Hisbah ta saki 'yan daudu 26 bayan yin sallar dare
A ranar Lahadi ne hukumar Hisba ta Kano ta kama 'yan daudu guda 26 a lokacin wani casu a birnin.
To sai dai a ranar Talatar ne kuma hukumar ta saki mutanen bayan sanya su yin sallar dare raka'a 40.
An kama 'yan daudun ne sanye da kayan mata a cewar mataimakin kwamandan hukumar, Tasiu Ishaq.
Daya daga cikin wadanda ake zargin ya ce an kama shi ne a wurin bikin wani abokinsa ne, amma wanda ya gayyace shin ya tsere a lokacin da 'yan Hisbah suka isa wurin.
"Sun yi mana wa'azi kuma tun daga lokacin da suka tsare mu muna yin Sallah. Na yi nadamar abin da ya faru, kuma idan Allah ya yarda ba zan maimaita ba," inji shi.






















