Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da suka faru a Najeriya da makwabtanta

Shafi ne da ke kawo maku abubuwan da suke faruwa a Najeriya da Nijar da Ghana da kuma Kamaru, har ma da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Halima Umar Saleh and Umar Mikail

  1. Wayewar kai irin ta Turawa na lalata al'adun Afirka na girmama manya - Buhari

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce abin takaici ne yadda wayewar kai irin ta Turawa ke lalata al'adun Afirka na girmama manya, da kuma yadda abin ke kara ta'azzara.

    Shugaban ya fadi haka ne a yayin da yake gabatar da jawabi a taron kungiyar Kasashen Afirka Ta yamma ECOWAS, a ranar Litinin.

    Ana taro ne don yin muhawarar kan batun inganta rayuwar tsofaffi a kasashen Afirka.

    Ministan Ayyuka na Musamman George Akume ne ya wakilci Shugaba Buhari a wajen taron, wanda ake yi na yini biyu a Abuja, babban birnin Najeriya.

    ''Saboda ci gaba da wayewa irin ta Turawa, al'adunmu da suke koya mana girmama manyanmu a yanzu suna gurbacewa.

    ''Hakki ne a kanmu mu dawo da martabar manyanmu don ba zai yiwu mu zauna muna kallon wasu suna yin abin da mu ya kamata a ce mun yi ba,'' '' a cewarsa.

    Mahalarta taron dai sun fito ne daga kungiyoyi daban-daban masu ruwa da tsaki ta bangaren kare hakkin dan'adam ta fuskar inganta rayuwar tsoffi a nahiyar Afirka.

  2. Sojojin Faransa sun mutu a hatsarin helikwafta a Mali

    Sojojin Faransa 13 ne uka mutu sakamakon wani hatsarin jirgi mai saukar ungulu a arewacin Mali.

    Hatsarin ya auku ne yayin da suke kai wani hari kan masu da'awar kishin Islama, a cewar wata sanarwa daga ofishin shugaban kasar Faransa.

    Helikwafta biyu ne suka yi taho-mu-gama a lokacin kai harin a ranar Litinin da yamma, kamar yadda sanarwar ta kara fada.

  3. Babbar jam'iyyar adawar Kamaru ba za ta shiga zaben 'yan majalisu da kananan hukumomi ba

    Babbar jam'iyyar adawa a Kamaru ta ce ba za ta shiga zaben 'yan majalisu da na kananan hukumomi ba.

    Jam'iyyar MRC ta ce ba za ta shiga tagwayen zabukan na ranar 9 ga watan Febrairun badi ba saboda a cewarta, hukumomin kasar sun gaza shawo kan rikicin yankin renon ingila.

    Da yammacin ranar Litinin ne wa'adin da Hukumar Zaben Kamaru ta sanya na rufe karbar takardun ‘yan takara ya cika.

  4. Gwamnatin Jamus ta bai wa Nijar tallafin kudi don raya birane

    Gwamnatin Jamus ta bayar da tallafin wasu makudan kudade don gudanar da ayyukan raya birane a Jamhuriyar Nijar.

    Kungiyar FICOD ta kasar Jamus kan yi amfani da irin wadannan kudade wajen gina asibitoci da makarantu, da kasuwanni da sauransu, da nufin kawar da hankulan 'yan kasashen Afirka daga tunanin barin gidajensu zuwa ci-rani kasashen Turai.

    Ga rahoton wakiliyarmu Tchima Illa Issoufou bayan ta ziyarci daya daga cikin asibitocin da kungiyar FICOD ta gina a jihar Tillabery.

  5. An kaddamar da rijistar fallasa masu fyade a Najeriya

    Gwamnatin Najeriya ta kaddamar da wata rijista da ta ce za ta yi amfani da ita wurin fallasa masu cin zarafin kananan yaran.

    Hakan wani yunkuri ne na kare 'yancin yaran.

    Wannan ne karon farko da kasar ta samar da irin wannan rijista da ta ce ta yi ne don fallasa asiri da ma kunyata masu irin wannan dabi'a.

    Ministar Mata ta Najeriya Pauline Tallen, ta ce zuwa yanzu an bude rijistar a jihohi bakwai, kuma Shugaba Muhammadu Buhari ya dauki lamarin da muhimmanci sosai.

    Ministar ta ce shugaban kasar ya sha alwashin hukunta duk wanda aka kama da laifin fyade, da kuma hukunta wadanda aka yi a kusa da inda suke ma.

    Shugabar hukumar yaki da fataucin al'umma ta Najeriya Donli Julie Okah, ta bayyana yadda rijistar za ta yi aiki.

    Ta ce ''rijistar masu fyaden na dauke ne da bayanan mutane masu aikata wannan laifi kamar sunayensu da hotunan da shekarunsu da garin da suke da kuma duk wasu bayanai da suka shafe su.''

  6. Labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabta a yau 26/11/2019

    Masu bin mu a wannan shafi Assalamu alaikum, barkanmu da safiya.

    Ku kasance da mu kamar kullum a wannan shafi don karanta abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Ghana da sauran makwabtan kasashe.

  7. Aisha Buhari ta ce za ta jagoranci yaki da cin zarafin mata

    Uwargidan Shugaban Najeriya, Aisha Muhammadu Buhari za ta jagoranci sauran matan gwamnoni wajen yaki da cin zarafin mata da kananan yara a arewacin Najeriya.

    A wasu sakonni da ta wallafa a shafinta na Twitter, Aisha Buhari ta bayyana cewa yau ce ranar farko a kwanaki 16 na yaki da cin zarafin mata a duniya.

    A jerin sakonnin nata, Uwargidan Shugaban ta yi kira ga maza da mata da kananan yara da su yaki duk wani nau'i na cin zarafi.

    Haka kuma, Aisha Buhari ta wallafa wani bidiyo a Twiiter wanda ke nuna matan gwamnonin arewacin Najeriya suna bayar da bayanai kan cin zarafin mata da kuma zaburar da mutane kan su guji cin zarafin mata.

  8. 'Ya kamata duniya ta kara kaimi kan tsaro a yankin sahel'

    Shugaban Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 74, Tijjani Muhammad Bande, ya ce akwai bukatar duniya ta kara mayar da hankali kan lamarin tsaro a yankin Sahel na Afirka saboda munanan rikice-rikicen Boko Haram da sauran kungiyoyin da ke da alaka da kungiyar IS da al-Qaeda.

    A baya-bayan nan, 'yan bindiga sun kaddamar da hare-hare a kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar da Najeriya inda suke kai wa sojoji hari.

    Tijjani Bande ya ce duk da kokarin da kasashen ke yi don dakusjhe wadannan kungiyoyi, har yanzu lamarin tsaro na kara tabarbarewa.

    .

  9. An gurfanar da Mompha a gaban kotu

    Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta'annadi EFCC, ta gurfanar da Isma'ila Mustapha wanda aka fi sani da Mompha a babbar kotu a safiyar yau, bisa zargin almundahanar naira biliyan 33.

    A watan Oktoba ne EFCC ta kama Mompha, wani fitacce a shafukan sada zumunta, a Abuja a hanyarsa ta zuwa Dubai bisa zargin aikata wasu manyan laifuka.

    EFCC ta ce Isma'ila na yaudarar mutane ya ce shi dan canji ne, ya sace masu kudi.

    Mompha kan sa hotunansa a shafukan sada zumunta cikin manyan motoci na alfarma da dimbin kudaden kasashen waje.

  10. Kamaru, Ana zaben fitar da gwani karkashin tsauraran matakan tsaro

    A yau ne Hukumar Zabe take rufe karbar takardun ‘yan takara da za su shiga tagwayen zabukan ranar 9 ga watan Fabrairu..

    ‘Yan takara daban-daban da jam’iyyun siyasa ne za su fafata domin neman lashe kujerun ‘yan majalisar dokoki 180 da kansaloli sama da 10,000 a cikin kananan Hukumomi 360.

    Yayin da aka fitar vda ‘yan takara ba tare da wata matsala ba a jerin ‘yan takarar jam’iyyun siyasa na bangaren adawa, a jam’iyyar RDPC mai mulki kuwa, zaben fidda gwanaye ya kasance cikin rudani karkashin sa idon jami'an tsaro.

  11. Ana tattaki don kawo karshe cin zarafin mata a Kano

    Wasu kungiyoyin kare hakkin dan adam a Kano na tatataki a yau, ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware don kawo karshe cin zarafin mata a duniya.

  12. Nijar, An koro 'yan makaranta 24,000 daga makarantu a Damagaran

    A jamhuriyar Nijar, matasan jihar Damagaram sun kafa wani kwamiti da zai yi aiki wajen fito da jihar daga fadawa mugun hali ta dalilin tabarbarewar illimi a jihar.

    A kalla 'yan makaranta 24,000 ne aka koro daga makarantu daban-daban a cikin wannan shekarar a fadin jihar, abin da ke shirin zama barazana ga rayuwar al'uma.

    Haka kuma, baya ga fannin illimi, fannoni irin na koyon lafiya da noma da kiyo ma na fuskantar koma baya a jihar kuma matasan sun sha alwashin kawo masu gudunmuwa.

  13. Ba mu gamsu da ikirarin Buhari ba - PDP

    Jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta ce har yanzu ba ta gamsu ba kan ikirarin shugaban kasar Muhammadu Buhari cewa ba zai yi kuskuren neman wa'adi na uku ba.

    An dauka cewa jawabin shugaba Buhari a karshen makon jiya zai kawo karshen rade-radin da ake yadawa cewa wasu sun fara zuga shugaban a kan ya nemi wa'adin mulki na uku, duk da yake tsarin mulkin kasar bai ba da irin wannan dama ba.

    Sai dai babbar jam'iyyar adawar kasar ta ce ba ta da kwarin gwiwa kan ikirarin shugaba Buhari, saboda ma ya yi irin wannan alkawari sau da dama, amma ya aikata sabanin haka.

    Zahraddeen Lawan ya tuntubi sakataren jam'iyyar PDP ta kasa Sanata Umar Tsauri, don jin ko me shugaban zai yi ya tabbatar musu da ikirarinsa?

    Ga bayaninsa a kasa.

  14. Barkanmu da war haka

    Masu bin mu a wannan shafi assalamu alaikum. Halima Umar Saleh da Fauziyya Kabir Tukur ke fatan kun wayi gari lafiya.

    Ku kasance da mu a yinin yau don kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da sauran makwabta.

  15. Kotun daukaka kara ta kori karar Abba Gida-Gida

    Kotun daukaka kara da ke zama a Kaduna ta tabbatar wa Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje kujerarsa.

    Kotun ta yi watsi ne da ikirari 24 da Abba Kabir da kuma PDP suka gabatar mata.

    Tun a ranar 8 ga watan Nuwamba ne kotun ta fara sauraron karar, wadda PDP ta daukaka bayan kotun sauraron kararrakin zabe ta yi watsi da ita a shari'ar da mai Shari'a Halima Shamaki ta jagoranta.

    Yayin da yake bayar da bayanai a kotun, Mai Shari'a Tijjani Abubakar ya ce hukuncin da kotun baya ta yanke ya inganta kuma Abdullahi Umar Ganduje ne ya ci zaben.

    Yanzu dama daya ce ta rage wa PDP da kuma Abba kabir, ita ce ta Kotun Koli.

    Hakan yana nufin har yanzu PDP ba ta yi nasara a dukkanin kararrakin da ta shigar ba game zaben gwamna na 2019.

    A yau din ne kuma wata kotun ta tabbatar da Aminu Waziri Tambuwal na PDP din a matsayin gwamnan jihar Sokoto a karar da APC ta shigar gaban Kotun Daukaka Kara.

  16. INEC ta saka ranar sake zaben mazabar Dino Melaye

    Hukumar zaben Najeriya INEC ta tsayar da ranar 30 ga watan Nuwamba domin kammala zaben dan Majalisar Dattawa na Kogi ta Gabas, wato mazabar Dino Melaye, da ke arewa ta tsakiyar kasar.

    A ranar Asabar da ta gabata ne aka yi zaben, wanda hukumar zaben kasar ta ce ba a samu gwani ba, kasancewar adadin kuri`un da aka soke ya zarce tazarar da dan takarar jam`iyyar APC, Smart Adeyemi ya bai wa Sanata Dino Melaye na jam`iyyar PDP.

  17. Kotu tana yanke hukunci kan karar Abba Gida-Gida

    A yau Juma'a ne Kotun Daukaka Kara da ke birnin Kaduna take yanke hukunci kan karar da Abba kabir Yusuf, dan takarar gwmnan jihar Kano a jam'iyyar PDP, ya daukaka yana kalubalantar nasarar Gwamna Abdullahi Umar Ganguje na jam'iyyar APC a zaben watan Fabarairu.

    Tun farko dai Mai shari'a Halima Shamaki ta kotun sauraron kararrakin zabe ta kori karar farko da Abba Gida-Gida ya shigar gabanta a ranar 2 ga watan Oktoba.

    Ku kasance da mu domin sanin yadda za ta kaya a kotun.

  18. An kama Sarkin Mayu na karya a Kano

    Hukumar karbar korafe-korafe ta jihar Kano a arewacin Najeriya, ta kama wani mutum mai da'awar shi Sarkin Mayu ne tare kuma da damfarar mutane kauyen Albasu.

    Shugaban hukumar karbar korafi Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya shaida wa BBC cewar 'Sarkin Mayun' kan bukaci kudi daga hannun wanda ake zargi da kama mara lafiya da maita, a matsayin tara.

    Muhuyi Magaji ya ce binciken da suka gudanar ya nuna musu cewar mutumin na amfani da wata ciyawa da yake amfani da ita wajen.

  19. Kotu ta tabbatar da Tambuwal a matsayin gwamna

    Kotun daukaka kara ta tabbatar da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal a matsayin zababben gwamnan jihar Sokoto.

    Kotun ta yi watsi ne da karar da jam'iyyar APC da dan takararta Ahmad Aliyu suka shigar suna kalubalantar nasarar da Gwamna Aminu Tambuwal na PDP ya samu a zaben gwamna na 2019.

  20. 'Yan gudun hijirar Sudan na zanga-zanga a Nijar

    'Yan gudun hijirar da suka fito daga kasashen Sudan da Afrika ta Tsakiya da Kamaru da Eritrea na zanga-zangar fitar da su daga sansanin 'yan gudun hijira da Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta MDD ta yi wato UNHCR.

    Mutanen sun yi zaman dirshen ne a gaban offishin hukumar tare da 'ya'yansu manya da yara suna kokawa cewa kusan wata biyu kenan suna kwana a titi.

    Hakan ya faru ne bayan hukumar ta danka masu 'yan kudi ta ce su kama gabansu.

    Sun ce suna wannan zama ne domin nuna rashin jin dadinsu game da matakin hukumar na nuna masu halin ko in kula.