Mutum 81,000 na dauke da kanjamau a jihar Delta - Amurka
Gwamnatin Amurka ta ce akwai mutum kimanin 81,000 masu dauke da cutar kanjamau a jihar Delta da ke kudancin Najeriya.
Akwai dai mutum milyan 1.9 da ke dauke da cutar a Najeriya.
Amurkar ta nuna rashin jin dadinta kan irin kudin da masu asibitoci a jihar ke karba daga hannu masu dauke da cutar.
Mataimakin jakadan ofishin jakadancin na AMurka a Najeriya, Kathleen FitzGibbon, ya bayyana damuwarsa ne ranar Alhamis lokacin da ya jagoranci wata tawaga yayin wata ziyara ga gwamnan jihar, ta Delta, Ifeanyi Okowa, bayan da jihar ta kaddamar da maganin cutar kanjamu da Amurka ta bayar da tallafinsa.