'Karya ne Boko Haram ba su kashe sojojinmu ba'
Rundunar sojin Najeriya ta ce bidiyon da ya rinka yawo a kafafen sada zumunta cewa 'yan Boko Hram sun kashe sojojinmu karya ne.
Mai magana da yawun rundunar, Kanar Sagiru Musa, a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsu na Facebook, ya ce "batun cewa an kashe gomman sojojinsu ranar 10 ga watan Disamba zuki ta-malle ce."
Sagir Musa ya alakanta bidiyon na boge da irin ayyukan kungiyar Biafra ta IPOB, inda ya ce suna yi ne da nufin tunzura al'umma.
Ya kuma kara da cewa wani abu da ke nuna cewa kungiyar IPOB din ce ta kitsa bidiyon shi ne yadda wani mai suna Simon Ekpa wanda na daya daga cikin wadanda suka fito a cikin bidiyon yake kira ga masu bautar kasa 'yan kudu maso gabas da su bar yankin arewa maso gabas da kuma yin kira ga 'yan kabilar Igbo da su shiga aikin soji.

Asalin hoton, AFP

















