Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da suka faru a Najeriya da makwabtanta

Shafi ne da ke kawo maku abubuwan da suke faruwa a Najeriya da Nijar da Ghana da kuma Kamaru, har ma da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Halima Umar Saleh and Umar Mikail

  1. Kasar Ghana za ta farfado da kamfanin jirgin samanta

    Kasar Ghana ta sanya hannu kan wata yarjejeniya da kamfanin kera jirgin sama na Boeing domin samar mata da jirage samfurin 787-9 Dreamliners guda uku a yunkurinta na farfado da kamfanin jirgin saman kasar mai suna Ghana Airways.

    Sun saka hannun ne kan yarjejeniyar da ta kai har dala miliyan 877 a ranar Talata a birnin Dubai na Daular Larabawa lokacin bikin Dubai Air Show.

    Ministan sufurin jiragen sama Joseph Kofi Adda ya ce:

    "Saboda girman bukatar da ke akwai ta matafiya a Ghana muna ganin cewa 787-9 Dreamliner shi ne jirgin da zai ba mu damar fara jigila a kasashen Afirka kafin daga bisani mu fara zuwa sauran nahiyoyi".

    Ya ci gaba da cewa: "Jirgin 787 yana da juriyar aiki sannan ba ya shan mai da yawa. Muna da kwarin gwiwar cewa mun samu abokan hulda na gari domin kawo sabon jirgi mallakar kasa ."

  2. Mutumin da ya yi damfarar ₦360m daga gidan yari a Najeriya

    Ana binciken wani dan damfara ta intanet, wanda ke tsare a gidan yari, kan wata gagrumar damfara da ya sake yi ta dala miliyan daya, a lokacin da yake tsare a gidan yarin Kirikiri mai cike da tsaro.

    Jami'an hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa sun ce Hope Olusegun Aroke ya yi amfani "gungun abokansa" don yin damfarar.

    An kama shi a shekarar 2012 kuma tun sannan ya fara zaman gidan yari na shekara 24 a gidan yarin Kirkiri mai cike da tsaro.

    Amma wani binciken farko-farko da aka gudanar ya gano cewa yana amfani da intanet.

    A wata sanarwa da hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC ta fitar a ranar Talata, ta ce ta samu wasu bayanan sirrri a kan damfarar da Aroke ya yi kuma suna bincike kan yadda aka yi ya samu damar ci gaba da "mummunar dabi'ar tasa" daga cikin gidan yarin.

  3. Mahama tsohon shugaban Ghana ya roki Najeriya kan rufe iyaka

    Tsohon shugaban kasar Ghana John Mahama ya roki gwamnatin Najeriya da ta bude iyakokinta da ta rufe "domin a ci gaba da harkokin kasuwanci a Yammacin Afirka".

    Jaridar TheCable ta ruwaito kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN yana cewa Mahama ya yi rokon ne a wurin taron lacca mai taken The Realnews Hall of Fame da kuma kaddamar da littafi mai suna ‘Pathways to Political and Economic Development of Africa in Lagos’ wanda aka gudanar a birnin Legas ranar Talata.

    Ya ce rufe iyakar musamman ta bangaren kasar Benin ya shafi ayyukan kasuwanci na manya da kananan 'yan kasuwa a kasashen Togo da Ghana da Ivory Coast, wadanda dukkansu sun dogara ne da ciniki tsakanin kasa da kasa.

    "Na tabbata su ma 'yan kasuwar Najeriya da suka dogara da kayan kasashen waje suna fama," in ji Mahama.

    Ya kara da cewa: "Ina so na yi roko ga Najeriya da ta bude iyakarta ganin cewa akwai yarjejeniya da ta saka hannu tsakaninta da kasashe makwabta saboda a samu ci gaba da harkokin kasuwanci."

  4. Najeriya ta sauya tsarin tafiyar da gidajen yari

    Gwamnatin Nijeriya ta ce ta bullo da wasu jerin sabbin tsare -tsare da za ta yi amfani da su a kokarinta na kawo gyara a gidajen yarin kasar.

    Sabbin tsare-tsaren sun kunshi yunkurin mayar da gidajen yarin kasar a matsayin cibiyoyin gyara halinka, inda daurarru a yanzu za su rika koyon sana’o’in dogaro da kai ta yadda za su kasance masu amfanar al'umma bayan sun kammala wa’adin zaman gidan yarinsu.

    Shi dai ministan shari'ar kasar Abubakar Malami ya bayyana cewa karkashin sabon tsarin, gwamnati za ta sanya na'urori da shigar da tsarin intanet a gidajen domin bibiyar shari'o'i da rayuwar mutanen da ke tsare.

    Auwal Bala wani mai rajin kawo gyara a gidajen yarin Nijeriya ne, saurari yadda yake kallon wannan sabon tsari

  5. Barka, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta a yau

    Masu bibiyarmu barkanku da safiyar Laraba, barka da shigowa shafin kai-tsaye mai kawo rahotanni kan abubuwan da suke faruwa a Najeriya da makwabtanta a yau.

    Umar Mikail ne ke maku fatan kun tashi lafiya.

    Ku yi kasa domin ku karanta labaran Talata.

  6. Kamaru, Gwamnati ta mayar wa Amurka martani kan zargin amfani da jami'an tsaro wajen cin zarafin mutane

    Gwamnatin kamaru ta mayar da martani kan abin da ta kira kage da Amurka ta yi wa jami’an tsaronta.

    Amurkar dai ta zargi gwamnatin Kamaru da amfani da jami'an tsaro wajen haddasa kisan rayukan jama’a babu gairi babu dalili, a yankin renon Ingila mai fama da rikicin 'yan aware.

    Haka kuma, Amurka ta ce jami’an tsaron Kamaru na take hakkokin dan Adam ta hanyar gallaza masu da cin zarafinsu.

    Hakan ya sa Amurka yanke shawarar cewa ranar 1 ga watan Janairun badi za ta janye kasar Kamaru daga jerin kasashen da suke cin moriyar shirin bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka (AGOA).

    Kakakin gwamnatin Kamaru ya ce kasar ba za ta ci gaba da cin moriyar wannan damar kamar da ba.

  7. Ko yarjejeniyar zaman lafiyar Zamfara na aiki?

    Mutane da dama na nuna fargabar cewa yarjejeniyar sulhu da gwamnatin jihar ta kulla da 'yan bindiga domin su ajiye makamansu na neman wargajewa a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya.

    Hakan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da zaman makoki da jimami a jihar, bayan mummunan harin da 'yan bindiga suka kai kauyen Karaye da ke karamar hukumar Gumi kuma suka kashe mutane a kalla 18.

    Hukumomi dai sun bayyana cewa ga alama harin na ramuwar gayya ne bayan da 'yan sintiri da ake kira 'yan sa-kai suka kashe 'yan bindiga kimanin 10 a farkon wannan wata.

    Is'haq Khalid ya tambayi mai bai wa gwamnan jihar ta Zamfara shawara kan lamuran tsaro ko shin ina makomar yarjejeniyar sulhun ganin yadda aka samun hare-haren a baya-bayan nan?

    Ku latsa lasifikar da ke kasa don sauraron hirar:

  8. Ayyukan 'yan majalisa a mazabunsu ba su yi tasiri ba - Buhari

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce bai ga amfanin ayyukan da ‘yan majalisa ke yi a mazabunsu da aka kashe sama da naira tiriliyan daya cikin shekaru 10 ba.

    Ya ce mazauna karkara da aka ji ta bakinsu sun ce ba su ga aikin da aka yi musu ba.

    Shugaba Buhari ya yi kalaman ne a wajen bude taron koli kan yaki da cin hanci da rashawa da ke gudana a Abuja babban birnin kasar.

    Ofishin sakataren gwamnatin tarayya Mr Bos Mustapha ne ya shirya taron, da hadin gwiwar kungiyoyin da ke yaki da rashawa da dangoginsu.

    t��}!�C

  9. Kashi 90 na gidajen Tanzania ba su da wajen bahaya

    Wani rahoto da aka fitar a ranar ban daki ta duniya, ya gano sama da kashi 90 na gidajen babban birnin kasar Tanzania ba su da matattarar bahaya.

    Rahoton ya ce kusan gidaje miliyan hudu a birnin Dar es Salaam sun dogara ga masu kwshe bahaya ba bisa ka'ida ba su kwashe na gidajensu.

    l; t�� ��C

  10. Ghana, Ana nema jagoran 'yan awaren Ghana ruwa a jallo

    'Yan sanda a Ghana sun fara neman jagoran 'yan aware ruwa a jallo, wanda ya ayyana wa yammacin Togoland 'yanci ranar Asabar.

    'Yan sanda na neman Charles Komi Kudzordzi mai sama da shekara 80, wanda ya jagoranci Cibiyar Homeland Study Group don ayyana 'Yammacin Togoland' [Yankunan Volta, wasu sassan Arewa da Arewa maso Gabashi da Yankin Upper East] a matsayin mai 'yancin kai.

    Rahotanni sun nuna cewa an tsere da shi a wata mota da ke jiransa yana gama ayyana 'yancin kai, inda mutanen da suka taru a tsohon bankin Unity Rural suka rika ihu da tafi.

  11. An cinna wa wata shugabar mata ta jam'iyyar PDP a Kogi wuta

    Rahotanni sun nuna cewa wasu da ake zargin 'yan dabar siyasa ne sun cinna wa wata shahararriyar 'yar siyasa a Kogi wuta ranar Litinin.

    Wasu jaridun Najeriya sun ruwaito cewa kakakin rundunar 'yan sanda na jihar Kogi, William Aya ya bayyana cewa, Salome Abuh mai shekaru 60 wadda ita ce shugabar mata ta jam'iyyar PDP a mazabar Ochadamu a karamar hukumar Ofu, na barci a gidanta lokacin da 'yan dabar suka cinna wa gidan wuta daf da magariba.

    Wannan dai na kara nuna cewa ba a shawo kan rikicin da aka yi a lokacin zaben jihar ta Kogi ba.

  12. Sojojin Najeriya sun tsallake kwanton baunar mayakan Boko Haram

    Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun tsallake wani kwanton bauna da mayakan Boko Haram suka yi musu a karamar hukumar Dikwa da ke jihar Borno a raewa maso gabashin kasar.

    Rundunar ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar mai sa hannun Kanal Aminu Iliyasu a Abuja.

    Kanal Iliyasu ya ce abin ya faru ne a ranar Litinin yayin da dakarun bataliya ta 153 da aka kai garin Sabon Marte suke kokarin fatattakar sauran mayakan kungiyar da ke Dikwa.

    A cewarsa, dakarun sun tsallake kwanton baunar ne a hanyar da suke sintiri ta kauyen Aka mai nisan kilomita bakwai daga garin Marte,

  13. Angela Merkel za ta gana da shugabannin Afirka kan taron kasuwanci

    Shugabannin kasashen Afirka 21 za su gana da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a birnin Berlin a yau Talata, domin tattaunawa kan habaka kasuwanci da zuba jari a Afirka.

    Za su halarci taron wani sabon shiri da gwamnatin Jamus ta kirkiro ne mai taken ''Compact for Africa Conference,'' da aka samar a shekarar 2017 don habaka zuba jari a Afirka.

    An kirkiro da shirin ne don samar da ayyukan yi da inganta rayuwa da kuma rage yawan masu neman mafaka da ke zuwa Turai.

    Tun lokacin da Jamus ta fuskanci tururuwar 'yan gudun hijira, gwamnatin kasar ta kaddamar da shirye-shirye masu yawa don taimaka wa tattalin arzikin kasashen Afirka, amma 'yan kasuwar Jamus ba sa mayar da martani sosai.

  14. Gobara ta hallaka miji da matarsa mai ciki da 'ya'yansu a Binuwai

    Jaridar Punch ta ruwaito cewa Mukaddashin Babban sakataren ma'aikatar kimiyya da fasaha ta jihar Kogi, Sekegh Akaa ya kone tare da matarsa mai dauke da juna biyu da 'ya'yansu biyu a wata gobara da ta mamaye rukunin gidaje na Kwararafa a Makurdi a daren ranar Litinin.

    Wani wanda ya shaida lamarin ya ce wutar ta fara ci ne da misalin karfe biyu na dare.

    Wata makwabciyar Mista Sekegh ta shaida wa wakilin jaridar Punch cewa ba a san abin da ya haddasa gobarar ba amma ana tunanin matsalar wutar lantarki ce ta haddasa ta.

    Wutar ta ci gaba daya gidan sannan ta shiga wasu gidaje uku, ciki har da gidan Babban Mai Taimaka wa Gwamna na musamman kan addini, Daniel Unongo.

    Jaridar Punch ta ruwaito cewa duk dai 'yan kwana-kwana sun yi aiki tukuru wajen don kashe wutar da kuma ceto rayukan mutane, gobarar ta dade tana ci.

  15. Najeriya za ta fara ba da biza ta intanet

    Hukumomi a Najeriya sun ce suna kokarin bullo da wani shirin bayar da biza ta intanet ga baki 'yan kasashen waje masu sha'awar zuwa kasar don yawon bude ido.

    Hukumar shige da ficen kasar dai ta ce zuwa karshen wannan shekara za ta fara bayar da irin wannan biza ta intanet.

    Matakin wani yunkuri ne da hukumomin kasar ke yi don mayar da Najeriya, zuwa wata kasa da masu sha'awar zuwa yawon bude idanu ke hankoron zuwa.

  16. 'Yan bindiga sun kashe sojojin Mali 24

    Rundunar sojin Mali tace an kashe jami'anta 24, sannan wasu kusan 30 sun jikkata a wani hari da 'yan bindiga suka kai kan iyakar kasar da ke arewa maso gabashin Nijar.

    Wata sanarwa ta ce harin ya faru ne a garin Tabankort da ke yankin Gawo.

    Sanarwar ta kara da cewa 'yan bindiga 17 ne suka mutu a harin.

    Amma sanarwar ba ta bayyana ko su wanene suka kai harin ba.

    Sai dai kuma rundunar sojin kasar ta shafe tsawon lokaci tana yakar masu tayar da kayar bayan da ke da alaka da kungiyar Al Qaeda da ISIS.

  17. Buhari ya ce PDP na iya zuwa kotu kan zaben Bayelsa da Kogi

    Shugaba Muhammad Buhari ya bai wa babbar jam'iyyar hamayya ta PDP da sauran jam'iyyu shawarar zuwa kotu idan ba su gamsu da sakamakon zaben jihohin Kogi da Bayelsa ba.

    Shugaban ya bayyana haka ne bayan da Hukumar Zabe mai Zaman Kanta, INEC ta sanar da gwamnan jihar Kogi kuma dan takarar jam'iyyar APC, Yahaya Bello da kuma David Lyon na Bayelsa a matsayin wadanda suka yi nasarar cin zaben gwamnonin jihohin da aka yi ranar Asabar.

    A wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kan yada labarai, Femi Adesina ya fitar, Buhari ya taya Yahaya Bello da David Lyon murnar cin zaben na ranar Asabar.

  18. Labarai kai tsaye

    Masu bin mu a wannan shafi assalamu alaikum.

    Halima Umar Saleh da Fauziyya Kabir Tukur ke muku maraba.

    Ku biyo mu don samu labarai da dumi-duminsu da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Ghana da Kamaru a yau Talata.