Abubuwan da suka faru a Najeriya da Nijar da makwabta

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma sauran kasashen Afirka.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir and Umar Mikail

  1. Salva Kiir da Riek Machar za su sake zama

    Idan anjima ne a yau shugaban Sudan ta Kudu, Salva Kiir da madugun 'yan tawaye, Riek Machar za su sake komawa teburin sulhu a fadar gwamnatin kasar da ke birnin Juba.

    A jiya ne dai shugabannin biyu suka amince da su kafa gwamnatin hadaka a watan Fabrairu, bayan karewar kwanaki 100 da aka deba na cimma zaman lafiya.

    Kasashen duniya dai na ci gaba da matsa wa bangarorin biyu lamba wajen ganin sun zartar da yarjejeniyar zaman lafiyar da suka cimma domin kawo karshen shekaru biyar na yakin basasa.

    A ranar 15 ga watan Disamban 2019 dai Amurka ta kakaba wa manyan jami'an gwamnatin Sudan ta Kudu da take zargi da yi wa shirin zaman lafiya tuggu, takunkumi.

    Sudan ta Kudu

    Asalin hoton, Getty Images

  2. Kotu ta yi kiranye kan tsare Sowore

    Wata kotu a Najeriya ta gayyaci ministan shari'a da shugaban hukumar tsaro ta farin kaya, DSS, su bayyana a gabanta domin bayar da bahasi kan ci gaba da tsare dan jaridar nan mai fafutuka, Omoyele Sowore.

    Kotun dai ta bukaci mutanen biyu, Abubakar Malami da Yusuf Magaji Bichi da su bayyana ranar Litinin 23 ga watan Disamba.

    A makon da ya gabata ne dai aka yi zargin jami'an hukumar DDS da sake kama Sowore a kotun ta hanyar yin artabu.

    Omoyele Sowore
  3. Masu digiri uku sun rasa aikin yi a Kamaru

    'Yan sanda a Kamaru sun lakada wa wasu malaman jami'a uku duka, inda aka kai su asibiti domin duba lafiyarsu.

    Malaman jami'ar dai kimanin mutum 200 na zanga-zanga ne a birnin Yaounde kan kasa samun aikin koyarwa a jami'a bayan kwashe shekaru suna koyarwa a kyauta.

    Wata mai shekara 45 ita ma ta sha guba al'amarin da ya yi sanadiyyar gaggauta kai ta zuwa asibiti.

    Wasu daga cikin masu zanga-zangar tuni suka fara yajin kin cin abinci.

    Ministan ilmin manyan makarantun kasar, Jacques Fame Ndongo ya yi alkawarin yin duba ga korafinsu duk da cewa ya ce an gudanar da daukar ma'aikatan ne ta hanyar da ya dace.

    Cameroon
  4. 'Mulkin dimokradiyya ne ke sa yaki da rashawa tafiyar hawainiya'

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce mulkin dimokradiyya ne ya yi masa tarnaki ga yadda yake fatan yakar rashawa da cin hanci.

    Jaridar Punch ta rawaito shugaba Buharin na fadar hakan ne yayin wani kwarkwaryar bikin murnar zagoyar ranar haihuwarsa da aka yi a fadar gwamnati ranar Talata.

    Muhammadu Buhari ya kwatanta irin yadda ya yaki rashawa da cin hanci a lokacin yana shugaban mulkin soja tsakanin 1983 zuwa 1985 da kuma yadda yake yi a yanzu.

    Buhari dai ya samu nasarar kama da daure manyan mutane cikin har da tsoffin gwamnoni da aka zarga da rashawa da cin hanci a cikin 'yan watanni kalilan.

    To amma yanzu da alama shugaba Buharin ya fahimci yakin da yake yi da rashawar da cin hanci bai kai mizanin da ya yi tsammanin zai yi ba.

    Shugaba Buhari

    Asalin hoton, Buhari Sallau

  5. Farawa

    Masu bibiyarmu barkanku da warhaka. Za mu bude shirin da tambayar ku sunan wannan tsuntsu a Hausa.

    Tsuntsu

    Asalin hoton, Getty Images

  6. Karshe!

    Nan muka kawo karshen labarai da rahotanni da muke kawo muku game da wainar da ake toyawa a Najeriya da Nijar da Ghana da kuma sauran kasashe makwabtansu. Sai kuma gobe. Mun gode.

  7. Jam'iyyar MPN ta tsayar da Ibrahim Yacouba a Nijar

    A

    Asalin hoton, Others

    Bayanan hoto, Dan siyasa Ibrahim Yacouba

    Jam'iyyar adawa ta MPN kishin kasa ta tsaida Ibrahim Yacouba a matsayin wanda zai mata takara a zaben shugaban kasa mai zuwa a jamhuriyar Nijar.

    An gudanar da bikin mika tuta a gaban duban magoya bayan jam'iyyar da suka fito daga sassan kasar daban-daban ranar Litinin.

    Dan siyasar ya yi rantsuwar yin dukkan abin da zai iya don ganin ya kai wannan jam’iyya ga nasara.

    Ya ce "na yi imanin cewa Allah ne ke ba da mulki ga wanda ya so a lokacin da ya so."

  8. Ana zaben kananan hukumomi a Ghana

    A
    A
    A
  9. Buhari ya sanya hannu a kasafin kudin 2020

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kasafin kudin kasar na shekarar 2020.

    Shugaban ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter a ranar Talata.

    A watan Oktoban da ya wuce ne shugaban ya gabatar da daftarin kasafin kudin kasar na fiye da naira tiriliyan 10 a gaban zauren majalisar dokokin kasar.

    Yayin da a farkon wannan watan majalisar dokokin kasar ta amince da shi a farkon watan nan.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  10. Rigakafi ya 'dawo' da Polio a Ghana

    Mutum 11 sun kamu da cutar Shan Inna da ake zargin an dauko ta ne daga allurar rigakafin cutar.

    Ma'aikatar lafiyar Ghana ta ce bullar cutar da aka samu daga watan Yuni zuwa yanzu abin damuwa ne ga gwamnatin kasa da sauran abokan huldansu.

    Tuni bangarorin suka kaddamar da bincike a yankunan da aka samu matsalar.

    Hukumomin kasar na shirin kaddamar da wani zagayen rigakafin cutar a fadin kasar a mako mai zuwa domin dakile yaduwar cutar.

    A shekarar 2008 ne yara takwas suka kamu da cutar Shan Inna.

    Matsalar da aka samu yanzu ta mayar da hannun agogo baya a kokarin kawar da cutar a Ghana.

  11. An kwato dala biliyan 5, Kudaden sun hada da dala biliyan uku da aka sace.

    An kwato dala biliyan biliyan daga barayin gwamnati a Angola.

    Ministan shari'ar kasar Francisco Queiroz ya bayyana cewa kudaden da aka gano na sun hada da dala biliyan uku da aka sace daga asusun inganta tattalin arzikin kasar.

    Ministan ya yi zargin wasu kasashe da yin kafar ungulu ga kokarin da Angola na bin diddkin kudaden da aka yi sama da fadi da su.

    A yanzu haka dai Jose Eduardo dos Santosh wanda da ne ga tsohon shugaban kasar na gaban shari'a kan zargin rashawa a lokacin da yake jagorantar asusun tattalin arzikin kasar. Sai dai ya ya musanta zargin da ake yi masa.

    Shugaban Angola Jawo Laurenco ya sha alwashin kawo karshen cin hanci da rashawa kasar.

    Jose Filomeno dos Santos ya musanta zargin
    Bayanan hoto, Jose Filomeno dos Santos ya musanta zargin
  12. An yi zanga-zangar neman sakin Sowore a Legas

    Wasu mutane sun yi zanga-zangar neman sakin mai kamfanin yada labarai na Sahara Repoters Omoyele Sowore a birnin Legas a ranar Talata.

    A farkon watan nan ne Hukumar tsaro ta farin kaya a Najeriya (DSS) ta sake kama Sowore kwana daya bayan ta sake shi.

    Jami'an DSS sun kama Mista Sowore ne bayan da ya bayyana a gaban kotu a Abuja don ci gaba da sauraren kararsa.

    A
    A
    A
  13. An kama 'yan Iran 12 da kwayoyi

    Hukumomi sun kama wasu 'yan Iran guda 12 da zargin safarar kilogram 1,500 na migayun kwayoyi a gabar Cabo Delgado na kasar Mozambique.

    Rundunar sojin ruwan Mozambique da hukumar binciken manyan laifuka ta kasar na bincikar lamarin.

    'Yan sanda na zargi mutanen da ke cikin jirgin ruwar da sa wa jirgin wuta bayan sun ga jami'an tsaro.

    'Yan sandan sun ce wutar da kona heroin da nauyinsa ya kai tone 1.5 da ke cikin jirgin.

    @

    Asalin hoton, Jami'an tsaron Mozambique

  14. Za a kafa gwamantin hadin gwiwa a Sudan ta Kudu

    Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir ya amince da yarjejeniyar kafa gwamnatin hadin gwiwa da madugun 'yan adawa Riek Machar a kasar.

    Yarjejeniyar 2018 ta kawo karshen yakin basasa a kasar, ta bukaci shugabannin su kafa gwamnatin hadin gwiwa a watan jiya, amma shugabannin suka kara kwana 100 a kan wa'adin.

    Shugabannin biyu sun yi ta ganawa a Juba a tsawon kwana ukun da suka gabata, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.

    A baya shugabannin sun taba kafa gwamantin hadaka a shekarar 2016, amma abin ya wargaje.

    Shugaba Salva Kiir madugun adawa Riek Machar.
    Bayanan hoto, Shugaba Salva Kiir madugun adawa Riek Machar.
  15. Rundunar 'yan sandan Najeriya za ta binciki wasu jami'an SARS

    Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce za ta binciki wasu jami'anta masu yaki da fashi da makami wato (SARS), kamar yadda ta bayyana a shafinta na Twitter.

    Wannan sanarwar ta biyo bayan wani sako da mutum mai suna Ray U. Morphy ya wallafa a shafin sada zumunta.

    Mista Morphy ya ce shi dan Najeriyya ne wanda yake zaune a kasar Netherlands.

    Ya ce ya zo Najeriya ne a makon jiya kuma yana kan hanyarsa ta zuwa gabashin kasar daga Legas.

    "Mutum biyu sun tsayar da ni wadanda suka ce jami'an SARS ne kuma suka karbi Naira 500,000 wanda na tura musu ta asusun ajiyata na banki," inji shi.

    Ya ce ba su tsaya a nan ba "don sai da na cika musu Naira 100,000".

    Rundunar ta ce za ta bayyana sakamakon bincikenta ga jama'a da zarar ta kammala.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  16. Amurka ta soki shugabannin yankin Sahel

    Amurka ta soki gwamnatocin Yammacin Afirka na yankin Sahel da rashin yin abin da ya dace wajen yaki da masu tsatstsauran ra'ayin addinin Musulunci.

    Mataimakiyar Jadakan Amurka a Majalisar Sinkin Duniya Cherith Norman Chalet ce ta bayyana hakan a gaban kwamitin tsaro na majalisar, inda ta ce kasar Mali ba ta yi wani abin a zo a gani ba wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya.

    Ta ce ya kamata shugabannin kasashen Yammacin Afirka su kara hada kansu wuri guda.

    A makon jiya ne dai wani bangare na kungiyar IS ya kai hari a wani sansanin sojoji a yammacin kasar Nijar wanda ya yi ajalin sojoji 71.

  17. An yi zanga-zangar adawa da Adama Barrow a Gambiya

    A

    Asalin hoton, Getty Images

    Duban 'yan kasar Gambiya ne a babban birnin kasar, Banjul sun yi zanga-zangar neman Shugaba Adama Barrow ya cika alkawarin da ya dauka na sauka daga mulkin kasar, idan wa'adinsa na shekara uku a watan gobe ya cika.

    Mista Barrow ya zama shugaban kasar Gambiya ne bayan zama shugaban jam'iyyun da ke adawa da tsohon Shugaba Yahya Jammeh.

    Hadakar jam'iyyun ya amince cewa Barrow ya jagoranci gwamnatin wucin gadi bayan shekara uku kuma daga ne sai ya kira zabe.

    Sai dai a farkon shekara nan ne wasu mambobin hadakar suka amince a tsawaita wa'adinsa zuwa shekara biyar kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

    Sai dai jam'iyyu biyu sun yi watsi da hakan ciki da babbar kasar wato jam'iyyar United Democratic.

    A

    Asalin hoton, Getty Images

  18. Aisha ta taya mijinta murna

    Uwar gidan Shugaban Najeriya Aisha Buhari ta taya mijinta murnar cika shekara 77 a duniya.

    Aisha ta bayyana hakan ne a wani sako da ta bayyana a shafinta na Twitter a ranar Talata.

    A makon jiya ne dai Aisha ta caccaki mai magana da yawun Buhari, Malam Garba Shehu.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  19. Yadda aka yi jana'izar makiyaya 19 da Boko Haram ta kashe

    A jiya Lahadi ne aka gudanar da sallar janaza ga makiyayan 19 da wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne suka harbe, a garin Ngala, na jihar Borno.

    Rahotanni na cewa al'amarin ya faru ne ranar Asabar a wajen kauyen Fuhe da ke kusa da garin Ngala mai kusanci da kasar Kamaru.

    An dai ce Fulani makiyaya ne suka raka 'yan Boko Haram da ke addabar yankunan nasu da hare-hare, amma daga bisani sai Boko Haram din suka yi wa makiyayan kwantan-bauna.

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito wasu shaidu na cewa bangarorin biyu sun kwashe dogon lokaci suna fafatawa, kafin Boko Haram ta kashe makiyayan guda 19.

    Shaidar da AFP ta yi magana da shi ya ce makiyayan ne suka debi gawarwakin 'yan uwansu zuwa ofishin 'yan sanda.

    An dai ce kafin nan sai da makiyayan suka fatattakin 'yan Boko Haram din da suka shiga garin domin satar dabbobinsu da kayan abinci.

    Jana'izar makiyaya 19 a garin Ngala

    Asalin hoton, Getty Images

    Jana'izar makiyaya a garin Ngala

    Asalin hoton, Getty Images

  20. Gwamnatin Edo ta rufe ofisoshin jami'ar Benin saboda kin biyan haraji

    Gwamnatin jihar Edo da ke Kudu maso Kudancin Najeriya ta rufe wasu ofisoshi na jami'ar Benin wato UNIBEN, ciki har da ofis din shugaban jami'ar, saboda zargin kauce wa biyan haraji.

    Kamfanin dillancin labarai na NAN ya ruwaito cewa jami'an hukumar karbar haraji ta jihar ne suka rufe ofisoshin da farar safiyar Litinin.

    Sauran ofisoshin da abin ya shafa sun hada da ofishin kula da harkokin daukar dalibai da na yin rajistar daliban da kuma na hukumar gudanarwar jami'ar (Senate Chamber).

    Wasu ma'aikatan jami'ar da suka bukaci da a boye sunansu sun shaida wa NAN cewa an ciri kudin haraji a albashinsu.

    Sai dai mai magana da yawun jami'ar Dr. Benedicta Ehanire, ya ce ba gaskiya ba ne maganar rufe ofisoshin.

    "Kamar yadda kuke gani, ina tsaka da aiki a cikin ofishina, shugabata ma tana ofishinta tana aiki," in ji Ehanire.

    Jami'an hukumar haraji ta jihar Edo ba su yi wani karin bayani ba lokacin da NAN ya tuntube su game da lamarin.