Mutum 65 Gobara ta kashe a Kaduna a 2019
Hukumar kashe gobara ta jihar Kaduna ta bayyana cewa an samu afkuwar gobara sau 523 sannan kuma mutum 65 ne suka mutu a jihar a tsakanin watan Janairun 2019 zuwa Disamba.
Babban daraktan hukumar Mista Paul Aboi ne ya bayyana hakan ranar Laraba a wata hira da kamfanin dillancin labarai na NAN, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Ya ce akasarin gobarar ta faru ne sakamakon rashin kulawa da kyau yayin amfani da kayayyakin lantarki da kuma rashin sanin yadda za a tunkari wayar lantarki da ba a rufe take ba.
Aboi ya kara da cewa an fi samun afkuwar gobarar a watan Dismaba."Akasari gobara ta fi afkuwa daga watan Disamba zuwa Afrilu saboda gari a bushe yake a wannan tsakanin," in ji Aboi.
Sannan ya ce sun ceto mutum 63 da ransu, sai 141 da suka samu raunuka da kuma 65 da suka rasa ransu bayan kiraye-kirayen neman dauki da suke samu.