samu bullar coronavirus a Algeria

    Ministan lafiya a Algeria ya tabbatar da bullar coronavirus a kasar a wani jawabi da ya yi ta gidan talbijin din kasar ranar Talata.

    Ministan Abdel Rahman Ben Bouzid, ya ce mutumin da ya kamu da cutar dan Italiya ne wanda ya isa kasar ranar 17 ga watan Fabrairu, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.

    Tuni dai aka kebe mutumin domin hana bazuwar cutar.

    Algeria ta zamo kasa ta biyu a Afirka da ta samu bullar coronavirus.

    Masar ce ta farko amma daga baya an ce mutumin ya warke daga cutar kuma yana samun sauki.

    coronavirus

    Asalin hoton, Getty Images

  20. Almajirai sun yi watsi da dokar Ganduje ta hana bara

    Da alama mabarata sun bijire wa matakin da gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta dauka na haramta bara a titunan jihar.

    Sai dai kwana guda bayan gwamanti ta haramta bara, wakilin BBC ya zaga birnin na Kano inda ya ga mabarata na ci gaba da gudanar da barace-barace, kamar yadda za ku gani a wadannan hotuna da ya dauko daga sassa daban-daban na birnin Kano.

    Almajirai sun yi watsi da dokar Ganduje ta hana bara
    Bayanan hoto, Almajirai sun yi watsi da dokar Ganduje ta hana bara
    Almajirai sun yi watsi da dokar Ganduje ta hana bara
    Bayanan hoto, Almajirai sun yi watsi da dokar Ganduje ta hana bara
    Almajirai sun yi watsi da dokar Ganduje ta hana bara
    Bayanan hoto, Almajirai sun yi watsi da dokar Ganduje ta hana bara