Abubuwan da suka faru a Najeriya da Nijar da sassan duniya

Wannan shafin yana kawo muku labarai da rahotannin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma wasu sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Nabeela Mukhtar Uba

  1. Najeriya na cikin kasashen da makomar yara ke cikin hatsari

    Najeriya na cikin kasashen da makomar yara kanana ke cikin hatsari, kamar yadda sabon binciken da aka fitar kan makomar rayuwar yara kanana a duniya ya nuna.

    Rahoton wanda Hukumar Lafiya ta Duniya da Asusun kula da kananan yara na Duniya, Unicef, da mujallar lafiya ta The Lancet suka fitar ya ce Najeriya ce kasa ta 174 cikin jerin kasashe 180 da aka yi nazari akansu game da bunkasar lafiya yara.

    Hakan na nufin Najeriya na daya daga cikin kasashe goma na karshe a duniya da makomar yara ke fuskantar rashin tabbas ta fuskar bunkasar rayuwarsu da lafiyarsu.

    Rahoton ya ce nazarinsa kan hatsarin da makomar yaran ke ciki ya dogara ne kan mizanin tsira da rai ga kananan yara da koshin lafiyarsu wadanda suka hada da lafiya da ilmi da abinci mai gina jiki da daidaito da tazarar da ke akwai ta fuskar kudin shiga.

    Binciken ya ce sama da yara Biliyan biyu ke rayuwa a kasashen da ci gabansu ke fuskantar barazana daga rikici da bala'o'i da canjin yanayi ke haddasa wa.

    Rahoton ya kwatanta kwazon kasashe 180 ne ta fuskar kosawar lafiyar kananan yara

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Rahoton ya kwatanta kwazon kasashe 180 ne ta fuskar kosawar lafiyar kananan yara
  2. An nemi matar shugaban kasa ta gurfana a gaban majalisa

    Shugabar majalisar dokokin Uganda ta aike da sabon sammaci ga mai dakin shugaban kasar, Janet Museveni, wadda kuma ita ce ministar ilimi, bayan wata takaddama da ta kaure sakamakon fito da sabuwar manhaja.

    Mrs Museveni bata je gaban ‘yan majalisar ba ranar Talatar makon jiya bayan shugabar majalisar Rebecca Kadaga ta bukaci ta je.

    Ta aiki wata ‘yar majalisa Rosemary Seninde da takardar neman afuwar takwarorinta a kan gazawarta ta zuwa zauren majalisar.

    Ta nemi gurfana a gaan ‘yan majalisar ranar Alhamis.

    Shugabar majalisar Kadaga ta aike da sabon sammaci sannan ta bai wa mai dakin shugaban kasar zabin kwana guda kacal domin ta bayyana a gabansu.

    ‘Yan majalisar dokokin Uganda sun zargi ma’aikatar ilimi da aiwatar da sabuwar manhajar a kananan makarantun sakandare duk kuwa da cewa majalisar ta bukaci a dakatar da aiwatar da shirin.

    ‘Yan majalisar sun nuna damuwarsu game da karancin littattafan karatu da kuma rashin gurbin horas da malamai a cikin sabuwar manhajar.

    Janet Museveni ita ce ita ce ministar ilimin Uganda

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Janet Museveni ita ce ita ce ministar ilimin Uganda
  3. Matar da ta sace kudin mabukata za ta yi zaman gidan yarin shekara shida

    Wata kotu a Denmark ta kama wata mata da laifin sace kimanin $17m na kudin gwamnati.

    Britta Nielsen ta kwashe shekara 40 tana aiki a ma’akatar kula da walwalar jama’a ta Denmark, inda take raba kudi ga mabukata.

    Amma a 2018 an zarge ta da laifin karkatar da kudi zuwa aljihunta.

    Ranar Talata wata kotu a birnin Copenhagen ta yanke mata hukuncin daurin shekara shida da rabi a gidan yari.

    Wannan lamari dai sabon abu ne a Denmark, kasar da ta yi suna wajen tabbatar da adalci da rashin cin hanci da rashawa.

    Nielsen ta tsere zuwa Afirka ta Kudu lokacin da aka zarge ta da laifin sace kudin. Ta amince ta koma Denmark bayan ‘yan kasan kasa-da-kasa sun yi sammacin kama ta.

    Nielsen

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Nielsen ta tsere zuwa Afirka ta Kudu lokacin da aka zarge ta da laifin sace kudin
  4. Kalaman Magu kan cin hanci sun jawo masa caccaka

    Kalaman da mukaddashin shugaban hukumar EFCC da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, Ibrahim Magu, ya yi cewa yana da yakinin cewa cin hanci ne silar bullar cutar coronavirus sun jawo ce-ce-ku-ce a kasar

    Ibrahim Magu ya bayyana haka ne ranar Talata a wajen bikin yaye sabbin dakarun EFCC da aka yi a Kaduna, yana mai cewa cin hanci da rashawa su babbar matsalar dan adam kuma sun fi duk wata cuta ta duniya illa.

    EFCC ta musanta cewa shugaban nata ya yi wadannan kalamai, duk kuwa da cewa an nuna shi yana yin su kai-tsaye a gidan talbijin na Najeriya, NTA.

    Masu amfani da shafukan sada zumunta sun caccaki shugaban na EFCC, inda ya kasance maudu’in da aka fi tattauna wa a kansa a shafin Twitter a Najeriya

    Wata mai amfani da Twitter, ta ce bai kamata Ibrahim Magu ya zama shugaban dandalin WhatApp ba ballantana shugaban hukuma mai muhimmanci.

    Shi ma wani mai amfani da Twitter, Hamma, ya ce Magu bai iya kalami ba yana mai cewa abin haushi ne duk da cewa sau biyu hukumar tsaro ta farn kaya a kasar na zarginsa da aikata laifi sannan majalisar dattawa ta ki wake shi domin zama shugaban din-din-din na EFCC, amma Shugaba Buhari yana ganin babu kamarsa wajen shugabancin hukumar.

    Kauce wa YouTube
    Ya kamata a bar bayanan Google YouTube?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da Google YouTube suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Google YouTube da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba. Ana yi samun tallace-tallace YouTube

    Karshen labarin da aka sa a YouTube

    Kauce wa X, 1
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 1

    Kauce wa X, 2
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X, 2

  5. Barkan mu da wannan lokaci

    Barkan mu da sake saduwa a wannan rana ta Laraba, wadda Hausawa ke cewa Tabawa ranar samu. Da fatan za ku kasance tare da mu domin sanin halin da duniya ke ciki, musamman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da ma wasu sassan duniya. Nasidi Adamu Yahaya da Nabeela Mukhtar Uba za su kasance tare da ku tsawon wannan rana.

  6. Rufewa

    Masu bibiyarmu a wannan shafin, a nan muka zo karshen labarai da rahotannin da muke kawowa kai tsaye.

    Za mu ci gaba da kawo muku wasu sabbin labarai da rahotannin ranar Laraba idan Allah ya kai mu.

    Kuna iya duba kasa domin karanta abubuwan da suka faru a Najeriya da sassan duniya yau Talata.

  7. Jordan ta soki shirin Isra'ila na fadada aikin layin dogo a Kudus

    Jordan ta yi Allah wadai da matakin Isra'ila na ci gaba da kudirinta na gina layin dogo da tashar jirgin kasa a karkashin birnin Kudus.

    Ma'aikatar sufuri ta Isra'ila a ranar Litinin ya ce an amince da wata sabuwar hanya domin fadada aikin layin dogon daga Tel Aviv zuwa Jerusalem.

    Jordan ta ta bayyana matakin a matsayin "take dokokin kasa da kasa."

    Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin waje Daifallah al-Fayez ya bukaci kasashen duniya su soki matakan Isra'ila da ba ya bisa doka.''

    Kudus

    Asalin hoton, AFP

  8. Amurka ta yi alkawarin samar da $8m domin yakar farin-dango

    Amurka ta yi alkawarin samar da dala miliyan takwas don takaita annobar farin-dango da ta bazu a Ethiopia da Kenya da Somalia.

    Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo, ya sanar da wannan tallafin a yayin wani taron manema labarai da ya yi da ministan harkokin wajen Ethiopia Gedu Andargachew a Addis Ababa.

    A makon da jiya ne Hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci kasashen duniya su samar da kusan $76m domin tallafawa da feshi a wuraren da annobar ta shafa.

    Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniyar ta gargadi gabashin Afirka cewa yankin na iya fuskantar matsalar abinci idan ba a takaita farin dangon da suke cinye albarkatun gona ba.

    Akwai fargabar cewa fari masu yawa - tuni cikin ɗaruruwan biliyoyin - suna ƙaruwa da yawa. Har yanzu kokarin da aka yi don magance tasirin bai yi tasiri ba.

    Farin dango

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Kenya na daya daga cikin kasashen da suke fama da annobar farin dango
  9. An sake zaben Ashraf Ghani a matsayin shugaban Afghanistan

    An sanar da Shugaba Ashraf Ghani a matsayin wanda ya lashe zaben watan Satumbar bara da aka gudanar a kasar sakamakon jan kafar da aka yi ta yi saboda zarge-zargen magudi.

    An sake zabar Mr Ghani da kashi sama da 50 na kuri'un da aka kada. Babban abokin hamayyarsa Abdullah Abdullah ne ya zo na biyu da kashi sama da 39 na kuri'un.

    Bangaren hamayya na cewa zaben 28 ga watan Satumbar cike yake da magudi da matsalolin na'urorin tantance kuri'u.

    Shugabar hukumar zaben kasar Hawa Alam Nutristani ta sanar da sakamakon ne a wani taron manema labarai a Kabul, babban birnin kasar.

    Ashraf Ghani

    Asalin hoton, REUTERS

    Bayanan hoto, Ashraf Ghani
  10. Buhari ya daina gudanar da mulki - PDP

    Babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya, PDP, ta yi ikirarin cewa shugaban kasar Muhammadu Buhari ya kaurace wa aikinsa na gudanar da mulki.

    A wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Twitter, PDP, ta ce zargin da mai bai wa shugaban kasar shawara kan sha’anin tsaro, Babagana Munguno ya yi cewa wasu mutane suna tsoma baki a harkokin tsaro, ya nuna abin da ta dade tana fada cewa shugaban kasar bai san abubuwan da ke wakana a gwamnatinsa ba.

    “Bayan wannan kalami da mai bai wa shugaban kasa shawara kan sha’anin tsaro ya yi, PDP tana jaddada kiran ta cewa kada shugaban kasa ya bata lokaci wajen sauka daga kan mukaminsa na shugaban kasa, domin a fili take cewa ba zai iya gudanar da aiki ba,” in ji PDP.

    PDP ta ce tana bai wa harkokin tsaro matukar muhimmanci a bangaren mulki, daga nan sai walwalar jama'a kuma tun da Shugaba Buhari ya gaza aiwatar da wannan nauyi bata ga dalilin ci gaba da zamansa a kan mulki ba.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  11. An saki dan Najeriyan da aka zarga da shigar da kwayoyi Saudiyya

    Bayanan sautiLatsa alamar lasifikar domin sauraron rahoton Imam Saleh

    Wata kotu a Saudiyya ta wanke wani malami dan Najeriya da ake zargin ya shiga kasar da miyagun kwayoyi.

    Hukuncin kotun na zuwa ne bayan da ya shafe shekara 3 yana tsare a kasar.

    A baya dai gwamnatin jihar Zamfara wato jihar da malamin ya fito ta bayyana cewa an kama shi ne bisa kuskure.

    Ko a shekarar da ta gabata ma, Jami'an tsaron Saudiyya sun kama wata matashiya 'yar Najeriya Zainab Aliyu jim kadan bayan sun isa Saudiyya don yin aikin Umara bisa zargin ta da shiga da miyagun kwayoyi kasar.

    Sai dai daga baya hukumomin Saudiyyan sun sake ta bayan da suka tabbatar ba ta da laifi.

  12. Ma'aikaciyar jinyar da take rawa don karfafa gwiwar marasa lafiya

    Wata ma'aikaciyar jinya a Afirka ta Kudu na rawa saboda ta sanya marasa lafiya nishadi.

    Jaridar Daily Sun ta kasar, ta nuna hoton bidiyon ma'aikaciyar, Thathakahle Gumede, 'yar shekara 57 tana ta taka rawa a gaban marasa lafiyan da suke jira su ga likita a wani asibiti da ke KwaZulu-Natal.

    Ms Gumede ta ce tana taka rawar ne domin marasa lafiyar da ke wajen su samu kwarin gwiwa a kan cutar da ke damunsu.

    Ta ce "Na yi amanna cewa magani ne ke warkar da ciwo, amma kuma mu ma ma'aikatan jinya na da rawar ta kawa wajen warkewar marar lafiya".

    Ms Gumede ta ci gaba da cewa "Yana da matukar muhimmanci ma'aikatan jinya su rinka yin abubuwan da za su sanyaya zukatan marasa lafiya, ba abin da zai bata musu ba".

    Ma'aikaciyar jinya na taka rawa a gaban marassa lafiya

    Asalin hoton, Via Facebook

    Bayanan hoto, Ma'aikaciyar jinya na taka rawa a gaban marassa lafiya
  13. Labarai da dumi-dumi, Buhari na ziyara a Kaduna

    Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, yana ziyara a jihar Kaduna da ke arewacin kasar.

    Wani bidiyo da mai taimaka wa shugaban kasar kan kafafen watsa labarai, Buhari Sallau, ya wallafa a shafinsa na Instagram ya nuna shugaban kasar a filin jirgin saman Kaduna inda manyan jami'an gwamnatin jihar,ciki har da Gwamna Nasir Elrufai suka tarbe shi.

    Shugaban kasar na ziyara ne kwana kadan bayan wasu 'yan bindiga sun kai hari kan motocin matafiya jim kadan bayan saukarsu daga jirgin kasa a tashar Rigasa da ke jihar.

    Kauce wa Instagram
    Ya kamata a bar bayanan Instagram?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a Instagram

  14. An kebe dan kasar China a Kenya saboda coronavirus

    An kebe wani dan kasar China da ke aiki a wani kamfanin gina hanya a arewa maso gabashin Nairobi babban birnin kasar Kenya, a wani mataki na gudun yaduwar cutar coronavirus.

    Babu wata alama da ta nuna mutumin wanda ke aiki a kamfanin kasarsu a Kenya yana dauke da cutar.

    An dai kebe shi ne a Mutomo da ke yankin Kitui, kuma ana mika masa abinci ne ta taga, in ji jaridar Daily Nation.

    Kamfanin dai ya aike da wata wasika ga mahukuntan yankin a kan cewa an kebe musu ma'aikaci bayan isowarsa kasar daga lardin Hebei da ke arewa maso gabashin China.

    Coronavirus

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Coronavirus
  15. Fada ya kaure a Ukraine

    Rundunar sojin Ukraine ta ce 'yan tawaye sun yi wa dakarunta da ke aiki a gabashin kasar ruwan harsasai, inda suka kashe soji daya sannan suka jikkata hudu.

    Sai dai 'yan tawayen wadanda Rasha ke mara musu baya sun ce dakarun sojin ne suka yi yunkurin kutsa kai yankin da bai kamata su shiga ba wanda aka da sa nakiyoyi lamarin da ya yi sanadin mutuwar soji biyu da jikkata soji uku.

    Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy zai gudanar da taron majalisar tsaron kasar da zummar sanin abin da ya haddasa fadan.

    Fadan yana barazana ga kwarya-kwaryar zaman lafiyar da aka samu tsakanin bangarorin biyu.

    Dakarun Ukraine

    Asalin hoton, AFP

  16. An kama mutanen da ake zargi da yunkurin kifar da gwamnatin Turkiyya

    Hukumomi a Turkiyya sun bada umarnin kama daruruwan mutane da ake zargi suna da hannu da kungiyar da aka zarga da kokarin kifar da gwamnatin da bai yi nasara ba a 2016.

    Kafofin yada labaran kasar sun ce an tsare kimanin mutum 50 a samamen da aka kai a birane 15 na kasar.

    Masu gabatar da kara sun bada takardar kama mutanen da ake zargi magoya bayan wani malamin addini ne dan Amurka Fethullah Gulen wanda gwamnatin Turkiyya ta zarga da kitsa yunkurin kifar da gwamnatin.

    Turkey

    Asalin hoton, Getty Images

  17. Shin Buhari na shirin sake zuwa hutu Birtaniya?

    Fadar shugaban Najeriya ta karyata labaran da ke cewa shugaban kasar na shirin zuwa hutu Birtaniya.

    Wata sanarwa da kakain shugaban kasar, Femi Adesina, ya fitar ta ce labaran na kanzon kurege ne kawai.

    "Ana ta watsa labarai cewa Shugaba Muhammadu Buhari na shirin tafiya Birtaniya inda zai yi kwana 20, sannan ya wuce Saudi Arabia da Austria. Wamnnan labarin karya ne. Karya ce kawai da wasu masu ganin baike suka kitsa."

    Mr Adesina ya bukaci 'yan kasar su kauracewa yada labaran kanzon kurege.

    A baya dai shugaban kasar ya je kasar ta Birtaniya, ciki har da ziyarar hutu da kuma ta jinya.

    Fadar shugaban kasa ta ce babu inda Shugaba Buhari zai je

    Asalin hoton, Instagram/BAYO OMOBORIOWO

    Bayanan hoto, Fadar shugaban kasa ta ce babu inda Shugaba Buhari zai je
  18. Mutumin da ya fi kudi a duniya ya ware $10bn kan sauyin yanayi

    Mutumin da ya fi kudi a duniya kuma mai kamfanin Amazon, Jeff Bezos, ya sha alwashin bayar da tallafin $10bn domin shawo kan matsalar sauyin yanayi a duniya.

    Mr Bezos ya ce za a yi amfani da kudin ne wurin daukar nauyin masana kimiyya da masu fafutikar kare muhalli da auran kungiyoyi.

    Ya ce: "Ina son yi aiki tare da sauran mutane domin sake yn sheka game da hanyoyin da aka sani da kuma wadanda za a lalubo da zummar yaki da matsalar sauyin yanayi."

    A sakon da ya wallafa a shafinsa na Instagram, Mr Bezos ya ce za a soma raba kudin a bazarar da ke tafe.

    Mr Bezos ya ce matsalar sauyin yanayi tana ci masa tuwo a kwarya

    Asalin hoton, AFP

  19. Kotun koli ta dage sauraron karar zaben Imo da Zamfara

    Kotun kolin Najeriya ta dage kararrakin da aka shigar gabanta wadanda ke kalubalantar hukuncin kotun na korar tsohon gwamnan jihar Imo, Emeka Ihedioha daga kan kujerarsa da kuma soke nasarar da jam'iyyar APC ta samu a zabukan 2019 da aka gudanar a matakai daban-daban a jihar Zamfara.

    Kotun ta dage karararrakin ne zuwa biyu ga watan Maris.

    Lauyan Ihedioha da PDP, Kanu Agabi, ya nemi a dage karar domin bai wa bangarorin damar kammala shirye-shirye.

    Lauyan Uzodinma da APC, Damian Dodo, bai kalubalanci rokon PDP ba.

    Alkalin alkalan kasar Mai shari'a Tanko Muhammad ya jagoranci lauyoyi bakwai a sauraron karar ta Ihedioha da mambobin APC a Zamfara kan kalubalantar hukuncin kotun.

    Sauran mambobin sun hada da Mai shari'a Sylvester Ngwuta da Kayode Ariwoola da Kudirat Kekere-Ekun da Inyang Okoro da Amina Augie da kuma Uwani Abba-Aji.

    TANKO MUHAMMAD

    Asalin hoton, TWITTER/@NGRPRESIDENT

  20. Pompeo ya yabi Angola ‘kan yaki da cin hanci’

    Sakataren wajen Amurka Mike Pompeo, wanda yake ziyara a Angola, ya ce daya daga cikin abubuwan da suka bas hi mamaki a yayin da yake kai ziyara kasashen duniya shi ne yadda cin hanci da shawara ya yi katutu.

    Amma ya yabi Shugaba João Lourenço bias kokarinsa na magance almundahana, yana mai cewa illar da ta yi wa Angola a bayyana take.

    Dangin tsohon shugaban Angola – musamman ‘yarsa Isabel dos Santos – a halin yanzu tana fuskantar bincike a kan zargin almundahana.

    A ziyarar da yake yi a Afirka, Mr Pompeo ya ce yana so ya bunkasa harkar masu zuba jari a Amurka sannan ya dakushe tasirin da Chinas take yi a nahiyar inda kuma ya kawar da fargabar da ake yi cewa Amurka na shirin rage yawan dakarunta a nahiyar.

    Daga Angola, zai wuce Ethiopia a ziyarar kasashen Afirka uku da yake yi. Tun da fari ya kai ziyara Senegal.

    Shugaba João Lourenço (Dama) tare da Sakataren wajen Amurka wanda ke ziyarar Afirka karon farko

    Asalin hoton, Getty Images