Abubuwan da suka faru a Najeriya da Nijar da sassan duniya

Wannan shafin yana kawo muku labarai da rahotannin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma wasu sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Nabeela Mukhtar Uba

  1. 'An gano yawan mutanen da suka bata a Kano'

    Kwamitin binciken gano yaran da suka bata da gwamnatin jihar Kano a Najeriya ta kafa ya ce ya gano adadin yawan mutanen da suka bata a jihar.

    Shugaban Kwamitin mai shari'a Wada Rano yashaida wa BBC cewa kwamitinsa ya gano mutum 113 da suka tabbatar da sun bata a jihar daga 2010 zuwa 2019.

    Ya ce ta hanyar iyayen da yaransu suka bata ne suka gano yawan adadinsu, kuma akwani wani gidan marayu da ake tafiyar da shi ba bisa ka'ida ba da aka gano wasu yaran da suka bata.

    Ya kara da cewa daga cikin Yaran da aka gano har da wasu guda uku 'yan kabilar Igbo daga jihar Anambra a kudancin kasar.

    Gwanma Ganduje

    Asalin hoton, SALIHU TANKO YAKASAI/FACEBOOK

    Bayanan hoto, Gwamna Ganduje
  2. Ana son kafa hukuma kan tubabbun ‘yan Boko Haram

    An yi wa wani kudurin doka da ke so a sake shigar da tubabbun mayakan kungiyar Boko Haram cikin al'umma karatu na farko a zauren majalisar dattawan Najeriya.

    Ranar Alhamis ne tsohon gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Geidam, ya gabatar da kudurin dokar.

    Kudurin dokar na so a kafa hukumar da za a dora wa alhakin ilimantar da kuma sake shigar da tubabbun mayakan Boko Haram cikin al’umma.

    Sai dai wasu ‘yan kasar na nuna damuwa kan yadda ke bai wa tubabbun ‘yan boko haram din muhimmanci, yayin da mutanen da suka raba da muhallansu ke cikin kuncin rayuwa.

    Majalisar datawan Najeriya

    Asalin hoton, NIGERIAN SENATE

    Bayanan hoto, Zauren majalisar datawan Najeriya
  3. Barkan mu da sake saduwa

    Barkan mu da sake saduwa a wannan rana ta Juma'a. Da fatan za ku bibiye mu tsawon wannan rana domin sanin halin da duniya ke ciki, musamman a kasashen Najeriya da Nijar, da makwabtansu, har ma da wasu sassan duniya.

  4. Rufewa

    A nan muka zo karshen labarai da rahotannin da muke kawo muku na wannan rana. Da fatan za ku kasance tare da mu ranar Juma'a domin samun sabbin rahotanni. za ku iya duba kasa don karanta labaran da muka riga muka gabatar. Kada ku manta za ku iya bibiyarmu a shafukanmu na sada zumunta da muhawara. Mun gode

  5. Kalli matar da aka yi wa tiyata a kwakwalwa tana kada goge

    Wata mara lafiya a Asibitin Kwalejin Kings da ke Landan ta kada goge a lokacin da likitoci suke mata tiyata a kwakwalwa don cire mata tsiro.

    Dagmar Turner, mai shekara 53, ta kada gogen ne don likitoci su tabbatar da cewa sauran sassan kwakwalwar da ke sa hannaye yin aiki ba su tabu ba a yayin tiyatar.

    Bayanan bidiyo, Kalli matar da aka yi wa tiyatar kwakwalwa tana kada goge
  6. Namibia za ta a fitar da naman sa zuwa Amurka

    Namibia ta zamo kasar Afirka ta farko da za ta fara fitar da naman sa zuwa Amurka, bayan shafe shekara kusan 20 ana yarjejeniya a kai.

    Kamfanin da ke sarrafa nama na kasar, Meatco, ya tura da naman da ya kai tan 25 a karon farko.

    Ministan harkokin wajen kasar, Netumbo Nandi-Ndaitwah, ya ce daga karshe dai kasar tasu ta fara fitar da naman sa zuwa babbar kasuwar Amurka.

    Ana sa ran Namibia za ta fitar da naman sa tan 860 a shekarar da muke ciki.

    Shanu

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Shanu
  7. 'Ana haifar ‘ya’yan da ba a bukatar su a Najeriya'

    Mai martaba Oni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, ya yi kira ga majalisar dokokin Najeriya ta fito da wata doka da za ta tilasta wa maza daukar nauyin 'ya'yansu.

    Oni Ogunwusi ya yi wannan kira ne a wurin taro mai taken "Sake Fasalin Zamantakewar Aure Domin Cigaban Najeriya," da aka yi a Abuja ranar Alhamis.

    Ya ce akwai bukatar a karbi mambobin BVN na bankunan magidantan da ke watsi da dawainyar iyalinsu ta yadda za a rika cire kudi daga asusunsu ana bai wa 'ya'yansu.

    Oni na Ife ya ce: “Maganganun baki sun isa haka, ina farin ciki shugaban majalisar dattawa yana nan. Muna bukatar daukar wannan batun da matukar muhimmanci, muna bukatar yin dokoki da za su tilasta wa iyaye lura da ‘ya’yansu.

    "Ya ma kamata duk matakin da za a dauka a hada shi da lambar banki ta BVN ta irin wadannan iyayen da ke haifo ‘ya’yan da ba a bukatar su, wadanda suke zama alakakai a cikin al’umma," in ji Oni na Ife

    A cewarsa: "Idan ma ba za a iya kwace musu dukiya ba, to a kwace musu asusun ajiyarsu na banki. A kuntatawa rayuwarsu, har su yi abin da ya kamata, ta yadda za mu ringa samun ‘ya’yan da muke bukata.”

    Oni na Ife ya bukaci a kwace asusun bankin iyayen da ba sa kula da 'ya'yansu

    Asalin hoton, Facebook/Africa Most Respected King

    Bayanan hoto, Oni na Ife ya bukaci a kwace asusun bankin iyayen da ba sa kula da 'ya'yansu
  8. Za a kafa gwamnatin hadin kan kasa a Sudan ta Kudu, Daga Catherine Byaruhanga BBC News, Kampala

    Shugaban Sudan ta kudu Salva Kiir da Riek Machar sun amince su kafa gwamnatin hadin kan kasa nan da ranar Asabar.

    Lamarin ya biyo bayan wani taro da aka yi ranar Alhamis a fadar shugaban kasar da ke Juba.

    Shugaba Kiir ya sha alwashin kare shugabannin hamayya.

    Magoya bayan Mr Machar sun nemi samun tabbaci kan lafiyarsa idan ya koma babban birnin kasar.

    Mr Kiir ya ce za a kammala tattauna muhimman batutuwa da ba a warware su ba kamar yadda shi da Mr Machar za su yi karba-karba a mulkin kasar da yadda za a hada kan 'yan hamayya a kwanaki masu zuwa.

    Mr Machar ya amince ya nada tsohon abokin adawarsa a matsayin mataimakin shugaban kasa na farko sannan kuma za a rushe majalisar zartarwa domin bai wa karin 'yan hamayya dama.

    Akwai fatan cewa yarjejeniyar za ta kawo karshen yakin basasar da aka shafe tsawon shekara shida ana yi a Sudan ta Kudu.

    Yakin ya yi sanadiyyar mutuwar mutum dubu dari hudu.

    Mutanen biyu sun taba kafa gwamnatin hadin kan kasa na takaitaccen lokaci a 2016 kafin Mr Machar ya bar Juba bayan da rikici ya sake barkewa.

    Sudan ta Kudu

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, An sha tashi baram-baram a tattaunawa tsakanin Salva Kiir (dama) da abokin hamayyarsa Riek Machar
  9. Rashin Tsaro: 'Buhari ba zai yi murabus ba'

    Gwamnatin Najeriya ta ce Shugaba Muhammadu Buhari ba zai yi murabus ba duk kuwa da matsalar tsaron da kasar ke fuskanta a yanzu.

    Ministan watsa labaran kasar Lai Mohammed ne ya bayyana haka ranar Alhamis lokacin da yake yi wa manema labarai jawabi a Abuja, babban birnin kasar.

    Ministan ya kuma mayar da martani kan kiraye-kirayen da wasu 'yan kasar ke yi na cewa shugaban ya sauka daga kan kujerarsa saboda gazawarsa a fannin tsaro.

    A cewar ministan, Buhari ya samu lamincewar jama'a kan tafiyar da harkokin kasar har zuwa karshen wa'adin mulkinsa a Mayun 2023.

    Ministan, wanda ya tabbatar da matsalolin tsaron, ya bayyana cewa gwamnati tana bakin kokari domin magance matsalar.

    Ya kuma shawarci masu fada-a-ji da ke kasar musamman malaman addini da 'yan siyasa da su rika sanin kalaman da za su furta domin kauce wa fadin abubuwan da za su raba kawunan 'yan kasar.

    Wasu 'yan kasar dai sun sha caccakar shugaban kasar musamman saboda, a cewarsu, ya bar harkokin tsaro na sake tabarbarewa.

    Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP ta yi kira ga Shugaba Buhari ya ajiye mukaminsa saboda ya gaza kare rayuwkan 'yan Najeriya.

    Lai Muhammad

    Asalin hoton, Getty Images

  10. Za a tuhumi firai minista kan kisan matarsa

    'Yan sanda a Lesotho sun ce za a tuhumi firai ministan kasar, Thomas Thabane, mai shekara 80, da laifin kisan matarsa Lipolelo Thabane.

    A watan Yuli Mr Thabane ya bayar da sanarwa zai sauyka daga mukaminsa saboda tsufa, ba tare da yin tsokaci a kan zargin kisan matarsa ba.

    Tuni aka tuhumi matarsa ta yanzu Maesaiah Thabane da laifin kisan tsohuwar matar firai ministan.

    Zai kasance shugaban wata kasa a yankin Afirka ta Kudu da aka zarga da irin wannan laifi yana kan mulki, lamarin da ya girgiza 'yan kasar.

    An harbe Lipolelo, 58, har lahira kwana biyu kafin Mr Thabane ya zama firai minista 2017.

    Mr Thabane ya auri Maesaiah a wani kasaitaccen biki a 2017

    Asalin hoton, Getty Images

  11. Ana yi wa majalisar dokokin Najeriya barazanar ta'addanci

    Har yanzu a Najeriya, yayin da ake kukan matsalar tabarbarewar tsaro a sassan kasar, musamman ma shiyyar arewa-maso-gabashi, yanzu kuma majalisar dokokin Najeriya ce ita ma ta ce ita kanta tana fuskantar barazanar ta'addanci.

    Damuwar ta taso ne sakamakon zaman da ake yi kara-zube a majalisun dokokin kasar.

    Wannan ta sa `yan majalisar suka fara wani yunkuri na tsaurara tsaro a mashigun majalisar tare da samar da kayan aiki na zamani, ciki har da kyamarorin tsaro.

    Ga rahoton Ibrahim Isa:

    Bayanan sautiRahoton Ibrahim Isah kan barazanar ta'addanci da ake wa majalisar dokoki
  12. Kwantena ta fado daga kan babbar mota ta kashe mutum 19 a Indiya

    Akalla mutum 19 ne suka mutu a wani hatsari da ya faru a kudancin Indiya, bayan da wata kwantena ta zame daga kan babbar mota ta fada kan motar bas mai dauke da fasinjoji.

    'Yan sanda suna bincike kan lamarin, amma jami'ai sun ce kwantenar ta fado ne bayan da daya daga cikin tayoyin babbar motar ta yi faci.

    ''Akwai kusan mutum 48 a bas din, kuma da yawansu na cikin mummunan yanayi,'' a cewar wani jami'i da ya shaida wa BBC Hindi.

    Lamarin ya faru ne da misalin karfe 3.3o na tsakar dare, daidai da karfe 9.50 agogon GMT, in ji 'yan sanda.

    Bas din tana tafiya ne a kan babbar hanya lokacin da kwantenar ta zame daga kan babbar motar daga daya bangaren titin. Sai ta gangara zuwa daya barin ta yi taho mu gama da bas din.

    Bas din kirar kamfanin Volvo, mallakar kamfanin sufuri na jihar Kerala ce, kuma tana tafiya ne daga birnin Bangalore na jihar Karnataka zuwa Ernakulam na Kerala.

  13. Gwamnatin Sudan Ta Kudu 'tana azabtar da fararen hula da yunwa da gangan', Daga Mary Harper Editar Afirka, BBC World Service

    Wani bincike na hukumar kare hakkin dan adam ta Majalisar DInkin Duniya ya zargi gwamnatin Sudan Ta Kudu da sauran kungiyoyin 'yan bindiga da azabtar da fararen hula da barin su da yunwa.

    Masu bincike sun gano cewa ana toshe duk wasu hanyoyi na shigar da taimakon abinci da sauran ayyyukan bukata da gangan, abin da ke sanya fiye da rabin al'ummar kasar cikin tsananin bukatar abinci.

    Sun ce jami'an gwamnati sun yi ruf da ciki kan miliyoyin dalolin gwamnati, kuma suna tattara shaidu don gabatarwa a kotu nan gaba.

    An wallafa rahoton nasu kwana biyu kafin ranar da aka sa don kafa gwamnatin hadin gwiwa.

    Kokarin cimma yarjejeniya da aka yi ta yi a baya ba su yi aiki ba.

  14. Rwanda da Uganda sun yi musayar fursunoni

    Rwanda da Uganda sun yi musayar fursunoni a yayin da shugabannin kasashen biyu ke shirin ganawa da juna ranar Juma'a domin kawo karshen rashin jituwar difilomasiyyar da ke tsakaninsu, lamarin da ya kai ga rufe iyakokinsu.

    Ranar Laraba an saki 'yan Uganda 20 da ke tsare a gidan yarin Rwanda, kwana guda bayan Uganda ta saki 'yan Rwanda 13 wadanda ta tsare bisa zargin leken asiri da wasu al'amuran tsaro.

    Ma'aikatar harkokin wajen Rwanda ta tabbatar da musayar fursunonin a sakon Twitter da ta wallafa:

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  15. An wanke malamar Uganda daga zargin cin zarafin Shugaba Museveni

    Wata malama kuma mai fafutuka a Uganda Dr Stella Nyanzi ta samu nasarar karar data daukaka a babbar kotun kasar game da samunta da aka yi da cin zarafin Shugaba Yoweri Museveni ta intanet.

    An samu Ms Nyanzi da laifi kan rubutun data wallafa a shafinta na Facebook a Satumbar 2018.

    A Agustan 2019 ne kuma aka yanke mata hukuncin kusan shekara biyu a kurkuku har ma ta kusa kare wa'adin.

    Ms Nyanzi dai ta ki amincewa a yi belinta lokacin da ake sauraron shari'ar kuma tuni ta yi wata tara a gidan yarin lokacin da aka same ta da laifin.

    Uganda
  16. 'Najeriya na bukatar sojoji 100,000 idan tana son murkushe Boko Haram'

    Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, ya ce kasar na bukatar karin kayan aiki da dakarun tsawo idan tana so ta ci galabar kungiyar Boko Haram.

    Gwamna Zulum ya ce kasar na bukatar karin soji 100,000, yana mai karawa da cewa ya kamata a dauki rabi daga cikinsu daga jihar Borno.

    Gwamnan ya shaida wa kwamitin harkokin tsaro na majalisar wakilan Najeriya cewa akwai bukatar kakakin majalisar ya tattauna da shugaban kasar Muhammadu Buhari game da yiwuwar daukar sabbin sojoji masu yawa aiki

    Jihar ta Borno ita ce cibiyar hare-haren mayakan Boko Haram, inda ko a makon jiya sai da wasu da ake zargi 'yan kungiyar ne suka halaka mutum 30 a harin da suka kai a garin Auno.

    Gwamna Zulum ya ce ya kamata a dauki rabi daga cikinsu daga jihar Borno.

    Asalin hoton, AFP

    Bayanan hoto, Gwamna Zulum ya ce ya kamata a dauki rabi daga cikinsu daga jihar Borno
  17. 'Yan Najeriya da India sun yi fim kan soyayya

    Wani fim mai suna 'Namaste Wahala' da aka hada gwiwa wajen shirya shi tsakanin taurarin fina-finan Indiya da takwarorinsu na Najeriya ya ja hankalin 'yan kallo.

    Za a soma nuna fim din ne ranar 24 ga watan Afrilun 2020.

    Tauraruwa Ini Dima-Okojie da tauraron fina-finan Indiya Ruslaan Mumtaz sun yi fim din "wanda yake bayar da labarin wasu masoya da ke nuna al'adun kasashen biyu".

    Fim din ya ja hankalin masu kallo inda suka yi ta tsokaci.

    "Fina-finan Najeriya sun hada gwiwa da na Indiya? Wannan abu ya yi armashi, kuma shi ne fim irinsa na farko," a cewar wani mai amfani da Twitter.

    Kauce wa Instagram
    Ya kamata a bar bayanan Instagram?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da Instagram suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta Instagram da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a Instagram

  18. Buhari na halartar taro kan sake fasalin iyali a Musulunci

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yana halartar taro kan yadda za a sake fasalin iyali a Musulunci.

    Mai taimaka wa shugaban kasar kan shafukan sada zumunta, Bashir Ahmad, ne ya bayyana haka a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter.

    A cewarsa: "Yanzu haka Shugaba Buhari yana halartar taron kasa kan sake fasalin iyali a Musulunci domin ci gaban kasa wanda Majalisar Koli ta addinin Musulunci da hadin gwiwar Gidauniyar Aisha Buhari ta Future Assured suka shirya.

    "Gwamnoni da malaman addini da sarakuna da sauran masu ruwa da tsaki suna halartar taron."

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  19. 'Fiye da yara miliyan daya na cikin matsala a Nijar'

    Bayanan sautiLatsa alamar lasifikar domin sauraron cikakken rahoton Tchima Illa Issoufou

    Sama da yara miliyan daya ne a jamhuriyar Nijar ke fuskantar tabarbarewar rayuwa dalilin wasu matsaloli, a cewar asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF.

    Asusun ya ce matsalolin na da nasaba da tsaro da rashin abinci mai gina jiki da bullar annoba da fari da gudun hijra da kuma ruwan sama.

    Wata sanarwa da asusun ya fitar ranar Laraba na cewa Jamhuriyar Nijar na da yan gudun hijira kimanin dubu dari hudu da hamsin kuma da dama na rayuwa a yankunan da ke fama da talauci.

  20. Najeriya: 'Zazzabin Lassa ya kashe akalla mutum 103 '

    Cibiyar yaki da yaduwar cututtuka a Najeriya ta yi ikirarin cewa zazzabin Lassa ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 103 tun lokacin da ya barke.

    Jaridar Premium Times ta ambato cibiyar na bayyana haka a rahotonta na mako-mako, wanda ta fitar ranar Laraba.

    Cibiyar ta ce an samu karuwar masu kamuwa da cutar da kuma wadanda ke mutuwa sakamakon kamuwa da ita.

    Kusan kowacce shekara ana bayar da rahoton bullar zazzabin Lassa a Najeriya, amma an fi ba da rahoton kamuwa da ita a watannin Nuwamba da Mayu, a cewa cibiyar.

    Ya zuwa ranar 16 ga watan Fabrairu, an samu karuwar sabbin wadanda ke harbuwa da cutar duk mako daga mutum 109 zuwa mutum 115.

    Cibiyar ta ce an samu bullar cutar a jiha 16: Ondo, Edo, Ebonyi, Kano, Kogi, Kaduna, Taraba, Plateau, Bauchi, Enugu, Abia, Benue, Borno, Gombe, Sokoto da kuma Katsina.

    Cibiyar ta ce an samu bullar cutar a jiha 16

    Asalin hoton, AUSCAPE

    Bayanan hoto, Cibiyar ta ce an samu bullar cutar a jiha 16