Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da suka faru a Najeriya da Nijar da sassan duniya

Wannan shafin ya kawo muku labaran abubuwan da suka faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Nabeela Mukhtar Uba

  1. Za a daure 'yan kasuwar da ke rufe fuskokinsu saboda coronavirus

    Gwamnatin Koriya ta Kudu ta ce 'yan kasuwa da ke lullube fuskoki da sauran kayayyakin da aka yi amfani da su don kare kansu daga kamuwa da coronavirus za su fuskanci daurin gidan yari na shekara biyu.

    Hukumomin kasar sun ce za a gurfanar da masu shago a yayin da suka yi ajiyar kaya na sama da sau daya da rabin adadin kayayyakin da suke saidawa na wata-wata a kan wasu kayayyaki, wanda kuma ya hada da sinadaran tsaftace hannu.

    An tabbatar da bullar coronavirus a Koriya ta kudu bayan da aka gano mutane 16 da suka kamu da ita.

    Babban kamfanin kera motoci na kasar, Hyundai, ya dakatar da duk ayyukan da ake yi a cikin gida, saboda ya kasa samar da wasu kayayyaki masu mahimmanci daga China.

  2. Coronavirus ba ta kai matsayin annoba ba – WHO

    Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce cutar Coronavirus da ta bulla a kasar China ba za a iya ayyana ta a matsayin annoba ta duniya ba.

    Dakta Sylvie Briand ta ce cutar ta bazu zuwa kasashe 23 amma har yanzu babu tabbacin cewa ta canza.

    Dakta Briand ta ce yanzu haka ana gudanar da gwaje-gwaje domin dubawa ko maganin da ake bai wa masu cutar AIDS za a iya amfani da shi ga masu dauke da cutar Coronavirus.

    Amma ta yi gargadin cewa babu wata tabbatacciyar shaida da ke nuna cewa irin wadannan magunguna suna da tasiri.

    A baya-bayan nan dai hukumomin kasar ta China sun ce mutane 64 sun mutu daga kwayar cutar a cikin sa'oi 24 da suka gabata, wanda ya kawo adadin zuwa 425.

  3. Coronavirus: An yi watsi da bukatar kwashe 'yan Najeriya daga China

    Majalisar wakilan Najeriya ta yi watsi da kiran da wasu suke yi na kwashe ‘yan kasar da ke China yayin da coronavirus ke bazuwa daga kasar ta China zuwa wasu kasashen duniya.

    Shugaban kwamitin majalisar kan yada labarai, Mr Benjamin Kalu ne ya gabatar da kudirin inda ya nemi a kwaso ‘yan Najeriya da ke China sakamakon annobar ta coronavirus.

    Sai dai ‘yan majalisar basu amince da kudirin ba.

    Kokarin kakakin majalisar, Femi Gbajabiamila, na ganin ‘yan majalisar sun saurari abin da kudirin ya kunsa ya ci tura.

  4. Hukumar kwastam ta kama $8m a filin jirgin saman Lagos

    Hukumar yaki da fasa kauri ta Najeriya ta ce ta kama $8,065,615 a filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Lagos.

    Shugaban hukumar, Hameed Ali, ne ya bayyana haka a wurin taron manema labarai da ya gudanar ranar Talata a birnin na Lagos.

    Ya kara da cewa an kama kudin ne a cikin wata mota ana dab da shigar da kudin cikin wani jirgi.

    Kakakin hukumar Mr Joseph Attah ya shaida wa BBC cewa baya ga wadannan makudan kudi da aka kama, hukumar ta kuma kama karin wasu kudin.

    Sai dai ya ce nan gaba kadan zai yi mana karin bayani.

    Sau da dama hukumar tana kama makudan kudi a filayen jiragen saman kasar, galibi ana dab da sanya su a cikin jirgi.

    Najeriya na cikin kasashen da cin hanci da rashawa da kuma safarar haramtattun kudi suka yi wa katutu.

  5. Netanyahu ya yi ganawa mai cike da tarihi da shugaban Sudan

    Firai Ministan Isra'ila Benjamin Nethanyahu ya yi ganawa mai cike da tarihi da shugaban gwamnatin Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan.

    Hakan alama ce ta farko da ke nuna cewa za su kulla dangantaka mai karfi bayan tumbuke tsohon shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir daga kan mulki a 2019.

    Al-Bashir ya shahara wajen sukar Isra'ila, kuma an zargi gwamnatinsa da bai wa kungiyar Hamas ta Falasdinawa makamai.

    Kazalika Sudan na cikin jerin kasashen da Amurka ke zargi da daukar nauyin ta'addanci saboda shugaban al-Qaeda Osama bin Laden ya taba zama a kasar.

    Mr Nethanyahu ya kai ziyarar kwana daya a Uganda, inda Shugaba Yoweri Museveni ya karbi bakuncinsa.

    Janar Burhan ya tafi kasar ta Uganda inda a can ya gana da Firai Ministan na Isra'ila.

    A wani sakon Twitter da ya wallafa a harshen Hebrew, Mr Netanyahu ya ce shi da Janar Burhan sun amince "su bayar da hadin kai domin dawo da alaka mai yauki tsakanin kasashen biyu.

  6. Iran ta yanke wa wani mutum hukuncin kisa saboda yi wa CIA aiki

    Kotun kolin Iran ta tabbatar da hukuncin kisa ga wani mutum da aka samu da laifin yi wa hukumar CIA aikin leken asiri.

    Amir Rahimpour "ya samu makudan kudade" don bai wa Amurka bayanai game da shirin nukiliyar Iran, a cewar mai magana da yawun ma'aikatar shari'a Gholamhossein Esmaili.

    Ya kara da cewa an yanke wa "wasu karin Amurkawa biyu" hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara 10 saboda leken asiri da karin shekara biyar saboda yi wa tsaron kasa barazana.

    Sai da Mr Esmaili bai bayyana sunayensu ba.

    Kawo yanzu, gwamnatin Amurka ko CIA basu ce komai ba game da batun.

  7. Buhari ya gabatar da tsarin ba da bizar Najeriya

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar da tsarin ba da takardar biza ta Najeriya.

    Mai taimaka wa shugaban kasar kan kafafen sada zumunta na zamani, Bashir Ahmad ne ya bayyana hakan a shafinsa na Twitter.

    Buhari ya gabatar da tsarin ne a fadarsa da ke Abuja, babban birnin kasar.

  8. Kotu ta ba da izinin kama Jacob Zuma na Afirka ta Kudu

    Babbar kotun Pietermaritzburg karkashin Alkali Dhaya Pillay ta ba da sammacin kama tsohon Shugaban kasar Afirka ta Kudu Jacob Zuma bayan kin bayyana gaban kotu.

    Zuma, wanda ake tuhuma da aikata laifuffuka da dama ciki har da cin hanci da sama da fadi da kudade, ana sa rai zai bayyana a gaban kotu ranar Talata sai dai bai samu halarta ba saboda rashin lafiya da yake fama da ita, a cewar lauyoyinsa.

    Lauyan gwamnati Billy Downer ya ce kotun za ta bukaci gamsar da kanta game da rashin lafiyar ta Mr Zuma ta hanyar yin bincike.

    Sammacin zai fara aiki ne idan kotu ta gane cewa Zuma ya ba da bayanin karya game da lafiyarsa kuma ya ki zuwa kotu ranar 6 ga watan Mayu.

    An tuhumi Mista Zuma da laifin rashawa da ke da alaka da yarjejeniyar makamai ta 1990.

  9. Karfin soji ba zai samar da zaman lafiya ba-Jonathan

    Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce tarin makaman nukilya da bindigogi ba shi ne zai samar da zaman lafiya a duniya ba.

    Mr Jonathan, wanda ya bayyana haka ranar Litinin a wurin wani taron kasashen duniya mai taken World Summit 2020 a birnin Seoul na Koriya ta Kudu, ya kara da cewa zaman lafiyar duniya "yana samuwa ne a cikin zukatanmu."

    "Ya kamata mu binciki zukatanmu sannan ko da yaushe mu nuna so da kauna domin kare mutanenmu."

    Tsohon shugaban na Najeriya ya sha yabo sosai lokacin da ya amince da shan kaye a zaben shugaban kasa na 2015, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya lashe.

  10. Birtaniya za ta haramta sayar da motoci masu amfani da fetur

    Gwamnatin Birtaniya ta gabatar da sauyi kan shirin haramta sayar da motoci masu amfani da man fetur ko dizel a kasar.

    Shirin, wanda a baya gwamnatin ta ce za ta fara a 2040, yanzu ta matso da shi zuwa 2035.

    Sauyin na zuwa ne bayan da kwararru suka ce idan har Birtaniya na son cimma kudirinta na rage yawan iskar carbon nan da shekarar 2050, to kuwa haramta irin motocin a 2040 zai kasance a kurarren lokaci.

    Firai Minista Boris Johnson zai gabatar da wannan manufar a wani taron koli kan dumamar yanayi na Majalisar Dinkin Duniya da za a gudanar a watan Nuwamba.

    Zai bayyana cewa taron wata babbar dama ce ta "kara kaimi" don kare duniya.

    Ana gudanar da taron mai taken COP26 kowace shekara wanda Majalisar Dinkin Duniya take jagoranta domin tantance irin ci gaban da aka samu kan shawo kan matsalar sauyin yanayi.

  11. Amurka za ta mayar wa Nigeria $300m cikin kudin da Abacha ya sace

    Gwamnatin Amurka ta ce za ta mayar wa Najeriya karin sama da $300m da tsohon shugaban mulkin sojin kasar marigayi Janar Sani Abacha ya sace.

    Amurkar ta ce an yi safarar kudin ne a lokaci da kuma bayan mulkin Janar Abacha, wanda ya rasu a shekarar 1998.

    Gwamnatin Birtaniya ce ta kwace kudin da aka boye a tsibirin Jersey bayan shari'ar da aka yi ta yi kan batun - ciki har da kalubalantar Amurka a shekarar 2014.

    Ma'aikatar shari'ar Amurka ta ce marigayi Abacha da 'yan korensa sun wawure dukiyar 'yan Najeriya, tare da karya dokokin kasa da kasa ta hanyar boye kudaden.

    Ma'aikatar ta ce tana kokarin sake gano wasu karin kudaden Najeriyar da aka sace.

  12. Nigeria: Za a soma sayar da tikitin jirgin kasa ta intanet

    Majalisar zartarwar Najeriya ta amince da wata kwangila da za ta bai wa ‘yan kasuwa damar sayar da tikitin jirgin kasa ta intanet.

    Majalisar ta dauki wannan mataki ne a taron da ta yi ranar Laraba a fadar shugaban kasar da ke Abuja.

    Mai taimaka wa Shugaba Muhammadu Buhari a shafukan sada zumunta, Bashir Ahmad, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa za a soma sayar da tikitin jirgin ta intanet ne a wuraren sayen tikiti na jiragen da ke jigila tsakanin Abuja da Kaduna.

    Da ma dai ‘yan kasar sun jima suna kokawa kan zargin da ake yi wa wasu ma’aikatan tasoshin jirgin da hada baki da ‘yan ka-yi-na-yi wajen sayar da tikitin jirgin cikin farashin da ya wuce kima.

  13. 'Yan Boko Haram sun yi kisa a Kamaru

    Rahotanni daga kasar Kamaru na cewa mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hari garin Mozogo da ke Arewa mai nisa inda suka kashe mutum biyu.

    Ko da yake har yanzu ba a kai ga tantance girman barnar da suka yi ba, amma wakilinmu ya ce mayakan sun matsa kaimi wurin kai hari a yankin.

    Kasar Kamaru, wadda ke makwabtaka da Najeriya, na fama da hare-haren mayakan na Boko Haram.

  14. Tsohon shugaban Kenya Daniel arap Moi ya mutu

    Tsohon shugaban kasar Kenya Daniel arap Moi ya mutu yana da shekara 95 a duniya.

    Shugaban kasar ta Kenya Uhuru Kenyatta ya tabbatar da mutuwar tsohon shugaban kasar a wata sanarwa da ya fitar da asubahin Talata.

    Mr Arap Moi ya dade yana jinya inda aka yi ta kwantar da shi a asibiti a lokuta daban-daban.

    Ko a watan Nuwambar 2019 an yi ta yada jita-jitar mutuwarsa amma daga bisani mai magana da yawunsa Mista Lee Njiru ya musanta.

  15. An nemi 'yan sanda su kama shugaban APC Adams Oshiomhole

    Gwamnatin jihar Edo da ke kudancin Najeriya ta bukaci rundunar 'yan sandan kasar ta kama shugaban jam'iyyar APC mai mulkin kasar, AdamsOshiomhole.

    Mr Oshiomhole tsohon gwamnan jihar ne kuma uban gidan gwamna mai ci Godwin Obaseki kafin rikicin siyasar da ya barke tsakanisu ya raba su.

    Gidan talbijin na Channels ya ambato mataimakin gwamna jihar, Mr Philip Shuaibu, yana shaida wa manema labarai a Abuja cewa sun nemi babban Sufeton 'yan sanda da shugaban hukumar tsaro ta farin kaya su kama Mr Oshiomhole bisa zargin yin taron siyasa ba bisa ka'ida ba a jihar duk kuwa da cewa kotu ta haramta masa yin haka.

    Ya zuwa yanzu Mr Oshiomhole bai ce komai a kan wannan kira da gwamnatin Edo ta yi ba.

  16. Barkanmu da warhaka

    Muna yi muku barka da wannan lokaci. Kuma muna fatan za ku bibiye mu domin karanta wainar da ake toyawa a Najeriya da Nijar da mawabtansu, har ma da wasu kasashen duniya. Kada ku manta za ku iya karanta labarai a shafukanmu na sada zumunta da muhawara.

  17. Ban kwana

    Jama'a mun kawo karshen rahotonnin kai-tsaye, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu.

    Ku duba kasa domin karanta labaran ranar Litinin.

  18. Wani dalibi dan kasar Kamaru ya kamu da cutar coronavirus

    Wani matashi dan kasar Kamaru, mai shekara 21, da ke karatu a China ya zama dan Afirka na farko da ya kamu da cutar numfashi ta coronavirus.

    Wata sanarwa da jami'ar Yangtze ta fitar ta ce yanzu haka ana kula da dalibin a wani asibiti da ke birnin Jingzhou bayan da ya kamu da cutar lokacin da ya kai ziyara birnin Wuhan, inda aka soma samun bullar cutar.

    Ya koma Jingzhou, inda a can yake zaune, ranar 19 ga watan Janairu, gabanin hana shiga da fita daga birnin na Wuhan da hukumomi suka yi domin hana yaduwar cutar, wacce ta kashe fiye da mutum 200.

    Wakilin BBC Killian Ngala da ke Yaoundé, babban birnin Kamaru, ya ce kamuwar da dalibin ya yi da coronavirus ta jefa fargaba tsakanin dalibai 300 'yan kasar Kamaru da aka killace a Wuhan ba tare da samun isasshen ruwan sha da abinci da kuma takunkumin da ake saynawa a fuska ba.

  19. Buhari ya gana da shugabannin majalisun tarayyar Najeriya

    Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya gana da Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan da kuma Kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila a wani taro na musamman a fadar gwamnatin Najeriya.

    BBC ba ta samu karin bayani ba kan abin da suka tattauna a taron, amma a makon da ya gabata shugabannin sun yi kira ga Buhari da ya dauki mataki kan tabarbarewar tsaro a Najeriya.

    Sanotoci 105 sun dauki nauyin gabatar da wani kudiri a zauren Majalisar Dattawa game da matsalar tsaron, inda suka yi wa gwamnatin Buhari rubdugu kan cewa lallai a dauki matakin kare rayuka da dukiyoyin al'umma.

  20. Ba za mu kara farashin tikitin jirgin kasa ba – Amaechi

    Ministan Sufuri na Najeriya Rotimi Amaechi ya ce gwamnati ba za ta kara farashin tikitin jirgin kasa ba na Kaduna zuwa Abuja domin a bai wa talakawa dama.

    Ministan wanda ya bayyana a shirin Sunrise Daily na Channels TV ranar Litinin, ya ce yana sane da irin kiraye-kirayen da ake yi na kara farashin domin ma'aikatarsa ta samu kudin biyan bashin da ta ciyo na aiyukan da ta yi da kuma yin tattalin jirgin.

    Sai dai Amaechi ya ce akasari jiragen kasa ba su fiya samun riba ba (daga farashin tikiti) a fadin duniya saboda ana samar da su ne domin samun sauki.

    Channels ta rawaito shi yana cewa: "Idan muka kara farashin tikitin ya za mu yi da talakawa masu son zuwa Kaduna daga Abuja? Ya batun talakan da ke aiki a Abuja kuma yake zaune a Kaduna domin ya saukaka wa kansa rayuwa?

    Saboda haka, a duniya baki daya ana saukaka farashin jirgi saboda talaka ya samu hanyar zirga-zirga cikin sauki. Ana samar da shi ne domin ya habbaka tattalin arzikin kasa.

    "Tattalin arzikin kasar zai cike gurbin. Duba yawan harkokin da kake kokarin ginawa ta wannan hanya, yawan kamfanonin da ka kirkira, sai kuma ka duba yawan harajin da suke biyanka."