An dakatar da malaman jami’a kan zargin lalata da dalibai
Jami’ar Ghana ta dakatar da malaman nan biyu da BBC ta bankado suna cin zarafin dalibai mata da kuma son yin lalata da su.
Tun a watan Oktoba ne aka soma dakatar da malaman jami’ar biyu, Farfesa Ransford Gyampo da Dr Paul Kwame Butakor domin gudanar da bincike a kansu.
Yanzu an dakatar da su na tsawon lokuta daban-daban ba tare da biyan su albashi ba.
Wata sanarwa da jam’iar ta fitar ranar Litinin ta ce an dakatar da Farfesa Gaympo tsawon wata shida ba tare da albashi da, yayin da aka dakatar da Dr Butakor tsawon wata hudu ba tare da albashi ba.
Dukkan su sun musanta zarge-zargen da aka yi musu.
Kazalika, dole ne malaman su samu horo kan kaucewa cin zarafin mutane ta hanyar lalata da kuma yadda ya kamata su rika tafiyar da harkokin dalibai.
Farfesa Gyampo da Dr Butakor ba za su koma bakin aiki ba sai an gamsu cewa sun gyara dabi’unsu.











