Shugaban kwamitin da ke kula da hukumar raya yankin Niger Delta (NDDC) a Majalisar Wakilan Najeriya Olubunmi Tunji-Ojo ya ce hukumar ta yi ta kashe kudi ba bisa ka'ida wato ba tare da yin kasafinsu ba a cikin kasafin kudi na tsawon wata 11.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito shi yana cewa NDDC ta sha aikata laifuka kan kasafin kudinta a cikin wata 14 da suka wuce sannan kuma har yanzu ba ta mika sabon kasafin ba ga Majalisar tun Satumban shekarar 2018.
Ya kara da cewa tun bayan da aka saka hannu kan kasafin kudin 2018 hukumar take kashe kudi ba tare da izini ba. Kazalika har yanzu ba ta mika kudirin kasafin kudinta na 2020 ga Majalisa ba, abin da ya kamata ta yi watanni da suka wuce.
"Labari ne maras dadin ji amma na ji dadi ganin cewa Majalisa ta tara tana bakin kokarinta wurin kula da jin dadin 'yan Njaeriya," in ji Olubunmi Tunji-Ojo, wakili daga jihar Oyo a jam'iyyar APC.
Ya ci gaba da cewa: "Za mu yi bincike kuma mu bayar da shawarwari masu karfi a kan ko su wane ne suka aikata hakan.
"Muna sane da cewa NDDC har yanzu tana aiki ne da kasafin kudi na 2018, wanda Majalisa ta takwas ta sahhale. Muna cikin Nuwamba amma har yanzu ba ta gabatar da kudirin kasafin 2020 ba.
"Wannan saba wa doka ne. Ba mu saba gani ba saboda tsara kasafi da kuma mika wa Majalisa ba wani abu ne mai wuya ba."