'Rashin iska ne ya kashe daliban da suka a turmutsin Kenya'
Rahotanni daga Kenya na cewa shida daga cikin dalibai 14 da suka mutu sakamakon turmutsitsin da aka yi a yammacin kasar sun mutu ne sakamakon rashin iska kamar yadda gwajin da aka yi kan gawarwakinsu ya tabbatar.
Wani likita Dickson Mchana ya ce tawagarsa na ci gaba da gudanar da bincike kan musabbabin mutuwar sauran daliban takwas a turmutsitsin da aka yi a makarantar firamare ta Kakamega da yammacin Litinin.
Dakta Mchana ya kara da cewa ''lokaci na neman kure musu yayin da suke neman karasa binciken sannan su shirya gawarwakin domin iyalan mamatan su karbe su domin yi musu jana'iza a filin wasa na Bukhungu da ke Kakamega.''
'Yan sanda su ma suna gudanar da nasu binciken kan lamarin da ya yi sanadiyyar raunata wasu daliban 39.
Sun samu bayanai daga malamai da dalaibai da wasu da abin ya faru kan idonsu domin gano abin da ya haddasa turmutsitsin.
Biyu daga cikin daliban dai na samun kulawa a asibitin Kakamega.