Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da suka faru a Najeriya da Nijar da duniya

Wannan shafin namu na kawo muku irin wainar da ake toyawa a Najeriya da Niger da Kamaru da Chadi da Ghana da sauran kasashen Afirka da ma fadin duniya.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir and Umar Rayyan

  1. Sadio Mane ya bada hakuri kan rashin zuwansa Senegal

    Dan wasan kwallon kafar nan na Liverpool kuma dan asalin kasar Senegal Sadio Mane ya bada hakuri kan rashin kai ziyara kasarsa ta asali bayan ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka da hukumar CAF ta ba shi.

    Dan kwallon mai shekaru 27 ya karbi kyautar ne a kasar Masar a ranar Talata kuma gaba daya duk an Laraba za tafi Senegal domin nuna murna.

    Tuni aka hada mashi kwarya-kwaryan taro a wani gidan tarihi a Dakar babban birnin Senegal.

    Sai dai kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta bayyana cewa ''an samu tsaiko da ya fi karfinsa da kuma kungiyar '' wanda hakan ya sa bai je Senegal din ba amma zai je a duk lokacin da ya samu wani sarari.

  2. An ceto yara 27 daga gidan marayu na 'bogi' a Kano da Kaduna

    Rundunar 'yan sandan Najeriya ta bayyana cewa ta ceto yara 27 daga jihohin Kano da Kaduna da ke arewacin kasar.

    Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Kano DSP Abdullahi Haruna ya shaida wa BBC cewa sun ceto yara 19 daga wani gidan marayu a jihar Kano wanda ake kira ''Du Merci''.

    Haka zalika ya bayyana cewa tare da taimakon hukumar NAPTIP, an ceto wasu yara takwas daga jihar Kaduna a gidan marayu na Du Merci da ke reshen jihar ta Kaduna.

    'Yan sandan sun tabbatar da cewa gidan marayun na bogi ne.

    A wata sanarwa da mai bai wa gwamnan jihar Kano shawara kan jin dadin yara da walwala da kuma dawainiyar mata Hajiya Fatima Abdullahi Dala ta fitar, ta bayyana cewa gidan marayun ya shafe shekaru 25 yana aiki ba tare da lasisi ba ko kuma sanin gwamnati.

    Ta kuma yi kira ga jama'ar Kano kan cewa su sa ido domin bayar da rahoto kan irin wadannan wurare da ke aiki ba tare da sanin gwamnati ba.

  3. An kashe sojoji uku a jihar Borno

      • Marubuci, Ishaq Khalid
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa, Abuja

    Akalla sojoji uku aka kashe a wata arangama tsakanin sojojin Najeriya da kuma 'yan kungiyar jihadi ta ISWAP a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.

    Sai dai a wani bangaren kuma kungiyar ta ISWAP cewa ta yi sojoji takwas ta kashe.

    'Yan bindigar sun lalata akalla gidaje 750 a garin Monguno, kamar yadda kamfanin dillanacin labarai na Reuters ya ruwaito.

    Wasu daga cikin majiyoyi sun shaida cewa maharan sun yi amfani da mota dauke da bam inda motar ta lalata gidaje.

    Sai dai rundunar sojin kasar wadda a kwanakin nan bata cika magana ba ta ki cewa komai dangane da harin.

    Fiye da shekaru 10 'yan kungiyar Boko Haram ne ke cin karensu babu babbaka a yankin inda sai daga baya aka samu bullar kungiyar ta ISWAP.

  4. Hatsarin jirgin Ukraine: Jirigin 'na kokarin koma wa filin jirgi ya yi hatsari'

    Binciken da Iran ta yi dangane da jirgin Ukraine da ya yi hatsari ya nuna cewa jirgin ya yi hatsari ne a hanyarsa ta komawa filin jirgi.

    Jirgin samfarin Boeing 737-800 ya fadi ne mintuna kadan bayan ya tashi daga filin jirgin Tehran a Iran kuma mutum 176 da ke ciki duk sun mutu.

    Binciken da aka gudanar ya nuna cewa jirgin ya samu tangarda inda ya kama da wuta,

    Jim kadan bayan faduwar jirgin, Iran ta bayyana cewa ba za ta mika akwatin da ke nadar magana a jirgi ba zuwa kamfanin Boeing ko Amurka.

    Akwatin dai yana bayar da damar sauraron batutuwan da aka tattauna a cikin jirgi kafin hatsari kuma a turance ana kiransa ''black box''.

    A karkashin dokar sufurin jirgin sama ta duniya, Iran tana da 'yancin jagorantar binciken, sai dai wadanda suka kera jirgin dole sai sun shiga ciki.

    Hatsarin jirgin na zuwa ne sa'o'i kadan bayan harin da Iran ta kai wa sansanonin soji na Amurka biyu da ke Iraki.

  5. Ra'ayoyi

    Wasu daga cikin ra'ayoyinku da kuka turo a shafinmu na Twitter

  6. 'A shirye mu ke mu yi sulhu da Iran'

    Amurka ta ce "ashirye take domin zama teburin sulhu da kasar Iran amma ba tare da gindaya wasu manyan sharudda ba", sakamakon tankiyar da aka samu tsakanin kasashen guda biyu.

    A wata wasika da Amurka ta aike wa Majalisar Dinkin Duniya, Amurkar ta yi bayani cewa kashe Qasem Soleimani da ta yi kariyar kai ne.

    Wasikar ta kafa hujja da sashe na 51 na dokokin Majalisar Dinkin Duniya da suka nemi "gaggauta kai korafi" ga kwamitin sulhu bayan daukar matakin kare kai.

    Haka zalika, wasikar wadda jakadan Amurka a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, Kelly Craft ya mika ta kara da cewa "dole ne Amurka ta kare ma'aikatanta da muradunta a yankin gabas ta tsakiya.

    Kelly Craft ya ce Amurka "a shirye take ta tattauna da Iranda manufar dakile karuwar rikicin da zai rikita duniya."

    Iran dai ta mayar da martani inda ta harba makamai masu linzami a sansanonin sojin Amurkar da ke Iraki amma ba a samu wadanda suka mutu ba.

    Ta shaida wa Majalisar Dinkin Duniya cewa kariyar kai ne. Mataimakin shugaban Amurka, Mike Pence ya shaida wa gidan talbijin na CBS cewa "bayanan sirri" sun tabbatar musu cewa Iran ta gargadi mayakan da take goyon baya a Iraki da ka da su kai wa dakarun Amurka hari.

    Zauren majalisar wakilai na Amurka ya shirya kada kuri'ar taka wa shugaba Donald Trump burki wajen kai wa Iran hare-hare ba tare da amincewar majalisar dokoki ba.

  7. Farawa

    Masu bibiyarmu barkanku da warhaka. Da fatan kun wayi gari lafiya. A yau Alhamis ma za mu ci gaba da kawo muku irin wainar da ake toyawa a Najeriya da Nijer da Kamaru da Chadi da Ghana da sauran sassan Afirka da ma duniya. Sai ku ci gaba da kasancewa da mu.

  8. Iraki ta yi Allah-wadai da harin da Iran ta kai cikin kasarta

    Ma'aikatar harkokin wajen Iraki ta gayyaci ambasadan kasar Iran a Baghadaza kan harin da Irani din ta kai wa sansanonin sojan Amurka a kasarta.

    A wata sanarwa da ta fitar, ma'aikatar ta ce "muna Allah-wadai da harin da aka kai kan sansanoninn da ke dauke da sojojin Iraki da wasunsu, sannan kuma mun dauke shi a matsayin keta hakkin 'yancin kasarmu".

    "Iraki kasa ce mai 'yanci sannan... tsaron cikin gidanta ta fi martabawa. Ba za mu bari ta zama filin yaki ba," sanarwar ta bayyana.

  9. Abu 7 da Trump ya fada:, "Ya kamata mu yi aiki tare da Iran"

    "Ba a kashe mana ko kaza ba"

    "Babu sojan Amurka ko na Iraki da ya mutu sakamakon harin makamai masu linzami da kasar Iran ta kai kan sansanin sojin Amurka da ke Iraki ranar Talata."

    "Ba lallai sai mun yi amfani da makamai ba"

    "Mu ne muka fi kowa karfin soja a duniya, inda muke da manyan makamai masu gudun walkiya. Sai dai hakan ba ya nufin lallai sai mun yi amfani da su."

    "Ya kamata ya yi mu yi aiki tare Iran"

    "Kungiyar IS makiyar Amurka ce sannan makiyar Iran ce, saboda haka ya kamata a ce mun yi aiki tare wajen murkushe kungiyar."

    "Muna kira a mayar da Iran saniyar ware"

    Donald Trump ya yi kira ga kasashen Turai da su warware duk wata alaka da ke tsakaninsu da kasar Iran.

    Ya ce: "Akwai bukatar mayar da kasar Iran saniyar ware ko ta gyara halinta."

    Trump ya kuma ce 'Iran ce ta hana zaman lafiya a gabas ta tsakiya.

    "Mai kaunar ransa ba zai kai mana hari ba"

    "Duk wanda yake kaunar rayuwarsa ba zai yi wa al'umarmu barazana ba Wadannan takunkuman masu tsauri za su ci gaba da zama a kan Iran har sai ta sauya halayenta.

    "Wajibi ne Iran ta ajiye shirinta na nukiliyya."

    "Soleimani dan ta'adda ne"

    Donald Trump ya ce "Janar Qasem Soleimani dan ta'adda ne wanda ya dade yana kitsa hare-hare kan al'ummar yammacin duniya wanda kuma ya kamata a ce tuntuni ya mutu."

    "Za mu kara wa Iran takunkumi"

    "Yayin da muke ci gaba da duba irin martanin da za mu mayar, Amurka za ta kara yawan takunkumai kan Iran."

  10. Trump ya kammala jawabi

    Shugaba Trump bai kwashe lokaci mai tsawo yana jawabin ba.

  11. 'Ya kamata mu yi aiki tare da Iran'

    Shugaba Donald Trump ya ce kungiyar IS makiyar Amurka ce sannan makiyar Iran ce, saboda haka ya kamata a ce mun yi aiki tare wajen murkushe kungiyar.

  12. 'Ba lallai sai mun yi amfani da makamai ba'

    "Mu ne muka fi kowa karfin soja a duniya, inda muke da manyan makamai masu gudun walkiya. Sai dai hakan ba ya nufin lallai sai mun yi a,mfani da su."

  13. 'Muna kira a mayar da Iran saniyar ware'

    Donald Trump ya yi kira ga kasashen Turai da su warware duk wata alaka da ke tsakaninsu da kasar Iran.

    Ya ce "akwai bukatar mayar da kasar Iran saniyar ware ko ta gyara halinta."

    Trump ya kuma ce 'Iran ce ta hana zaman lafiya a gabas ta tsakiya.

  14. Donald Trump ya ce:

    "Duk wanda yake kaunar rayuwarsa ba zai yi wa al'umarmu barazana ba Wadannan takunkuman masu tsauri za su ci gaba da zama a kan Iran har sai ta sauya halayenta.

    "Wajibi ne Iran ta ajiye shirinta na nukiliyya.

  15. 'Soleimani dan ta'adda ne'

    Donald Trump ya ce "janar Qasem Soleimani dan ta'adda ne wanda ya dade yana kitsa hare-hare kan al'ummar yammacin duniya wanda kuma ya kamata a ce tuntuni ya mutu."

  16. 'Ba a kashe mana ko kaza ba'

    Shugaba Amurka, Donald Trump ya ce babu sojan Amurka ko na Iraki da ya mutu sakamakon harin makamai masu linzami da kasar Iran ta kai kan sansanin sojin Amurka da ke Iraki ranar Talata.

  17. Labarai da dumi-dumi, Kotun Koli ta tabbatar da zaben Gwamna Sani Bello na Neja

    Kotun Koli ta yi watsi da karar da dan takarar PDP Umar Nasko ya shigar gabanta inda ya kalubalanci nasarar da dan takarar APC Abubakar Sani Bello ya yi a zaben gwamna.

    Kotun ta tabbatar da sahihancin zaben da aka yi da kuma gazgata hukuncin da kotun sauraren kararrakin zabe ta yi a baya kan zaben.

  18. Labarai da dumi-dumi, Kotun Koli ta tabbatar da Darius Ishaku a matsayin gwamnan Taraba

    A hukuncin da Kotun Kolin ta yanke, ta tabbatar da sahihancin zaben gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku inda ta tabbatar da shi a matsayin gwamna.

    Haka zalika kotun ta yi watsi da karar da aka shigar kan zaben Okezie Ikpeazu a matsayin gwamnan jihar Abia.

    Kotun ta bayyana cewa ta amince da hukuncin da kotun sauraren kararrakin zaben ta yanke kan zaben Taraba inda ta ce jam'iyyar APC ba ta da dan takara a jihar a lokacin zabe.

  19. Kotun Koli za ta yanke hukunci kan zaben Taraba, Abia da Neja

    Kotun Kolin Najeriya za ta yanke hukunci kan kararraki 14 a yau.

    Akasarin shari'un da za a yanke hukunci kansu na zabe ne.

    Daga cikin jihohin da za a yanke hukunci kansu a yau akwai Abia da Taraba da Niger da Delta.

    Tuni dai kotun ta zauna inda ta fara bayar da hukunci kan karar zaben jihar Abia.

    Wakilinmu Sani Aliyu yana kotun kuma za mu ci gaba da kawo muku bayanai.

  20. Wani ya bayyana cewa shi ‘dan jihadi’ ne a coci

    'Yan sanda a Kenya sun kama wani mutum a garin Mombasa da ya shiga coci ya bayyana cewa shi dan kungiyar nan ne da ke ikirarin jihadi ta al-Shabab.

    Kafafen yada labarai a kasar sun bayyana cewa fasto din cocin ya kira 'yan sanda bayan mutumin ya shaida cewa bai dade da dawowa daga Somaliya ba.

    A ranar Talata, wata kotu a garin na Mombasa ta bayar da umarnin ci gaba da tsare wanda ake zargin sama da kwanaki 10 domin bayar da dama ga 'yan sanda su kammla binciken su.

    Jaridar The Standard ta Kenya ta ruwaito masu shigar da kara suna cewa wanda ake zargin a shirye yake da ya bayar da shaida da za ta kai ga kama wadanda suke da alaka da 'yan kungiyyar ta al-Shabab.

    Sai dai masu shigar da karar sun ki yarda su bayyana sunan wanda ake zargin da kuma faston ko kuma cocin.