Falana na son a saki Sowore
Batun sake kama dan jaridar nan mai fafutuka a Najeriya, Omoyele Sowore na ci gaba da tayar da kura a kasar, har ma wasu na kira da a gudanar da bincike.
Lauyan mutumin da aka sake kamawa, Femi Falana tuni ya sake nanata bukatar a saki mutumin da ya ke karewar tare da sauran duk mutanen da ake tsare su saboda siyasa a kasar.
Ita dai fadar shugaban kasa ta nesanta shugaba Muhammadu Buhari daga batun sake kama Sowore.



