Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da suka faru a Najeriya da makwabtanta

Shafi ne da ke kawo maku abubuwan da suke faruwa a Najeriya da Nijar da Ghana da kuma Kamaru, har ma da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Halima Umar Saleh and Umar Mikail

  1. An tsare 'yan Rwanda 200 kan shiga Uganda ba bisa ka'ida ba

    An tsare mutane kusan 200 a yammacin Uganda wadanda galibinsu 'yan kasar Rwanda ne, a wani mataki na hana mutane shigowa kasar ba tare da izini ba.

    Gwamnan lardin arewacin Rwanda ya gargadi mutane su daina tsallakawa zuwa Uganda saboda dalilan tsaro.

    Ana zaman dar-dar tsakanin Uganda da Rwanda duk da yarjejeniyar sulhu da aka cimma tsakanin shugabannin kasashen biyu.

    Mazauna yankunan kan iyaka -- sun yi korafin cewa bambamci siyasa na raba kan iyalan da ke zaune a garuruwan da ke kan iyakar kasashen biyu.

  2. Likitoci na zargin gwamnati da kisan kiyashi a Zimbabwe

    Manyan likitoci a Zimbabwe na zargin gwamnatin kasar da aikata kisan kiyashi cikin ruwan sanyi kan al'ummar kasar.

    A wata wasika da suka fitar, likitocin sun ce hukumomi sun mayar da asibitocin gwamnati tamkar tarkunan mutuwa saboda rashin samar da magunguna da wasu kayayyakin kula da lafiya.

    Manyan likitocin sun kaurace wa asibitoci domin nuna goyon bayansu ga kananan likitoci fiye da 400 da aka dakatar.

  3. Yara dubu 400 ne ba sa zuwa makaranta a Jihar Yobe

    Gwamnnatin Yobe a arewa maso gabashin Najeriya ta ce ta tantance kananan yara sama da dubu dari hudu da ba sa zuwa makaranta sakamakon ayyukan Boko Haram a sassan jihar.

    Saboda wannan dalilin ne, gwamnan jihar Mai-mala-Buni ya ce gwamnatinsa ta ware kaso mafi tsoka ga bangaren ilimin boko da kuma na tsangaya a wani mataki na farfado da jihar Yobe.

  4. An yi garkuwa da basarake a Abuja

    Wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da sarkin Rubochi da ke yankin Kuje a Abuja babban birnin Najeriya.

    Wani mazaunin garin ya tabbatar wa da BBC cewa masu garkuwar sun sace Alhaji Mohammed Ibrahim Pada da tsakar daren ranar Talata.

    Za mu kawo maku karin bayani.

  5. Hukumomin Agadez sun samar da cibiyoyi don saukaka wa al'ummomi samun takardun bukata

    Hukumomin garin Agadez a Jamhuriyar Nijar sun samar da wasu cibiyoyi biyu don saukaka wa al'ummomin unguwanni sama da 40 damar samun takardun da suke bukata.

    Ganin yadda garin na Agadez ya kara girma da yadda al'ummomin birnin ke wahala wajen gano ofishin magajin gari da ya zamo wuri daya tilo da ake samar da takardun haihuwa da takardun filaye da sauran takardu masu mahimanci ga rayuwa, ya sa hukumomin yin kananan ofisoshi da aikinsu shi ne yin wadannan takardu.

    Hakan dai ba karamin dadi ya yi wa mazauna birnin ba, suna masu cewa wahalhalunsu ta wannan fanni sun kare.

  6. Kamaru na shan matsi daga kasashe kan yankin rainon Ingila

    Kamaru na dada shan matsi daga kasashen ketare domin ta samu ta warware rikicin yankin rainon Ingila ta hanyar lumana.

    Bayan kasar Amurka ta bayyana matsayinta a karo da dama game da wannan rikici, a wannan karo kuma wasu kungiyoyi ne suka karbi ragama.

    Hakan ya Shugaban Hukumar kungiyar tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat tare da sakatarorin kungiyoyin kasashen Commonwealth da Francophonie Patricia Scotland da Louise Mushikiwabo suka kawo ziyara Kamaru.

    Suna ziyarar ne domin a samu a dawo da tsaro da zaman lafiya da yankin rainon Ingila ya jima bai gani ba tsawon shekara uku da suka gabata. Saurari rahoton Mohaman Babalala:

  7. 'Yan Najeriya na zanga-zanga kan dokar kalaman kiyayya

    Wasu 'yan Najeriya suna zanga-zangar nuna kin amincewarsu game da kudirin dokar nan ta kalaman kiyayya wato Hate Speech Bill, wanda Sanata Aliyu Abdullahi Sabi ya gabatar a Majalisar Dattawa.

    Tun sanda sanatan ya gabatar da kudirin dokar 'yan Najeriya suka yi Allah-wadai da shi musamman ayar da ta tanadi hukuncin kisa ga duk wanda ya furta kalaman kiyayya kuma ya yi sanadin ran wani to shi ma za a dauki ransa ta hanyar rataya.

    Zanga-zangar tana gudana ne a farfajiyar zauren majalisar a safiyar yau Laraba tare da yin kira ga shugabannin majalisun tarayya da su dakile shirinsu na yin dokar.

    Kazalika, ana yin irinta a jihar Legas, inda masu zanga-zangar suka yi wa majalisar dokokin jihar tsinke. Honorabul Yusuf ne ya wakilci kakakin majalisar yayin tarbar masu koken.

    Tun 12 ga watan Nuwamba ne dokar ta tsallake karatu na farko a zauren majalisar kuma yanzu tana jiran karartu na biyu.

    Sai dai a wani bayani da ya fitar ranar Lahadi, Sanata Alyu Abdullahi ya ce "kudirin zai fuskanci 'yan gyararraki musamman ayar da ta tanadi hukuncin kisa wanda 'yan Najeriya suka fi kokawa a kansa" idan sun tashi sake muhawara a kan dokar.

    Kazalika, Sanatan ya bayyana a wani bidiyo da shafin Majalisar Dattawa ya wallafa a shafukan sada zumunta, inda yake cewa kudirin dokar ya tanadi cewa hukuma ce mai zaman kanta za a kafa da za ta kula da irin wadannan laifiuka.

    Sanatan ya kara da cewa sai wannan hukuma ta duba ta tabbatar da cewa kalaman da mutum ya yi sun kai munzalin kalaman kiyayya (hate speech) sannan su bayar da shawarar dokar ta yi aiki a kansa.

  8. Nijar - Bakin haure

    Masu ruwa da tsaki kan yaki da kwararar bakin haure a Jamhuriyar Nijar sun fara wani zama don yin nazari kan hanyoyin da za a bi wajen kawo karshen tafiya cirani ta barauniyar hanya.

    Taron na yini uku ya kunshi jami'an gwamnati da masu yaki da matsalar ta bakin haure wadanda za su samu kwarewar aiki kan dabarun yaki da safarar bakin haure.

    Ga rahoton Tchima Ila Issoufou daga Nijar:

  9. Yadda 'yan fashi ke ci gaba da tarwatsa kauyuka a jihar Neja

    Hukumar bayar da agajin gaggawa a Najeriya ta ce tana ci gaba da tsugunnar da daruruwan mutanen kauyuka da dama wadanda 'yan fashin daji suka far wa musamman a yankin karamar hukumar Shiroro na jihar Neja.

    Maharan sun auka kan kauyukan inda suka bude wuta da bindigogi tare da cinna wa gidaje wuta, lamarin da ya tilasta wa mutane tserewa zuwa daji.

    Rahotanni sun ce maharan sun rika bi gida-gida suna kwasar dukiya da dabbobin jama'a.

    Saurari rahoton Zahraddin Lawal.

  10. Ko majalisar Kano za ta yi sabuwar dokar masarautu?, Abubuwan da suke faruwa a Najeriya da makwabtanta

    Rahotanni daga jihar Kano a arewacin Nijeriya na cewa majalisar jihar za ta katse hutunta a yau domin yin sabuwar dokar kirkirar karin masarautu a jihar.

    Ana sa ran zaman wanda yake tamkar na gaggawa ne zai gudana a yau Laraba, inda za a gabatar da kudirin neman kirkirar masarautun a gaban majalisar, kamar yadda doka ta tanada.

    A ranar 6 ga watan Mayun bana ne dai majalisar ta gabatar da kudirin kirkirar masarautun Rano da karaye da Gaya da Bichi, inda aka yi wa dokar karatu na daya da na biyu da na uku aka kuma amince da dokar a rana daya.

    To sai dai a watan Nuwambar nan wata kotu ta rushe sababbin masarautun, inda ta ce ba a gabatar da kudirin dokar ba a kan ka’ida.

    Gwmmnatin jihar ta ce ba ta ji dadin hukuncin kotun ba, amma za ta dauki matakin da ya dace kan batun.

    Tuni dai ‘yan majalisar suka fara hallara zauren majalisar a safiyar yau domin zaman.

    To sai dai akawun majalisar ya ce ‘yan majalisar za su katse hutunsu ne domin amincewa da dokar kafa hukumar tallafawa ilimi ta jihar ta Kano.

    Wasu dai na ganin ‘yan majalisar za su yi amfani da damar wajen gabatar da kudirin dokar ta kirkirar masarautu.

    Bayanan da BBC ta samu daga majiyoyin majalisar sun tabbatar da cewa akwai maganar sake gabatar da kudirin dokar kirkirar masarautun, sai dai majiyoyin ba su tabbatar da cewa ko yau ne za a gabatar da kudirin ba.

  11. Barka

    Jama'a barkanmu da safiyar Laraba. Ku duba kasa domin karanta labaran ranar Talata, sama kuma don karanta na yau Laraba.

  12. An kai tsohon kwamishinan Zamfara gidan yari

    Wata kotu a jihar Zamfara da ke arewacin Nijeriya ta bayar da umarnin tsare wani tsohon kwamishina a jihar Ibrahim Dan Malikin Gidan Goga a gidan yari har zuwa 12 ga watan Disamba.

    A ranar Talatar ne kotun ta ba da umarnin kai tsohon kwamishinan gidan yari, bayan an gurfanar da shi gabanta bisa tuhumar bata sunan gwamnan jihar ta Zamfara Bello Matawallen Muradun.

    'Yan sanda sun kama tsohon kwamishinan nan ne a ranar Litinin, bisa zargin tunzura jama’a, kamar yadda sammacin kama shi ya nuna.

    Makusantansa sun shaida wa BBC cewa an tsare shi a sashin binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sandan jihar.

    Sun yi zargin cewa an kama shi ne bisa umarnin gwamnan jihar Bello Matawalle, sai dai mai magana da yawun gwamnan, Yusuf Idris ya musanta cewa akwai hannun gwamnati a kamen.

    Ya shaida wa BBC cewa ‘yan sanda ne kawai suka kama Ibrahim Dan Malikin, ba tare da saka hannun gwamnatin jihar ba.

    A ranar Asabar din da ta gabata ne dai Ibrahim Dan Maliki ya mayar wa gwamna Matawalle martani kan zargin da ya yi cewa tsohon gwamnan jihar Abdulaziz Yari ne yake haifara da tashe-tashen hankula da kashe-kashe a jihar.

    A hirarsa da BBC, Gwamna Matawalle ya yi barazanar kama Abdulaziz Yari idan ya sake shiga jihar aka samu tashin hankali.

    Bangaren tsohon gwamnan dai sun musanta wadannan zarge- zarge.

  13. Nijar

    A jamhuriyar Nijar yayin da ake shirye shiryen rufe kamfanin hakar Uranium na Cominak, ma'aikatan kamfanin da ma mazauna garin Akokan inda kamfanin yake sun shiga hali na zulumi.

    Sakataren kungiyar ma'aikatan ma'adanai Mutari Abubacar ne ya bayyana wa BBC cewa su ma'aikatan kamfanin ba su ma gamsu da hujjojin da masu kamfanin suka bayar ba.

    Eљ(a=5Lq"

  14. Jami'ar Akure ta kori dalibai shida kan dukan wata daliba

    Jami'ar Gwamnatin Tarayya ta Akure a Najeriya ta kori dalibai shida da suka ci zarafin wata daliba ta hanyar lakada mata duka.

    Daliban da aka kora din sun hada da Popoola Olaniyi Agboola 'yar aji uku da Oluwadare Faith Tobiloba 'yar aji biyu da Nandi Yohanna Jessica 'yar aji biyu da Ajuwon Tolani Emmanuella 'yar aji daya da Emmanuel Funmilayo Taiwo 'yar aji daya da kuma Alao Olabimpe Cecilia 'yar aji daya.

    Daraktan yada labarai na jami'ar Adegbenro Adebanjo, ya ce an kori daliban ne saboda sakamakon binciken da aka yi ya nuna sun aikata laifin a wajen makaranta ranar 16 ga watan Nuwambar 2019.

  15. Mataimakin shugaban kasa ya dawo aiki bayan jinyar wata hudu

    Mataimakin shugaban kasar Zimbabwe Constantino Chiwenga ya koma bakin aiki bayan da ya shafe wata hudu yana jinya.

    Mr Chiwenga ya koma kasarsa a ranar Asabar daga China, inda ake jinyarsa kan cutar da ba a bayyana ba.

    An yi ta duba shi a wani asibiti a Afirka Ta Kudu da Indiya kafin a wuce da shi China.

    Jim kadan bayan isarsa gida, Mr Chiwenga, wanda yana daga cikin na gaba-gaba da suka hambarar da Shugaba Robert Mugabe daga mulki, ya yi wata ganawar sirri da Shugaba Emmerson Mnangagwa.

  16. An daure mawaki kan 'zagin' 'yan sanda a kafafen sada zumunta a Moroko

    An yanke wa wani mawaki a Moroko hukuncin daurin shekara daya a gidan yari saboda cin mutuncin 'yan sanda da ya yi a shafukan sada zumunta.

    Mohamed Mounir, wanda ke amfani da sunan Gnawi, ya amsa laifinsa cewar ya zagi 'yan sanda lokacin da yake wani bidiyo kai tsaye a shafin Instagram, sa'o'i bayan da aka tsayar da shi a lokacin da yake tuki a Rabat, babban birnin kasar.

    Gnawi na daya daga cikin mawakan da ke tashe a Moroko, kuma ya shahara ne bayan da ya wallafa wata wakarsa mai taken ''Long Live the People' a shafin YouTube a watan da ya gabata.

    An kalli wakar wacce ke duba kan cin hanci da wadaka da kudin al'umma, sau miliyan 15.

    Masoyansa sun ce wakar ce ta saka shi a cikin matsala.

    Ya ce ya zagi 'yan sandan ne saboda irin halin rashin kirkin da aka yi masa.

    A kotu kuwa, cewa ya yi tun da ya zo duniya yake fuskantar gallazawa daga 'yan sanda.

  17. Tsawa ta fada kan jirgi a sararin samaniya

    Wani matukin jirgi a kasar Zambiya ya yi wata bajinta a ranar Litinin inda ya sauka lafiya da jirgin samfurin Dash 8-300, mai dauke da fasinjoji 41, bayan da tsawa ta fada kan jirgin.

    Lamarin ya faru ne a lokacin da jirgin mallakin kamfanin jiragen sama na Proflight da ke kasar, ke tunkarar babban birnin kasar Lusaka, bayan ya bar garin Livingstone.

    Jirgin yana tafiya ne a sararin samaniya lokacin da walkiyar ta shafe shi, har ma ta lalata hancin jirgin.

  18. Hotuna: Gwamnan Kaduna Nasir el-Rufa'i da mataimakiyarsa

    Gwamnan jihar Kaduna Nasir Ahmad el-Rufa'i da mataimakiyarsa Hadiza Sabuwa Balarabe suna tattaunawa a ofis a safiyar ranar Talata.

    Hotuna daga Maryam Abubukar a shafin Twitter.

  19. Matasa na son mamaye titunan Najeriya karo na biyu

    Wani maudu'i da aka kirkira a shafukan sada zumunta na Najeriya mai taken #OccupyNigeriaSeasonII yana ci gaba da tashe da daukar hankali.

    Matasa ne suka kirkiri maudu'in a kokarinsu na nuna adawa da sanya doka kan amfani da shafukan sada zumunta don hana labaran karya.

    Tuni dai kudurin dokar ya tsallake karatu na biyu a majalisar dattijan kasar.

    Sai dai mafiya yawan matasan kasar ba sa goyon bayan kudurin dokar.

  20. Wasikar Abdul'aziz Yari ta tayar da kura a Najeriya

    Wata wasika da ke shawagi a shafukan sada zumunta cikin Najeriya wadda ake zargin cewa tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdul’aziz Yari ne ya rubuta ta ga gwamnatin jihar ta haddasa ce-ce-ku-ce a tsakanin al’ummar Najeriya.

    Wasikar dai ta kunshi batutuwa da dama ko da yake, bukatar tsohon gwamnan ta neman a biya shi hakkokinsa na tsohon gwamna ta fi jan hankula.

    Buhari Muhammad Fagge ya bi diddigin wasikar ga kuma rahoton da ya hada mana. Sai ku latsa lasifikar da ke kasa don sauraro.