Sai wani lokacin
A nan muka kawo karshen sharhin da muke kawo mu ku kai tsaye.
Mu hadu a wasannin zagaye na biyu da za a fafata a gasar cin kofin duniya a Rasha.
Sai wan lokacin.
Senegal ta kasa tsallakewa zuwa zagaye na biyu a gasar cin kofin duniya bayan Colombia ta doke ta 0-1 a wasan rukuni na karshe da suka fafata.
Abdulwasiu Hassan and Awwal Ahmad Janyau
A nan muka kawo karshen sharhin da muke kawo mu ku kai tsaye.
Mu hadu a wasannin zagaye na biyu da za a fafata a gasar cin kofin duniya a Rasha.
Sai wan lokacin.

An fitar da Senegal, kasa ta karshe da ta rage a Rasha daga Afirka.
Yanzu za a buga zagaye na biyu babu kasa daya daga Afirka.
Colombia ta samu sa'ar Senegal 0-1
Senegal na bukatar ta ci kwallo
Borja ya karbi Falcao
Saura minti biyu lokaci ya cika
Sakho ya karbi Niang

Asalin hoton, FIFA
Lerma ya karbi Uribe
Senegal na kokarin ta farke
Japan da Senegal dukkaninsu yanzu suna a maki hudu, kuma ba banbanci a yawan kwallaye.
Wata kila za a diba kasar da tafi karbar katin gargadi.
Mane ya yi kokarin sa kai amma Golan Colombia ya kame kwallon
Mina ne ya zura kwallon a ragar Senegal a bugun kwana

Asalin hoton, Getty Images
Colombia za ta tsallake Idan ta tashi babu ci da Senegal bayan Poland ta sha Japan.

Asalin hoton, FIFA