Hukumar kwallon kafa ta Afirka, CAF za ta bayyana gwarzon dan kwallon kafa na nahiyar da babu kamarsa a 2019 ranar Talata.
Cikin guda ukun da za a zabi gwarzon bana sun hada da dan wasan tawagar Algeria da Manchester City, Riyad Mahrez da na Masar da Liverpool, Mohamed Salah da na Senegal da Liverpool, Sadio Mane.
Mane da Salah sun taimaka wa Liverpool ta lashe kofin Zakarun nahiyoyi, kuma Salah na takara karo na uku a jere.
Mahrez shi ne ya ja ragamar Aljeria ta lashe kofin nahiyar Afirka da aka yi a Masar, inda Mane ya taimaka wa Senegal zuwa wasan karshe a 2019.
Haka kuma za a bayyana gwarzuwar 'yar kwallon Afirka da babu kamarta a 2019.
Wadanda ke takara sun hada da Ajara Nchout ta tawagar Kamaru da kungiyar Valerenga da Asisat Oshoala ta Najeriya Barcelona da 'yar wasan tawagar Afirka ta Kudu mai taka leda a Beijing Phoenix, Thembi Kgatlana.
Koci-Koci da daraktan tsare-tsare da kyaftin din mambobin tawagogin kwallon kafar Afirka ne za su yi zaben gwarzayen Afirka na 2019.
Za a bayyana wadanda suka yi fice a Afirka a wani biki da CAF za ta gudanar a otal mai suna Hurghada da ke Masar.