Abubuwan da suka faru a Najeriya da Nijar da makwabta

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma sauran kasashen Afirka.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir and Umar Mikail

  1. Gobara ta lashe kamfani a Ibadan

    An tafka asarar miliyoyin naira a wata masana'anta da ta kama da wuta a birnin Ibadan na jihar Oyo.

    An dai ce wutar ta fara ci ne da daren ranar Lahadi bayan da masu masana'antar da ma'aikata suka rufe suka tafi gida.

    Ba dai a samu asarar rai ko daya ba.

    Wurin da wutar ta tashi na daya daga cikin wuraren da ake da tarin masana'antun yin leda da robobi.

    Ibadan
    Ibadan
    Ibadan
  2. Jami'ar Abuja ta kori farfesa kan lalata

    Jami'ar Abuja wato UniAbuja ta kori wani farffesa wanda tsohon shugaban tsangayar koyon aikin gona bisa zargin lallata da mata dalibai.

    Jaridar Daily Trust ta buga cewa wata majiyarta ta bayyana cewa hukumar zartarwar jami'ar ce ta amince da korar malamin bayan yin nazarin rahoton wani kwamitin mutum takwas da aka kafa domin bincike kan badakalar lalata da dalibai.

    A watan Yuli ne dai wata daliba a jami'ar ta UniAbuja ta yi zargin cewa farfasan ya neme ta da lalata domin ta samu makin jarrabawa.

    An kuma dakatar da farfesan bayan wani tarko da 'yan sanda suka kafa dana masa.

    Jami'ar Abuja

    Asalin hoton, UniAbuja

  3. Rikicin daba ya barke a birnin Legas

    Fadan daba ya kaure a yankin Paco and Ijeshatedo na birnin Legas tsakanin bangarori biyu kan wane bangare ne ke iko da wurin.

    Bayanai sun ce an samu rasa rayuka da lalata gidaje sakamakon rashin jituwar.

    Tuni dai 'yan sanda suka mamaye yankin domin kwantar da tarzoma.

    Rikicin daba a Legas
  4. Majalisa za ta kashe naira bilyan 37 wajen gyaran zaurukanta

    Majalisar dokokin Najeriya ta amince da kashe naira bilyan 37 domin gyaran zaurukan majalisar.

    Majalisar ta kuma kebe naira bilyan daya domin gudanar gyaran fuska ga kundin tsarin mulkin kasar da ake sa ran farawa a farkon shekara mai kamawa.

    Jaridar The Nation ce ta ambato Daraktan yada labarai na majalisar dokokin, Dr. Rawlings Agada lokacin da yake wannan bayani.

    A ranar 8 ga watan Oktoban 2019 ne dai shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kudirin kasafin kudin 2020 na fiye da naira tiriliyan 10 ga majalisar dokokin kasar.

    Sai dai kuma 'yan majalisar sun kara kusan naira bilyan 30 a kan wanda shugaban ya gabatar.

    Buhari

    Asalin hoton, Buhari Sallau

  5. 'Gwara na mutu da na koma APC'

    Tsohon ministan sufurun jiragen sama a Najeriya, Femi Fani Kayode, wanda jigo ne a jam'iyyar adawa ta PDP ya ce gwara ya mutu da ya koma jam'iyyar APC.

    Fani Kayode ya wallafa hakan ne a shafinsa na Twitter ranar Lahadi.

    Ya ce "masu yada cewa na bar jam'iyyar PDP zuwa APC karya ce kuma labarin boge ne. Gwara na mutu da na koma jam'iyyar almajirai.

    Femi Kayode ya kuma bayyana jam'iyya mai mulki ta APC da jam'iyyar 'almajirai' wato 'The Almajiri Peoples Party'.

    Wannan dai na zuwa 'yan kwanaki bayan da wani rahoto ya yi ta yawo a kafafen sada zumunta cewa Femi Kayode ya koma jam'iyyar APC mai mulki.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    Femi Fani Kayode na yawan sukan gwamnatin Buhari

    Asalin hoton, Twitter

  6. An kama buhuhunan tabar wiwi

    Hadin gwiwar hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA da rundunar soji a Najeriya ta kama buhu 725 na tabar wiwi.

    Sun kuma yi nasarar kwato bindigogi takwas kirar gida daga hannun bata garin.

    Hukumomin sun kama buhunan curarren tabar wiwi guda 545 ne aka kama da daya daga cikin maboyar, baya ga wasu buhu 113 da aka kama a wani wuri, da kuma wasu 73

    An kama buhunan tabar wiwin da aka cuccure ne a wasu manyan buhuna, Mai magana da yawun runduna ta hudun sojin Najeriya a Benin, Manjo Ojo Adenegan, ya ce ma'ajiyar tabar winin na wasu maboya uku ne a cikin kungurmin jeji a karamar hukumar Owan ta Yamma a jihar Edo.

    'Yan jarida da 'yan sanda lokacin da 'yan sanda a Kano ranar 13 ga Nuwamba 2015

    Asalin hoton, Getty Images

  7. An sauya sunan yaro daga Buhari zuwa Sulaiman a Katsina

    A karshen mako ne dai aka yi wani gagarumin bikin sauya sunan wani yaro dan shekara hudu da haihuwa, a jihar Katsina, lamarin da yake matukar jan hankalin 'yan Najeriya.

    Mahaifin yaron ya sauya sunan dan nasa mai suna Buhari zuwa Sulaiman saboda a cewarsa mai asalin sunan yana da tausayi ba kawai mutanen da yake jagoranta ba, har ma dabbobin da ke karkashin mulkinsa.

    Bikin na zuwa ne, mako guda bayan wani makamancinsa da aka yi a Kano, wanda wani magidanci ya sauya sunansa daga Muhammmadu Ibrahim zuwa Muhammadu Buhari.

    Shugaba Muhammadu Buhari

    Asalin hoton, Getty Images