Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da suka faru a Najeriya da Nijar da sassan duniya

Wannan shafin ya kawo muku labaran abubuwan da suka faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Nabeela Mukhtar Uba

  1. Kungiyar OIC ta yi watsi da shirin Trump na zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya

    Kungiyar hadin kan kasashen Musulmi ta Organisation of Islamic Cooperation (OIC) ta yi watsi da shirin zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya da Shugaban Amurka Donald Trump ya samar.

    Kungiyar kuma ta yi kira ga kasashe mambobinta guda 57 da kada su taimaka wurin aiwatar da shirin.

    Kungiyar ta bayyana hakan ne bayan wani taron ministocin harkokin wajen mambobinta da ta gudanar ranar Litinin a birnin Jeddah na Saudiyya, kamar yadda rahoton jaridar Saudi Gazette ya rawaito.

    OIC wadda ke wakiltar Musulmi kusan biliyan 1.5 a fadin duniya, "ta yi watsi da wannan shiri na Amurka da Isra'ila saboda bai yi la'akari da mafi kankantar abin da Falasdinawa ke muradi ba da kuma hakkokinsu, sannan ya saba wa hanyoyin samar da zaman lafiya," in ji ta a wani bayani da ta fitar.

    "Muna kira ga mambobin wannan kungiya da kada su taimaka ko kuma yin aiki tare da Amurka wurin aiwatar da shi ta kowacce irin hanya."

    A karkashin shirin wanda Trump ya fitar a makon da ya gabata, Isra'ila za ta ci gaba da yin iko da birnin Kudus a matsayin babban birninta "nata ita kadai" sannan kuma ta mallaki wuraren da ta mamaye na Falasdinawa.

    Trump ya ce za a bai wa Falasdinawa damar kafa babban birninsu a cikin yankin da Isra'ilar ta mamaye.

    Saboda haka ne OIC ta jaddada goyon bayanta ga yankin gabashin Kudus a matsayin babban birnin kasar Falasdinu da za a samar nan gaba tare da nanata "alakarta da al'ummar Larabawa da kuma Musulunci".

  2. Cin tafarnuwa ba zai hana kamuwa da coronavirus ba – WHO

    Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya (WHO) ta ce cin tafarnuwa da kuma wanke hanci da ruwan gishiri ba zai kare mutum daga kamuwa daga kwayar cutar coronavirus ba.

    Kamfanin dillancin labarai na NAN ya rawaito cewa hukumar ta wallafa gaskiya da kuma karairayi game da matakan kariya daga cutar a shafinta na intanet ranar Litinin kan sabuwar cutar ta 2019 mai lakabin 2019-nCoV.

    WHO ta ce tafarnuwa abinci ne mai lafiya wanda ke dauke da sinadarin antimicrobial, "sai dai babu wani tabbas kan ko cin tafarnuwar ya kare mutane daga kamuwa daga cutar ta baya-bayan nan wato 2019-nCoV," in ji hukumar

    Kazalika, ta bayyana cewa babu wani tabbaci kan ko wanke hanci da ruwan gishiri akai-akai ya kare su daga cutar ta coronavirus, wadda ta fi kamari a China.

    Coronavirus ta kashe sama da mutum 300 sannan sama da mutum 14,000 suka kamu da ita.

  3. Zabtarewar kasa ta hallaka mutum 13 a Rwanda

    Kimanin mutum 13 ne suka mutu bayan wani mamakon ruwan sama da ya sauka a Rwanda a daren Lahadi abin da ya janyo zabtarewar kasa kamar yadda hukumomi suka ce.

    Shida daga cikin mamatan sun mutu ne a gidajensu da ke Kigali, babban birnin kasar.

    Wani mazaunin Kanombe da ke kusa da babban filin tashi da saukar jiragen sama na Kigali ya bayyana wa BBC cewa makwabciyarsa da ‘ya’yanta biyu sun mutu suna tsaka da barci bayan da zabtarewar kasa ta shafi gidan.

    "Da safe muka gano hakan," a cewarsa. "Ruwan ya yi karfi sosai kuma kowa ta tsorata."

    Hukumar kula da yanayi a kasar ta ce ana hasashen samun karin ruwan sama mai karfin gaske a sassan kasar ranar Litinin.

    ‘Yan sanda kuma na gargadin masu baburan hawa da su rage gudu a lokacin daminar domin kaucewa hadari.

  4. Za a bai wa fararen hula makamai domin yaki da ta'addanci

    Mahukunta a Burkina Faso na fama da karuwar hare-haren masu ikirarin jihadi wanda ke addabar yankin, lamarin da ya sa suke shirin fara bai wa fararen hula makamai.

    Gwamnatin kasar na fuskantar matsin lamba a kan ta dauki sabbin matakai na kawar da 'yan ta'adda.

    A watan Janairun 2020 kadai, an kashe mutum akalla 60 a wasu hare-hare hudu da aka kai a karo daban-daban a arewacin kasar.

    A kwanan nan 'yan majalisar dokokin kasar sun kada kuri'ar amincewa da taimakawa fararen hula a wani yunkuri da suke ganin zai taimaka wajen yaki da masu tayar da kayar baya.

  5. Amurka ta gayyaci shugaban Sudan zuwa kasarta

    Amurka ta gayyaci shugaban kasar Sudan zuwa Washington - a wata ziyara irin ta ta farko cikin shekara 30.

    Sudan ta ce Laftanal Janar Abdel Fattah al-Burhan zai je Amurka ne don tattauna hanyoyin karfafa dangantaka tsakanin su.

    Shi ne shugaban riko na Sudan tun watan Agusta karkashin wata yarjejeniya ta rabon madafun iko wadda za ta tabbatar da mika mulki ga farar hula a shekarar 2021 har zuwa lokacin zabe a 2022.

    Dangantaka ta gyaru tsakanin Sudan da Amurka tun bayan hambare gwamnatin Shugaba Omar al-Bashir a bara.

    Har yanzu Sudan na cikin jerin kasashen da Amurka ta lissafa da ke daukar nauyin ta'addanci, amma Amurkar ta nuna alamun za a iya cire ta daga jerin nan ba da dadewa ba.

  6. An samar wa mata kofin yin fitsari don hana kamuwa da cuta, A Kenya

    Wata mata 'yar kasar Kenya ta samar da wata mafita ga masu fama da irin cututtukan da ake kamuwa da su bayan amfani da bandakunan da ba su da tsafta.

    Njeri Muthaka tana sayar da kofuna da ke taimaka wa mata yin fitsari a tsaye, ba tare da sun tsuguna ba don kare su daga zama kan shadda mara tsafta da za su iya daukar kwayoyin cuta.

    Ms Muthaka ta shaida wa BBC Swahili cewa ta sayo kofunan yin fitsarin ne daga wata kasa bayan da ta yi fama da cututtukan da suka shafi al'aura da mafitsara ba sau daya ba ba sau biyu ba.

    Bayan da ta yi amfani da kofin ta kuma ga muhimmancinsa wajen hana ta sake kamuwa da cutar, sai ta anke shawarar sayar da kofunan.

    Likitoci sun yi amanna cewar kofin fitsarin zai rage kamuwa da cututtuka. Wani likita Chris Obwaka ya ce: "Idan har ba kya zama a kan shadda ta gama-gari don yin fitsari, hakan zai iya rage hadarin kamuwa da cututtuka.

    ''Amfani da kofin zai taimaka sosai.''

    Sai dai mazan Kenya na cewa amfani da kofin ya kauce wa tsarin al'adunsu.

  7. Ghana za ta yi bincike kan zargin cin hanci a kamfanin Airbus

    Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo ya umarci mai shigar da kara na musamman na gwamnati da ya fara bincike a kan zargin badakalar cin hanci da ya hada da kamfanin kera jiragen sama na Airbus da wasu tsofaffin jami'an gwamnatin Ghana.

    Ya bayar da umarnin ne bayan kamfanin na Airbus ya amsa laifin bayar da cin hanci ga wasu tsofaffin jami`an gwamnati Ghana, domin tabbatar da wasu kwantaragai a 2011 da 2015 a gaban wata kotu a Landan.

    Gwamnatin tsohon shugaban kasa John Dramani Mahama ake zargi da wannan badakala, amma tuni jam`iyyar tsohon shugaban kasar ta NDC ta musanta zargin.

  8. Coronavirus: China ta zargi Amurka da jefa fargaba a zukatan mutane

    Gwamnatin China ta zargi Amurka da sanya fargaba a zukatan mutane game da yaduwar cutar numfashi ta coronavirus.

    Ta yi zargin ne bayan da Amurka ta yanke shawarar hana 'yan kasashen wajen da suka ziyarci China a mako biyu da suka wuce cikin Amurka da ma ayyana cutar a matsayin wani babban bala'i na gaggawa

    Zuwa yanzu dai an tabbatar da rahotanni 17,000 na cutar a China. Tuni mutum 361 suka mutu sakamakon kamuwa da cutar a China kawai.

    A wajen China, an tabbatar da mutum 150 da suka kamu da cutar - inda kuma mutum daya ya mutu a Philippines.

  9. Amurka ta gayyaci shugaban Sudan

    Hukumomi a Amurka sun gayyaci shugaban gwamnatin Sudan domin kai ziyara Washington - wannan ne karon farko da wani shugaban kasar zai kai ziyara Amurka cikin fiye da shekara 30.

    Sudan ta ce Laftanar Janar Abdel Fattah al-Burhan zai tafi Amurka nan ba da jimawa ba domin tattaunawa kan abubuwan da kasashen biyu za su ci moriya.

    Tun a watan Agusta ya zama shugaban gwamnatin majalisar kolin Sudan wacce ke karkashin gwamnatin rikon-kwarya da ke raba iko tsakanin soji da farar hula kafin a yi zabe a 2022.

    Dangantaka tsakanin Amurka da Sudan ta fara yaukaka tun bayan da aka kawar da shugaban kasar Omar al-Bashir daga kan mulki a shekarar da ta gabata.

    Har yanzu Sudan na cikin jerin kasashen da ake zargi da daukar nauyin 'yan ta'adda, sai dai Amurka ta ce watakila a cire ta daga jerin nan ba da dadewa ba.

  10. Hotuna kan hana acaba a Lagos

    Karin hotuna kan haramcin hana amfani da babura masu kafa uku a Lagos.

    Mun kawo muku labarin tun dazu don haka ku duba labaranmu na baya domin karanta cikakken bayani.

  11. Akwai jan aiki a gabana—Emmanuel Amuneke

    Tsohon dan wasan Najeriya Emmanuel Amuneke ya ce "akwai jan aiki a gabansa" bayan da ya soma aikin horas da 'yan wasan kungiyar kwallon kafar El-Makkasa da ke buga wasa a rukunin firimiya lig a kasar Masar.

    Ya sanya hannu domin jagorancin kungiyar daga yanzu zuwa karshen kakar wasa ta bana.

    An tabbatar da kocin mai shekara 49 kan wannan mukami ne ranar Asabar domin maye gurbin Ahmed Hossam Mido, kuma kocin kungiyar na hudu cikin shekara uku.

    Amuneke ya shaida wa BBC Sport cewa "Muna da jan aiki a gabanmu don haka ba za mu yi wa kanmu karya cewa komai yana tafiya daidai ba."

  12. Faransa za ta aika karin dakaru 600 yankin Sahel

    Kasar Faransa ta ce za ta aika karin dakaru 600 zuwa yankin Sahel, domin tabbatar da tsaro.

    Hakan ya kawo adadin sojinta 5,100 a yankin.

    Za a aike da akasarin sojojin ne iyakokin kasashen Nijar da Mali da Burkina Faso da ke fama da hare-haren mayaka masu ikirarin jihadi.

    Sai dai duk da haka, masana na ganin jami'an soji da jirage marasa matukan da ake amfani da su a yankin Sahel sun gagara magance matsalar tsaro a yankin.

    A baya-bayan nan mayaka masu alaka da kungiyar al-Qaeda sun zafafa kai hare-hare a kasashen yankin na Sahel.

  13. Yadda aka kama wani matashi da bam a Coci a Kaduna

    Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta ce ta kama wani matashi dauke da ababen fashewa a cikin jakarsa, a Cocin Living Faith da ke Unguwar Sabon Tasha.

    An kama matashin ne a daidai lokacin da mabiya addinin Kirista ke gudanar da ibadarsu a ranar Lahadi.

    Mai magana da yawun 'yan sandan jihar DSP Yakubu Abubakar Sabo ya shaida wa BBC cewa sunan matashin Nathaniel Samuel, kuma ya shiga cocin ne dauke da wata jaka a matsayin wanda ya je ibada.

    Ku latsa alamar lasifika da ke kasa domin sauraren cikakkiyar hira da DSP Sabo:

  14. An fara aiki da dokar hana amfani da Keke Napep a Lagos

    A yau Litinin ne mazauna birnin Lagos da ke Najeriya suka wayi gari da haramcin da gwamnatin jihar ta yi musu na hawa babur mai kafa uku, wanda aka fi sani da Keke Napep ko Marwa ko A Daidaita Sahu.

    Wakilan BBC sun aiko mana da hotuna da ke nuna mutane cirko-cirko suna jiran ababen hawa.

    Galibi dai an fi yin amfani da wadannan babura wajen yin sufuri a birnin.

    A watan jiya ne gwamnati ta haramta amfani da acaba Opay da GOKADA da Maxkeke.

    Gwamnatin jihar ta ce ta haramta aikin masu baburan ne saboda karya doka da hadurran da masu sana'ar ke haddasawa.

    Sai dai masu haya da baburan sun yi zanga-zanga domin nuna bijirewarsu ga wannan haramci.

  15. ‘Yan Najeriya kusan 245 ne suka mutu a watan Janairu

    Kimanin ‘yan Najeriya 245 ne suka mutu sakamakon hare-hare da aka kai musu a watan Janairu na shekarar 2020.

    Jaridar PremiumTimes da ake wallafawa a shafin intanet ta ambato wani bincike da kungiyar da ke bin diddigin harkokin tsaro mai suna Expat Insider Survey of 2019 by InterNations ke cewa Najeriya ce kasa ta uku da ke fama da matsanacin matsalar tsaro da cin hanci da rashawa.

    Kungiyar ta kara da cewa binciken da ta gudanar a fadin kasar ya nuna dalla-dalla kan yadda wuraren da aka kai hare-haren da kuma mutanen da aka kashe.

  16. Barkanmu da warhaka, Labaran ranar Litinin 3 ga waan Fabrairun 2020

    Muna yi wa masu bibiyarmu fatan kun wayi gari lafiya. Da fatan za ku kasance tare da mu a wannan rana ta Litinin domin jin wainar da ake toyawa a Najeriya da Nijar da makwabta har ma da sauran kasashen duniya.

    Nasidi Adamu Yahaya ne zai dinga kawo muku labaran wainar da ake toyawa kafin daga wasu abokan aiki su karbe shi.