Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da suka faru a Najeriya da Nijar da sassan duniya

Wannan shafin ya kawo muku labaran abubuwan da suka faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Nabeela Mukhtar Uba

  1. Twitter ya fito da ka'idojin yaki da labaran karya

    Shafin Twitter ya fito da wasu sabbin ka'idoji domin maganin yada labaran karya ko masu karin gishiri a dandalin.

    Manufar wannan matakin ita ce yin maganin matsalar saka bidiyo-bidiyo na bogi da aka hada ta hanyar amfani da na'ura mai kwalkwalwa, inda ake sauya kamannin mutum ko kuma furucinsa.

    Twitter din zai fara aiwatar da wadannan ka'idojin a watan Maris.

    Twitter ya ce ya dauki matakin ne sakamakon wani bincike na baya-bayan nan, wanda ya ji ra'ayoyin mutum 6,500.

    An zabo mutanen daga kungiyoyin farar hula da malamai da kuma jama'ar gari.

    Matakin na Twitter na zuwa ne kusan wata guda bayan Facebook ya sanar cewa zai cire bidiyo-bidiyo da aka sauya asalinsu ta hanyar amfani da ma'aikatansa da kuma masu bincike don tantance sahihancin bidiyo-bidiyo din.

  2. 'Tabarbarewar siyasa na rura rikicin makiyaya da manoma a Najeriya'

    Masana a Najeriya sun dora laifin ta'azzarar da rikicin makiyaya da manoma ya yi kan tabarbarewar tsarin siyasa a kasar.

    Shugaban cibiyar habaka ci gaban arewacin Najeriya ta Arewa Research and Development Center Dakta Usman Bugaji ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da BBC.

    Ya ce akwai bukatar a yi gyara a tsarin shugabancin kasar domin dakile irin wadannan rikice-rikice.

    A cewarsa tsarin shugabancin da ake yi a Najeriya a yanzu, ya kara gurbata abubuwa a kasar.

    Da yake tsokaci game da dokar da gwamnatin Najeriya ta fitar ta National Livestock Transformation Act, Bugaje ya bayyana cewa ''Ko ka yi tsari mai kyau, sai ka koma ka gyara shugabanci.''

    Ya kara da cewa: ''A yadda siyasar take tafiya ba za ka samu shugabanni masu kyau ba sai ka koma ka gyara yadda ake zaben shugabanni.''

  3. Cristiano Ronaldo ya cika shekara 35 da haihuwa

    Dan wasan tawagar kwallon kafar Portugal da Juventus, Cristiano Ronaldo ya cika shekara 35 da haihuwa ranar Laraba.

    An haifi Ronaldo dos Santos Aveiro ranar 5 ga watan Fabarairun 1985 a Funcal, Madeira da ke Portugal.

    Dan wasan ya fara murza leda a karamar kungiyar Sporting ta Portugal, daga nan ya koma taka leda cikin manyan 'yan wasa a 2000.

    Ya fara buga wa kasarsa Portugal wasa a shekarar 2001.

    Kungiyoyin da ya buga wa tamaula:

    2002-2003 Sporting

    2003-2009 Manchester United

    2009-2018 Real Madrid

    2018- Juventus

  4. Khamenei ya caccaki shirin Trump kan Gabas ta Tsakiya

    Jagoran addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya sake yin kakkausar suka kan shirin gwamnatin Trump na zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya da kuma kasashen Larabawa wadanda suka nuna goyon baya ga wannan tsarin a fakaice.

    Ayatollah Khamenei ya ce shirin da aka kira yarjejeniyar sabon karni zai riga Trump mutuwa.

    Falasdinawa dai sun yi fatali da shirin wanda Mista Trump ya gabatar a kwanakin baya.

    Amma an sami martani kalilan na kin amincewa da shi daga wasu kasashen Larabawa, abin da a fakaice ya inganta dangantakarsu da Isra'ila domin yakar Iran wadda suke gani a zaman abokiyar gabarsu.

    Ita ma kungiyar hadin kan kasashen Musulmi ta OIC ta yi watsi da shirin a makon nan, inda ta jaddada goyon bayanta ga Falasdinawa da kuma cewa "biinin Kudus na kasar Falasdinu ne" ba Isra'ila ba, kamar yadda shirin ya nuna.

  5. Za a gudanar da kuri'ar raba gardama kan kundin tsarin mulkin Guinea

    Firai Ministan Guinea, Alpha Conde, ya ba da sanarwar cewa za a gudanar da kuri'ar raba gardama kan kundin tsarin mulki a ranar daya ga watan Maris - ranar da za a gudanar da zaben majalisar dokokin kasar.

    ‘Yan adawa na fargabar zai yi amfani da ranar a matsayin wata hujja ta neman rike madafun iko fiye da wa’adin mulkinsa na shekara biyu, wanda zai kare a wannan shekarar.

    Wata gamayyar kungiyoyin 'yan adawa da masu fafutuka sun ce za su yi kokarin hana kada kuri’ar.

    An yi zanga-zangar adawa a Guinea a cikin ‘yan watannin da suka gabata kan adawa da canjin tsarin mulki, inda aka kashe mutane da dama.

  6. An yi umarnin yi wa tsarin rijistar layin waya garambawul

    Gwamnatin Najeriya ta umarci hukumar sadarwar kasar da ta gaggauta yi wa tsarin rajistar layin waya garambawul da kuma yadda ake amfani da shi.

    Ministan sadarwa na kasar, Isa Ibrahim Pantami ne ya bayar da umarnin cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mataimakinsa na musamman kan fasahar sadarwa Dr Femi Adeluyi ranar Laraba.

    Ya ce umarnin ya zo daidai da ikon da yake da shi a matsayinsa na minista kamar yadda yake kunshe a sashe na 25(1) na dokar sadarwar Najeriya ta 2003.

    A cewar sanarwar, "an dauki matakin ne saboda yawan korafe-korafen da hukumomin tsaron kasar ke yi game da yadda aka yi gyare-gyare kan wasu layukan waya a Satumbar 2019 da kuma toshe layukan wadanda suka gaza yin rajista."

  7. Mutum biyu sun kamu da coronavirus a Malaysia

    Malaysia ta tabbatar da mutuwar 'yan kasarta biyu daga cikin wadanda aka kwashe daga birnin Wuhan bayan sun kamu da cutar coronavirus.

    Ministan lafiya na kasar, Dzulkefly Ahmad, ya ce “mutanen biyu basu nuna wata alamar kamuwa da cutar ba lokacin da aka tantance su jim kadan da jirginsu ya sauka a kasar ranar Talata,“ a cewar jaridar The Star.

    Jaridar ta kuma rawaito cewa gwajin da aka yi wa 'yan uwan marasa lafiyar ya nuna cewa basu kamu da cutar ba.

    Ministan lafiyar ya kuma bai wa 'yan jarida tabbacin killace sauran fasinjojin har tsawon mako biyu kamar yadda sauran kasashe suke yi wa 'yan kasarsu da suka dawo daga China.

    Ahmad ya ce wani mutum da dansa daga cikin fasinjoji 108 da suka dawo daga Wuhan sun kamu da cutar ta coronavirus.

  8. An tsige shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Kano

    'Yan majalisar dokokin jihar Kano da ke arewacin Najeriya sun tsige shugaban masu rinjaye na majalisar Labaran Abdul Madari.

    Abdul Madari, wanda ke wakiltar karamar hukumar Warawa da ke jihar, ya shaida wa wakilin BBC da ke Kano, Khalifa Dokaji cewa 'yan majalisar tamkar sarakai ne don haka suna da 'yancin cire shi sannan su zabi wanda suke so.

    Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Bunkure, Muhammed Uba Gurjiya ne ya gabatar da kudirin tsige shi a zauren majalisar.

    Gurjiya ya ce batun na da matukar muhimmanci, yana mai yin kira ga 'yan majalisar karkashin jam'iyyar APC sun amince da kudirin.

    Da yake nuna goyon baya ga kudirin a madadin 'yan jam'iyyar APC, dan majalisar da ke wakiltar Sumaila Zubairu Hamza Massu ya ce 'yan jam'iyyar APC a zauren majalisar sun amince da kudirin tsige shugaban masu rinjayen kuma tuni suka zabi mataimakinsa Alhaji Kabiru Hassan Dashi a matsayin wanda zai maye gurbinsa.

    Ya kara da cewa an zabi Tasi'u Ibrahim Zabainawa a matsayin sabon mataimakin shugaban masu rinjayen na majalisar.

    Wata majiya ta tabbatar wa BBC cewa an cire Labaran Madari ne saboda karfin da yake da shi a majalisa wadanda wasu 'yan majalisar ke ganin bai kwanta musu a rai ba.

  9. Hotuna: Yadda aka gudanar da zaman majalisar zartarwar gwmanatin Najeriya

    Hotunan yadda zaman majalisar zartarwar gwamnatin Najeriya ya gudana ranar Laraba.

    Shugaba Buhari ne ya jagoranci zaman a fadarsa da ke Abuja, babban birnin kasar.

  10. Janar Babangida ya yi alhinin rasuwar arap Moi

    Tsohon shugaban mulkin soji na Najeriya, Ritaya Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya bayyana kaduwarsa dangane da samun labarin rasuwar Daniel arap Moi.

    Tsohon janar din, ya shaida wa BBC cewa mutuwar arap Moi, babban rashi ne ga dukkan 'yan Afirka.

    Ibrahim Badamasi Babangida, wanda ya yi mulkin Najeriya a lokacin da arap Moi ma ke mulkin Kenya ya ce, kasar Kenya da ma Afirka gaba daya sun yi babban rashi bisa la'akari da abubuwan da ya aikata.

    Tsohon shugaban na Najeriya ya ce " Moi ya na daya daga cikin wadanda suka kafa kungiyar OAU, wato kungiyar hadin kan kasashen Afirka".

    Ya ce a lokacin da ya ke shugaban Kenya shi kuma ya ke shugabancin Najeriya, akwai kyakkyawar alaka a tsakanin kasashensu biyu.

  11. Kashi casa'in na mutanen da Boko Haram ta kashe Musulmi ne—Buhari

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya shaida wa kafafen watsa labarai cewa akasarin mutanen da mayakan Boko Haram suka kashe Musulmi ne, yana mai cewa burin 'yan kungiyar shi ne su yi amfani da addini wajen raba kan 'yan kasar.

    A wata makala da ya rubuta wacce aka wallafa a jaridar Christianity Today, Shugaba Buhari ya ce bai kamata a kyale mayakan Boko Haram su raba kan 'yan Najeriya ba.

    "A hakikanin gaskiya, kashi casa'in cikin dari na mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa Musulmi ne: cikinsu har da 'yan makaranta mata musulmi 100 wadanda aka sace tare da takwararsu kirista guda daya, da kai hare-hare a masallatai da kuma kashe fitattun malaman addinin Musulunci."

    Wadannan 'yan ta'adda suna so su gina katanga da za ta raba tsakaninmu. Sun gaza a yunkurinsu na hare-haren ta'addanci, don haka yanzu suna so su raba kanmu ta hanyar sanya mu sukar juna."

    Shugaban kasar ya rubuta makalar ne domin yin jaje da alhinin kisan da wasu da ake zargi mayakan Boko Haram ne suka yi wa wani limamin Kirista, Rabaran Lawan Andimi bayan da suka sace shi.

  12. Gwamnatin Ganduje ta rufe kamfanin Sani Danja

    Fitaccen tauraron fina-finan Kannywood, Sani Danja, ya yi zargin cewa hukumar tace fina-finan jihar Kano ta rufe kamfanin daukar hotonsa saboda siyasa.

    Sai dai hukumar ta ce ta dauki matakin ne saboda kamfanin bai cika sharudanta na yin rijista ba.

    Tauraron ya shahara wajen goyon bayan tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da jam'iyyar PDP da ke hamayya a Kano, wanda ya raba gari da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje tun bayan zaben 2015.

    A wata tattaunawa da ya yi da BBC, tauraron ya ce, "Babu wata maganar yin rijista, akwai da ma mutanen da ake hakonsu saboda dalilai na siyasa."

    Sani Danja ya ce sai da ya yi rijista da dukkan hukumomin da ke kula da harkokin kasuwanci kafin ya bude kamfanin daukar hoton, ciki har da Hukumar rijstar harkokin kasuwanci ta Najeriya, Corporate Affairs Commissioin.

    Sai dai shugaban hukumar tace fina-finai ta Kano, Malam Isma'ila Na'abba Afakallah ya shaida wa BBC cewa ba makarkashiyar siyasa ce ta sanya suka rufe kamfanin tauraron ba, yana mai cewa rashin yin rijista ne.

    "Babu wani gida[na daukar hoto] da muka rufe don yana daukar hoto; mai yiwuwa idan gidan daukar hoton wanda kake magana a kai [Sani Danja] ya fado cikin wadanda basu yi rijista ba, to an rufe shi," in ji shi

  13. Aisha Buhari da Turai Yar’adua sun gana kan cin zarafin mata

    Mai dakin shugaban Najeriya, Aisha Buhari da matar tsohon shugaban kasar, Turai Yar'adu sun gana a fadar shugaban kasar.

    A wani sako da ta wallafa a shafinta na Instagram ranar Talata, Aisha Buhari ta ce sun tattauna kan babutuwa da dama ciki har da cin zarafin mata da shan miyagun kwayoyi.

    "Na ji dadin ganin Mrs. Yar'adua cikin koshin lafiya, kuma mun tattauna kan batutuwa da dama da suka hada da cin zarafin mata da shan miyagun kwayoyi da ci gaban matasa a Najeriya," in ji ta.

    Ta kara da cewa ta saurarin ra'ayin matar tsohon shugaban kasar kan wadannan batutuwa, inda kuma ta kewaya da ita bangarorin fadar shugaban kasar, lamarin da ya tuna mata lokacin da take fadar.

  14. Buhari ya mika ta'aziyyar rasuwar jakadan Saudiyya a Najeriya

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya mika ta'aziyyar rasuwar jakadan Saudiyya a Najeriya, Adnan Mahmoud, ga Sarki Salman na Saudiyya, inda ya bayyana ta da "rashin babban aboki ga Najeriya".

    Buhari ya ce jakadan yana daya daga cikin wakilai mafiya kwazo da ya taba yin aiki da su, a cewar mai magana da yawun fadar shugaban kasa malam Garba Shehu.

    A ranar Talata ne ofishin jakadancin Saudiyya a Najeriya ya bayar da sanarwar mutuwar Ambasada Adnan bin Mahmoud Bostaji.

    Sai dai sanarwar ba ta yi wani karin bayani a kan abin da ya janyo mutuwar tasa ba.

  15. Shugaban kasar Algeria ya yi wa dubban fursinoni afuwa

    Shugaban kasar Algeria Abdelmadjid Tebboune ya yi afuwa ga fursunoni sama da 3,000 wadanda aka yanke hukuncin da bai da tsawo a gidan maza, a yunkurinsa na neman goyon bayan 'yan kasar bayan an kwashe watanni ana rikicin siyasa.

    An sha kama daruruwan masu zanga-zangar kyamar gwamnatinsa.

    Shugaba Tebboune ya lashe zabe a watan Disamba ko da yake dubban 'yan asar sun yi watsi da zaben nasa suna amsu neman dukkan wani mutum da ya yi aiki da gwamnatin baya ya sauka daga kan mukaminsa.

    Mr Tebboune ya zama firayim minista a 2017 bayan ya kwashe shekaru da dama yana aikin gwamnati. Ya taba zama ministan gidaje da na yada labarai.

    Shi amini ne ga tsohon shugaban kasar Algeria Abdelaziz Bouteflika, wanda aka kora daga kan mulki.

  16. Mai hannu daya tana daukar hoto

    Wata ‘yan kasar Congo mai sana’ar daukar hoto da mahara suka guntule hannunta daya ta shaida wa BBC Swahili yadda ta kafa kamfanin daukar hoto.

    Yanzu dai Patience Dositha, wadda ke da kamfanin daukar hoto mai suna Abled Photography, tana zaune ne a kasar Kenya.

    Ta bar Jamhuriyar Dimokradiyyar tana yarinya karama bayan da aka kashe mahaifiyarta a wani hari, sannan aka ji wa mahaifinta munanan raunuka har ma ya nemi wasu mutane da ke wucewa a wancan lokacin su dauki ‘yarsa su tafi da ita inda za ta tsira.

    Daga nan ne wata mata da ta ceto ta ta dauki Patience zuwa Rwanda, ko da yake ‘ya’yan matar sun kore ta daga gidan da ta girma bayan mahaifyarsu ta mutu ita kuma Patience ta kammala makaranta.

    Daga nan ne ta hadu da wani ya dauke ta a mota zuwa Gabashin Afirka, inda kuma ya shiga da ita kasar Kenya.

    "Da muka iso sai ya ba ni dala biyar, ko da yake daga bisani sun kare ta yadda na soma kwana inda kuma nake samun abinci daga wuraren zubar da shara." In ji ta.

    Daga bisani Patience ta hadu da kungiyar bayar da agaji ta International Rescue Committee wacce ta dauki nauyinta wurin koyon daukar hoto.

  17. Barkanmu da wannan lokaci

    Daga nan Sashen Hausa na BBC muke yi muku barka da wannan lokaci. Da fatan za ku bibiye mu domin jin halin da ake ciki a Najeriya da Nijar da makwabtansu har ma da wasu sassan duniya. Mun gode

  18. Sharadin da Amurka ta gindaya wa Najeriya kan kudin sata

    Gwamnatin Amurka ta shardanta wa Najeriya cewa muddin ta bari aka sace kudin da take shirin dawo mata da su yayin aikin da aka tsara za a gudanar da su to sai ta biya.

    A ta bakin mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar, Amurka ta shardanta cewa Najeriya za ta biya duk wani kudi da aka sace yayin gudanar da aiyukan raya kasa da aka karbo kudin dominsu, kamar yadda suka yi yarjejeniya.

    Gwamnatin Najeriya ce ta wallafa wannan sanarwar a shafinta na Twitter a ranar Talata.

    Ranar Lahadi ne Ministan Shari'ar Najeriya, Abubakar Malami, ya je birnin Washington na Amurka domin saka hannu kan yarjejeniyar dawo da kudin da tsohon shugaban mulkin soji Sani Abacha ya sace kuma ya jibge su a can.

    Kudin sun kai dalar Amurka miliyan 308, kwatankwacin kusan naira biliyan 112.

  19. An tuhumi matar firai minista da kisan kishiyarta

    An tuhumi matar firaministan kasar Lesotho da kisan kishiyarta, wadda suka rabu da shugaban.

    Tun farko Uwar Gida Maesaiah Thabane ta kai kanta ofishin 'yan sanda domin a yi mata tambayoyi a kasar da ke kudancin Afirka.

    Shi ma Firaminista Thomas Thabane an yi masa tambayoyi game da kisan tshohuwar mai dakin nasa.

    An harbe Lipolelo Thabane a kofar gidanta a babban birnin kasar Maseru kwana biyu kafin a rantsar da shi a matsayin firaminista a shekarar 2017. A lokacin, ma'auratan suna yunkurin rabuwa da juna.

    An daura wa wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba alhakin kisan, sai dai takardun bayanan da aka gabatar wa kotu a kwanan nan sun saka ayoyin tambaya.

    An bayar da umarnin kama Maesaiah Thabane mai shekara 42 a ranar 10 ga watan Janairu bayan ta yi batan dabo.

  20. Mikel Obi ya sha kalaman wariya a Turkiyya

    Kungiyar Trabzonspor ta yi tir da kalaman wariyar da aka yi wa Mikel Obi, bayan da suka doke Fenerbahce 2-1 a gasar Turkiya ranar Asabar.

    Tsohon dan wasan Chelsea, mai shekara 32, ya sha kalaman wariya a kafar sada zumunta, bisa komawa Trabzonspor da ya yi maimakon Fenerbahce.

    Trabzonspor ta ce ta shigar da karar wadanda suke zargi ga hukuma domin a dauki matakin shari'a.

    ''Kalaman wariyar launin fata ba su dace ba kuma rashin ilimi ne,'' kamar yadda Trabzonspor ta wallafa a shafinta na Twitter.

    Abokin Mikel da suke taka leda tare a Trabzonspor, Joao Pereira, ya ce abin takaici ne kuma ba abin da za a amince da shi ba ne.

    Pereira ya kara da cewar: ''Kwallon kafa tana da girman da ta dara tsirarun mutane da suke yin kalaman wariya'.