Masu sa ido a zabe 'sun gamsu' da shirye-shiryen INEC
Masu sanya ido a zabukan Najeriya na 2019 sun ce sun gamsu da shirye-shiryen da hukumar zaben kasar take yi na gudanar da zabe a jihar Kano da ke arewacin kasar. Sun bayyana wa taron manema labarai anar Juma'a cewa ba su da ja game da yadda INEC ke raba kayan aikin zabe.











































