An kama buhu 700 na tabar wiwi a Edo, Curarren tabar wiwi guda 545 ne aka kama a wata maboya
Hadin gwiwar hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA da rundunar soji a Najeriya ta kama buhu 725 na tabar wiwi. Sun kuma yi nasarar kwato bindigogi takwas kirar gida daga hannun bata garin.
Hukumomin sun kama buhunan curarren tabar wiwi guda 545 ne aka kama da daya daga cikin maboyar, baya ga wasu buhu 113 da aka kama a wani wuri, da kuma wasu 73
An kama buhunan tabar wiwin da aka cuccure ne a wasu manyan buhuna, Mai magana da yawun runduna ta hudun sojin Najeriya a Benin, Manjo Ojo Adenegan, ya ce ma'ajiyar tabar winin na wasu maboya uku ne a cikin kungurmin jeji a karamar hukumar Owan ta Yamma a jihar Edo.


















