Yadda ma'aikatan zabe suka kwana a ofis

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images
Wannan shafi na kawo muku labarai da rahotanni da bayanai har ma da martani kan matakin da hukumar zaben Najeriya ta dauka na dage zaben.
Nasidi Adamu Yahya and Mohammed Abdu

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Twitter

Asalin hoton, Twitter

Asalin hoton, Twitter
Tun kan a dage zabe wasu kayayyaki da za a yi aiki da su suka isa ofishin INEC a sassa daban-daban na Najeriya.
Shin ko yaya za a yi da su?

Asalin hoton, Getty Images
Auwal Adam: Allah ya saka shine mafi alkhairi ga yan Nigeria.
Sani Abubakar: Tabbas hukumar zabe ba ku yi wa talakawa adalci ba, domin wasu jama'a da dama sun kashe kudin motor daga wurare da dama sun dawo mahaifar su, domin su kada kuri'ar su amma kuka daga zabe gaskiyar magana ba ku yi mana adalci ba, amma shure shure baya hana mutuwa.
Muhammad Musa Waloji: Allah ya sa dage zaben da akayi ya zama alkhairi dama kasarmu baki daya ameeen. Mariya M Aliyu: Na sayi sababbin baturan radio dan sauraron BBC Hausa, yanzu kan wani satin sunyi sanyi, ya kamata hukumar zabe ta biya mu diyya, dan gaskiya anyi asarar dukiya.
Mutane da dama sun bayyana ra'ayoyinsu kan matakin da hukumar zaben Najeriya ta dauka na dage zaben kasar.
Ku latsa alamar lasifika don sauraron ra'ayoyin Kanawa kan batun:
A yayin da hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya INEC ta daga zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki sa'o'i kadan gabanin a fara kada kuri'a, BBC ta yi nazari kan ko sau nawa aka taba dage zabe a kasar.
A ranar biyu watan Afrilun 2011, an soma kada kuri'a a jihohi irin su Lagos da Kaduna da Kebbi da Zamfara, yayin da shugaban hukumar zaben kasar Farfesa Attahiru ya dage zaben.
Kazalika a ranar 8 ga watan shekarar 2015 ne shugaban INEC na wancan lokacin Farfesa Attahiru Jega ya dage manyan zabukan kasar, a lokacin da ya rage saura kwana shida a gudanar da su.
Farfesan ya sanar da dage zaben wanda aka sanya za a yi a ranar 14 ga watan Fabrairu, zuwa makonni shida.
Farfesa Jega ya ce ya yi hakan ne saboda barazanar matsalar tsaro da ake fuskanta.

Asalin hoton, Getty Images
Tun lokacin da aka soma yada jita-jitar cewa hukumar zaben Najeriya ta dage zaben kasar ne 'yan jarida suka yi wa ofishin hukumar da ke Abuja tsinke.
'Yan jarida sun kashe dare a ofishin hukumar suna jiran shugabanta, Farfesa Mahmood Yakubu ya fito ya yi musu jawabi kan matakin da hukumar ke shirin dauka.
Daga karshe dai, shugaban hukumar zaben ya fito bayan ya shafe tsawon lokaci, inda ya sanar da dage zabukan.


Abokin aikinmu Naziru Mika'il ya rubuta mana sharhi kan irin tasirin da dage zaben Najeriya zai yi. A sha karatu lafiya:
Sanarwar hukumar zaben ta kada zukatan 'yan kasar da dama, kuma za ta jawo ce-ce-ku-ce musamman tsakanin manyan jam'iyyun kasar, domin babu shakka kalaman na Farfesa Yakubu ba za su gamsar da dama daga cikin 'yan Najeriya ba.
Wani abu da zai kara bakantawa mutane rai shi ne yadda hukumar ta shafe shekara hudu tana shirya wannan zabe, amma kwatsam sai a mintinan karshe ta sauya matsaya.
Gabanin zaben dai gobara ta tashi a wasu ofisoshin hukumar amma ta dage cewa hakan ba zai shafi shirnta na zabe, kuma a yanzu ba ta ambaci hakan a matsayin dalili ba.
Sai dai tambayar a nan ita ce, mai ya sa sai yanzu, mai ya hana hukumar fitowa ta bayyana matsayinta tun farko, kuma mai ya sa ba ta dauki darasi daga ayyukanta na baya ba.
Jama'a da dama sun kashe kudade, wasu sun bar ayyukansu, wasu sun yi doguwar tafiya domin zuwa wuraren da za su kada kuri'unsu. Wannan mataki zai bakanta musu rai.
Wasu na hasashen wannan dagewar ka iya shafar adadin mutanen da za su fito domin kada kuri'unsu a mako mai zuwa.

Asalin hoton, Twitter/@nazirumikailu
Masu bibiyar shafukanmu na sada zumunta da muhawaa sun tofa albarkacin bakinsu kan matakin hukumar zaben Najeriya na dage zaben kasar. Ga ra'ayoyin wasu daga cikinsu:
Alhaji Zakariyya Aliyu Ba mu ji dadin dage zaben Najeriya ba amma ba yadda za mu yi.
Lawal Ibrahim Wannan dage zaben ya mayar da hannun agogo baya; a gaskiya hukumar zabe bata yimana adalci ba.
Muhammed Sani Umar Unity Gaskiya a Nigeria ba a damu da matsalar da talaka yake ci gaba fuskanta ba idan ba haka ba ta yaya za a dage zabe ba tare da la'akari da asarar dukiya da lokaci ba?
Kwamitin yaki neman zaben shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi allawadai da matakin hukumar zaben kasar, INEC, na dage manyan zabuka.
Sanarwar da Mr Festus Keyamo, mai magana da yawun kwamitin yakin neman zaben shugaban Najeriya ya fitar ta zargi INEC da hada baki da jam'iyyar hamayya ta PDP domin magudin zabe.
"Muna fatan INEC za ta zama 'yar ba-ruwanmu a wannan harka ta zabe domin kuwa jita-jitar da ake watsawa na cewa an dage zaben ne da hada bakin babbar jam'iyyar hamayya ta PDP, wacce da ma bata shirya shiga zaben ba," in ji Mr Keyamo.

Asalin hoton, TWITTER/@BASHIRAHMAAD
Dan takarar shugaban Najeriya na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya zargi gwamnatin Muhammadu Buhari da kitsa dage zaben kasar da zummar harzuka 'yan Najeriya.
Sai dai snarwar da Atiku Abubakar ya fitar ranar Asabar ta yi kira ga 'yan kasa da kada su karaya wajen sake fitowa su kada kudi'unsu.
"Sun sani cewa 'yan Najeriya sun yi shirin kayar da su, shi ya sa suka rude suna yin duk abin da za su iya wajen ganin basu sha kaye ba," in ji tsohon mataimakin shugaban kasar.
Ya kara da cewa gwamnatin Buhari ta kwashe shekara hudu tana shirin zabe amma sai da aka zo gargara take neman kwancewa 'yan Najeriya zane a kasuwa.

Asalin hoton, Twitter:@atiku
Tun da tsakar daren Juma'a ne hukumar zaben ta Najeriya ta ce ta dage zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki ne zuwa ranar 23 ga watan Fabrairu.
Da yake sanar da matsayin hukumar, shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya kara da cewa an dage zaben gwamnoni zuwa ranar tara ga watan Maris.
Nasidi Adamu Yahaya ne ke muku fatan kun wayi gari lafiya. Ku bibiye mu a wannan shafi domin samun bayanai da martani daga bangarori daban-daban kan matakin da hukumar zaben Najeriya ta dauka na dage zabukan kasar.
A nan muka kawo karshen labarai da rahotannin da muke kawo maku game da shirye-shiryen zaben Najeriya. Sai ku kasance da mu gobe da safe inda za mu kawo maku sabbin rahotanni game da yadda ake gudanar da zaben shugaban kasa da 'yan majalisar dokokin kasar.
Masu sa ido na kasashen waje kan zaben Najeriya sun yi taro a Abuja babban birnin kasar gabannin zabe a kasar. Tsohuwar shugabar Liberia Madam Ellen Johnson-Sirleaf ce ta jagoranci tattaunawar.
Sun bayyana cewa a shirye suke wajen sa ido a gudanar da sahihi da kuma ingantaccen zabe a kasar.
Sun kuma yi kira ga jam'iyyu da su martaba yarjejeniyar zaman lafiyar da suka sanya wa hannu da kauce wa rikice-rikice tare da amincewa da sakamakon zabe kuma idan suna da tantama a kan sakamakon zaben sai su bi hanyar da shari'a ta ce.
Shugaban hukumar zaben Najeriya Farfesa Mahmud Yakubu tare da wasu 'yan kungiyar ECOWAS sun halarci tattaunawar.

Asalin hoton, ECOWAS

Asalin hoton, ECOWAS
Majalisar dake kula da hulda tsakanin jam'iyyu kenan watau IPAC da suka kai ziyara ga Sarkin Fika Alhaji Dakta Abali Ibn Mohammadu Idris. Sarkin yayi kira ga matasa da su guji haddasa fitina ko wani abu da ka iya jawo rashin zaman lafiya a lokacin zabe da kuma bayan zabe.


Wasu daga cikin masu zabe a birnin Owerri dake jihar Imo da kuma birnin Makurdi dake jihar Benue a Najeriya sun bayyana ra'ayoyinsu a kan zaben kasar
Hotunan da wakilin mu na BBC a Miaduguri ya aiko mana kenan dangane da yadda ake kai kayan zabe da kuma shirye-shiryen da hukumar zaben ke yi na gudanar da zaben



Dan takarar shugaban Najeriya na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ce sakataren wajen Amurka Mike Pompeo ya yi masa waya ranar Juma'a inda ya jaddada alwashin kasarsa da kasashen duniya wurin ganin an yi zabe na gari a Najeriya.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X