Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Najeriya za ta karbi gasar kwallon mata ta Afirka
Hukumar kwallon kafa ta Najeriya, NFF ta sanar da niyyar karbar bakuncin gasar cin kofin nahiyar Afirka ta mata ta 2020.
Shugaban hukumar kwallon kafar Afirka, CAF, Ahmad ya fada a gidan radiyon Faransa FRI cewar Equatorial Guinea ita ma tana son yin zawarci.
CAF na neman kasar da za ta karbi bakuncin gasar kofin nahiyar Afirka ta mata ta 2020, bayan da Congo ta janye daga gudanar da wasannin a bara.
Ahmad ya sanar cewa a taron hukumar kwallon kafar Afirka da za ta yi ranar 15 ga watan Janairu, za ta bayyana kasar da ta zaba don karbar bakuncin wasannin.
Najeriya ta karbi bakuncin gasar kwallon kafar nahiyar Afirka ta kuma lashe kofin a 1998 da 2002 da kuma 2006.
Mahukuntan kwallon Najeriya na ganin lokaci ya yi da ya kamata kasar ta kara karbar bakuncin wasannin da ta tsara za a yi a Lagos da Benin da Asaba da kuma Uyo.
Kawo yanzu ba a tsayar da ranar buga gasar ba a 2020, amma akan yi a tsakiyar shekara a sauran wasannin da aka yi.
Kasashe shida ne suka karbi bakuncin gasar tun lokacin da aka fara ta a 1998, inda Najeriya da Afirka ta Kudu suka karbi bakunci sau uku-uku,.
Sai Equaotorial Guinea da ta karbi wasannin karo biyu, yayin da Kamaru da Namibia da Ghana kowacce ta karbi bakuncin sau daya.
Tawagar kwallon kafar mata ta Najeriya ta lashe kofin nahiyar Afirka karo na tara.