Abubuwan da suka faru a Najeriya da Nijar da makwabta

Wannan shafin na kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da ma sauran kasashen Afirka.

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir and Umar Mikail

  1. Kamaru za ta bai wa yankunan renon Ingilishi dama

    Majalisar dokokin jamhuriyar Kamaru ta amince da wani kudurin doka da ya bai wa yankunan renon Ingilishi wata daraja ta musamman, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito gidan rediyon kasar na fadi.

    Kudurin wanda majalisar wakilai ta amince da shi ranar Larabar nan, idan ya samu amincewar majalisar dattawa, yankunan renon Ingilishi ka iya tsara wa kansu tsarin ilmin da shari'a da suaka dace da su.

    Taswirar Kamaru
  2. An rantsar da Abdelmajid Tebboune a matsayin shugaban Algeria

    An rantsar da tsohon firai ministan Algeria kuma mamba na jam'iyya mai mulki ta kasar NLF, Abdelmajid Tebboune, a matsayin sabon shugaban kasa.

    Tebboune ne dai ya lashe zaben ranar 12 ga watan Disamba da aka gudanar a kasar da kaso 58 na kuri'ar da aka kada.

    Dubban 'yan kasar ne dai suka hau tituna suna zanga-zangar nuna kin amince wa da sabon shugaban bisa zargin cewa makusanci ne ga tsohon shugaba Abdel'aziz Bouteflika.

    A watan Afrilu ne dai Bouteflika ya yi murabus a dai-dai lokacin da gwamnatinsa ta fuskanci matsin lamba kan kwashe shekaru 20 tana jagorantar kasa.

    Abdelmajid Tebboune

    Asalin hoton, AFP

  3. Shugaba Buhari a Kano

    Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya hallara a wurin taron bikin fara zangon karatun 2019/2020 na kwalejin koyon aikin 'yan sanda da ke Wudil a Kano.

    A jawabin da ya gudanar, Buhari ya ci alwashin ci gaba da yaki da ta'addanci da inganta aikin 'yan sanda tare da amfni da kwalejin ta Police Academy wurin kara habaka kwazo da dabarun aiki.

    Shugaba Buhari
    Shugaba Muhammadu Buhari
  4. Boko Haram ta 'kashe' mutum 14 a Chadi

    Rahotanni daga Chadi na cewa akalla mutum 14 ne suka mutu sakamakon harin kungiyar Boko Haram a kan iyakar Najeriya da Chadin.

    Wadanda suka mutu dai masunta ne da ke gudanar da sana'o'insu a iyakar Najeriyar da Chadin.

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito wasu hukumomi na cewa mutum 13 sun yi batan dabo sannan an jikkata biyar sakamakon harin na Boko Haram kan garin masunta da ke yammacin kasar ta Chadi.

    Idris Deby

    Asalin hoton, AFP

  5. An yi garkuwa da hakimin Birnin Gwari

    Rahotanni na cewa wasu 'yan bindiga da ba tantance su ba sun yi awon gaba da hakimin garin Birnin Gwari a kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwarin.

    An dai ce da misalin karfe 12 na ranar Laraba ne aka yi garkuwa da Alhaji Ibrahim Yahaya a kan hanyarsa ta zuwa wani wuri da aka kebe domin yin sasanci tsakanin al'ummar Birnin na Gwari da masu sata da kisan jama'a a yankin.

    A kwanakin baya an yi wata tattaunawar tsagaita wuta tsakanin ‘yan bindiga da jami’an karamar hukumar Birnin Gwari karkashin jagorancin shugaban karamar hukumar, Alhaji Garba Gambo.

    Sai dai an cimma yarjejeniyar ce ba tare da karbe makaman da ke hannun ‘yan bingidar ba.

    Kuma wasu bangarorin ‘yan bindigar sun bayyana karara cewa ba za su kasance cikin yarjejeniyar ba.

    Bayanai daga mazauna yankin na nuna cewa ‘yan bindigar na shawagi firi-falo da makamansu a cikin kauyuka suna gudanar da harkokinsu ba tare da shakku ko fargaba ba.

    Hakimin Birnin Gwari, Alhaji Ibrahim Yahaya

    Asalin hoton, OTHERS

  6. Mata na gangamin Alla-wadai da kisan sojoji 71 a Nijar

    A jamhuriyar Nijar yau ne mata 'yan siyasa suke yin wani gangami na nuna bakin ciki dangane da abun da ya faru ga sojojin kasar 71, inda suka yi kira ga al'umma da su yi hatara da abun da suke gani a shafukan sada zumunta.

    A makon da ya gabata ne dai 'yan ta'adda' suka kai wa sansanin sojin da ke yankin Tillaberi hari, inda suka kashe sojojin kasar 71.

    A ranar Lahadin nan ne ake sa ran shugaban Faransa, Emmanuel Macron zai kai ziyarar nuna alhini ga 'yan jamhuriyar ta Nijar.

    Taron mata a Nijar
    Taron mata a Nijar
  7. Sarakan jihar Kano biyar sun hallara

    Sarakunan jihar Kano guda biyar sun hallara a filin taron da ake yi na bude fara karatun kwalejin koyon aikin dan sanda na 2019/2020.

    Sai dai ba kamar yadda jama'a suka tsammata ba, dukkanin sarakunan sun halarci taron inda sarakuna hudu na Bichi da Gaya da Karaye da Rano suke zaune a wuri guda, shi kuwa Sarki Sanusi na zaune a gefe daban.

    An dai ce Sarki Sanusi bai gaisa da sarakan hudu ba wadanda ya iske su a wurin.

    Hakan na nufin dukkannin sarakan guda biyar sun kasance iyayen taro ba guda daya ba kamar yadda aka sani a baya.

    Hakazalika, wannan ne karon farko da sarakunan biyar suka taba haduwa a wurin wani taro tun bayan kirkirar masarautun a tsawon kimanin watanni biyar da kirkirar sabbin masarautu.

    Sarkin Bichi
    Sarakunan Bichi, Gaya, Karaye da Rano a wuri guda
    Isar Sarki Snausi filin taro
    Sarki Sanusi a zaune
  8. Buhari zai je Kano

    A yau Alhamis ne ake sa ran shugaba Muhammadu Buhari zai je Kano, inda zai bude bikin fara karatun 'yan sanda na shekarar 2019/2020 na kwalejin koyon aikin 'yan sanda da ke Wudil.

    Wani abu da jama'a ke daukin ganin faruwarsa a yayin bikin shi ne Sarkin da zai zama uban taro tsakanin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi da na Bichi, Aminu Ado Bayero.

    Bisa al'ada dai Sarkin Kano ne ke zama uban taro a irin wadannan taruka da ake gudanarwa a jihar a lokacin Sarkin guda daya ne.

    Sai dai a yanzu haka kasancewar sarakan sun zama biyar, abin jira a gani shi ne wanne ne daga ciki zai zama uban wannan taro.

    An shafe watanni dai ana sabata-juyata tsakanin bangaren gwamna Ganduje da na masarautar Kano, a gaban kuliya kan sahihanci ko akasin kirkirar sabbin masarautu guda hudu da gwamnati ta yi.

    Shugaba Buhari

    Asalin hoton, Getty Images

    Ganduje da Sarki Sanusi

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamna Ganduje da Sarkin Bichi, Aminu Ado
  9. Farawa

    Masu bibiyarmu barkanku da warhaka a cikin shirinmu na kawo muku bayanai kai tsaye a shafinmu na bbchausa.com. Da fatan za ku kasance da mu a yau Alhamis domin jin wainar da ake toyawa. Mun gode.

  10. Ban kwana

    Nan muka kawo karshen rahotannin kai-tsaye game da abubuwan da suka faru a Najeriya da makwabtanta zuwa yanzu da muke rufewa.

    Za ku iya ci gaba da karanta sauran labarai a shafin farko, amma yanzu ku duba kasa don karanta rahotannin yau.

  11. Senata Ben Uwajumogu ya mutu

    Dan majalisar dattawan Najeriya, sanata Ben Uwajumogu ya rasu.

    Uwajumogu ya rasu ne yau Laraba bayan rashin lafiya a Abuja.

    Dan majalisar mai wakiltar Imo ta Arewa ya rasu yana da shekara 51.

  12. Kotun koli ta tabbatar da zaben Kaduna, Nasarawa, Oyo

    Nasir El-Rufai

    Asalin hoton, Getty Images

    A Najeriya kotun koli ta tababtar da zaben Nasir El-Rufai a matsayin gwamnan jihar Kaduna a 2019.

    Kotun ta kuma tabbatar da Abdullahi Sule a matsayin zababben gwamnan jihar Nassarawa.

    Alkalan kotun karkashin jagorancin mai Sharia Mary Peter-Odili ta ya watsi da daukaka karar da David Ombugadu na jam'iyyar PDP ya yi na kalubalantar zaben gwamna Sule.

    Alkalan sun ce mai daukaka karar da jam'iyyarsa ta PDP ba su da kwararan hujjoji.

    Kotun ta kuma tabbatar da nasarar Seyi Makinde a zaben gwamnan jihar Oyo.

    Kotun kolin ya yi watsi da hukuncin kotun daukaka karar da ta soke hukuncin da kotun sauraren karar zaben gwamnan jihar wadda ta yi watsi da karar da jam'iyyar APC da dan takararta Adebayo Adelabu.

    APC da Adelabu na kalubalantar nasarar Makinde a zaben.

    Kotun daukaka karar ta ce kotun sauraren kararrakin zaben ta yi kuskure wajen yin watsi da korafin jam'iyyar APC, amma ta ki tsige Makinde a matsayin gwamnan Oyo.

    Amma kotun koli ta soke hukuncin a yau Laraba.

  13. Najeriya na son a dawo mata da 'yan kasarta

    Gwamnatin Najeriya ta shaida wa BBC cewa, ta na shirin shigar da korafinta ga kungiyar tarayyar turai matukar ba a dawo mata da wasu dalibai biyu 'yan kasarta da yanzu haka suke a Bosnia ba.

    Gwamnatin ta ce tana dakon a dawo mata da 'yan kasar ta ta a cikin wannan makon ko kuma ta dauki matakin. An dai kai daliban ne bisa kuskure zuwa Bosnia da ga Croatia, inda suka halarci gasar wasan kwallon tennis da aka shirya.

    Da ta ke yi wa BBC karin bayani, shugabar hukumar da ke kula da 'yan Najeriya da ke zaune a kasashen waje, ta ce yakamata ace an dawo da daliban gida Najeriya tun a ranar Jumma'a, amma kuma har yanzu suna Bosnia.

    Ta ce "muna fatan za su dawo gida a cikin wannan makon, dole su dawo, idan kuma har aka ci gaba da rike su to zamu dauki mataki na shigar da korafinmu a kungiyar tarayyar Turai da kuma kungiyoyin kare hakkin dan adam.

    Croatia da Bosnia ba su da ikon rike mana 'yan kasarmu, kai ko da ma ace sun aikata wani laifi ne to a dawo da su gida mana tun da suna da takardun izinin shiga kasar Croatia, kuma a dawo da su gida ma na."

    Abike Dabiri Erewa, ta ce ta tattauna da daliban wato Alexandro Abia da Kenneth Eboh, sun kuma shaida mata cewa suna cikin mummunan yanayi.

    Ta kara da cewa, daya daga cikinsu har suma ya yi a wani sansanin 'yan gudun hijra da ke Bosnia.

    A cewar Mrs Dabiri, ofishin jakadan Najeriya da ke Croatia bai san da kasancewar 'yan Najeriyar a Bosnia da Croatia ba.

    Abike Debiri Erewa

    Asalin hoton, Getty Images

  14. Mutum 6 sun mutu a Jos a wurin hakar ma'adanai

    Ramin hakar ma'adanai

    Asalin hoton, Getty Images

    Akalla mutum shida ne suka rasu bayan da ramin hakar ma'adanai ya rufta a kansu a garin Zawan na karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato ranar Talata.

    Dan Majlaisar Tarrayyar Najeriya mai wakiltar yankin, Gwottson Fom, ne ya tabbatar wa da kamfanin dillancin labarai na NAN ranar Laraba, inda ya ce shekarun wadanda abin ya shafa sun fara ne daga 20 zuwa 27.

    Gwottson ya ce lamarin ya faru ne sakamakon hakar ma'adanan ba bisa ka'ida ba.

    "Mun san cewa wadannan matasan sun mutu ne ta hanyar hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba, amma a bayyane take cewa rashin aikin yi ne ya sa su aikata haka," in ji shi.

    Wakilin NAN da ya ziyarci wurin da abin ya faru ya ce wasu da dama sun ji raunuka.

    Wani mazaunin yankin kuma shugaban kungiyar matasa, Emmanuel Gyang, ya ce abin ya faru ne da tsakar ranar Talata yayin da kusan mutum 50 ke cikin ramin a lokacin da ya rufto.

    Gyang ya kara da cewa wannan ne karon farko da irin wannan hatsarin ya faru a yankin nasu, wanda ya ce "abin tashin hankali ne".

  15. ICPC ta zargi 'yan Majalisar Tarayyar Najeriya da almundahana

    'Yan Majalisar Dattawan Najeriya

    Asalin hoton, @NGRSenate

    Hukumar yaki da almundahana ta ICPC, ta zargi 'yan Majalisar Tarayya da yunkurin yin almundahanar kudi ta hanyar fakewa da ayyukan mazabu wato constituency projects a cikin wani rahoto da ta wallafa.

    Tun a ranar Lahadi ne jaridar Premium Times ta wallafa rahoton mai taken Constituency Projects Tracking Group (CPTG), wanda shugaban hukumar Bolaji Owasanoye ya sanya wa hannu, inda ya zargi 'yan majalisar da yin "amfani da hanyoyi daban-daban na satar kudin al'umma".

    Rohoton ya kara da cewa sun saka wasu ayyuka a kasafin kudi sama da sau daya da sunan aiki iri daya, siffa daya, farashi daya, wuri daya, sannan kuma dan kwangila daya.

    Kazalika, ICPC ta zarge su da kunsa wasu ayyuka a cikin kasafin kudi da suka kira “capacity building and empowerment projects", wanda ya tanadi horar da mutanen mazabarsu da samar masu da kayayyaki har ma da ba su kudi.

    Yayin da suke mayar da martani a zauren majalisar ranar Talata, 'yan majalisar sun bayyana rahoton da cewa wani yunkuri ne kawai na aibatawa tare da muzanta ayyukansu da gangan, kamar yadda jaridar ThisDay ta ruwaito.

  16. 'Matasan da ba su da aiki a Najeriya sun fi milyan 100'

    Ministan kwadago na Najeriya, Chris Ngige ya ce akalla akwia matasa milyan 100 da ba su da aikin yi na a-zo-a-gani.

    Ngige ya bayyana hakan ne a fadar shugaban kasa yayin wani taro kan hijra.

    Chris Ngige ya ce a yanzu haka yawan 'yan Najeriya ya wuce milyan 200 kuma kimanin kaso 60 na matasan kasar na bukatar aikin yi.

    Wannan dai shi ne kusan karon farko da gwamnatin shugaba Buhari ta amince da matsalar rashin aikin yi na matasa a kasar.

    A baya wasu kungiyoyi sun sha bayyana girman matsalar amma gwamnati na mayar da kakkausan martani.

    Chris Ngige

    Asalin hoton, Twitter

  17. An rantsar da 'yar Najeriya a matsayin 'yar Majalisar Birtaniya

    Chinyelu Susan Onwurah

    Asalin hoton, @ChiOnwurah

    An rantsar da 'yar asalin Najeriya kuma 'yar Birtaniya, mai shekara 54, a matsayin 'yar Majalisar Dokokin Birtaniya mai wakiltar mazabar Newcastle ta Tsakiya a ranar Talata.

    Chinyelu Susan Onwurah wadda ita ce 'yar majalisa bakar fata ta farko daga Newcastle, an zabe ta ne tun a 2010 sannan aka sake zaben ta a 2019.

    Onwurah ta wallafa godiyarta ga al'ummar yankin bisa zabenta da suka sake yi a karo na biyu a shafinta na Twitter.

    "An rantsar da ni a yau (Talata) a matsayin 'yar Majalisar Dokoki mai wakiltar Newcastle ta Tsakiya. Ina alfaharin wakiltarku. Ko ma wa kuka zaba ni ce muryarku a Majalisa kuma zan yi bakin kokarina don na taimaka maku."

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

    Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ce shugabar hukumar 'yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa, ta tura wa Onwurah sakon taya murna. Ta ce: "Ina yi maki murna da fatan alheri."

  18. Macron zai je Nijar kan kashe sojoji 71

    Shugaban Faransa, Emmanuel Macron zai kai ziyara birnin Yamai na jamhuriyar Nijar ranar 22 ga watan Disambar nan domin yin ta'aziyya da jajanta wa kasar kan sojoji 71 da aka kashe mata a wani hari kungiyar IS kan sansanin soji da ke yammacin Tillaberi.

    Shafin jaridar Actu Niger na intanet ya ce Macron zai kuma tattauna da shugaban Nijar, Mahamadou Issoufou dangane da abin da ya shafi harkar tsaron yankin.

    A ranar Litinin ne dai kasashen yankin Sahel guda biyar suka amince da kara yawan dakaru a yankin nasu da manufar dakile tasirin kungiyoyin 'yan ta'adda' da ke musu barazana.

    Emmanuel Macron

    Asalin hoton, Getty Images

    Mahamdou Issoufou tare da jama'a yayin sallar janaza ga sojoji 71
  19. 'Yan kaciya sun mutu a Afirka ta Kudu

    Rahotanni daga Afirka ta Kudu na cewa an samu simatsi yayin yi wa yara maza kaciya a kudu maso gabashin kasar, inda da dama suka mutu.

    A kasashen Afirka da dama a kan yi wa yara maza kaciya da lokacin hunturu, inda mafi yawancin lokuta ake tara yaran unguwa ko gari sai wanzamai su sha su.

    Hukumomi da kungiyoyi na yawan kira ga al'umma da su kai yaransu ga asibiti domin shan su ko kuma ga wanzaman da suke da rijista.

    To sai dai kasashen Turai ba ma su yarda da yi wa yara kaciya ba, har sai lokacin da suka girma sai su zabi yin kaciyar ko zama da loba.

    Ana yi wa yara kaciyar gayya a Afirka

    Asalin hoton, Getty Images

  20. Ilhan Omar ta bukaci Amurka ta yafe wa Somaliya bashi

    Amurka ta yafe wa Somaliya dimbin bashin da take bin ta da suka ta samma dala bilyan daya.

    'Yar majalisar wakilan Amurka, Ilhan Omar ce dai ta mika wannan bukata, inda ta ce yafe wa kasar Somaliya bashin zai taimaka wa kasar wurin samun ci gaba.

    Ana dai tsammanin abin da Amurkar ta yi wa Somaliya zai kwarara wa kasashen duniya da kungiyoyi su ma su yafe wa Somaliyar basussukan da suke bin ta domin samun damar sake gina kasar tun bayan yakin basasar da ya illata ta.

    Ilhan Omar

    Asalin hoton, Getty Images