Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni dangane da muhimman batutuwa da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 03/05/2025.

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed da Abdullahi Bello Diginza

  1. Isra'ila ta tabbatar da kai hari a Syria

    Netanyahu

    Asalin hoton, Reuters

    Sojojin Isra'ila sun tabbatar da kai hari yankin sojin Syria, bayan ƙungiyar da ke sa ido a yaƙin ƙasar ta ce sun kai sama da hare-hare ta sama 20 a sassan ƙasar.

    Wakilin BBC ya ce kafar yaɗa labaran Syria ta ce ababen fashewa sun tashi a arewaci birnin Damascus da wajen kusa da birnin Hama.

    An kuma ba da rahotannin wasu hare-haren a Latakia da arewa maso yammacin yankin Idlib.

    Wannan na zuwa ne bayan hari ta sama da Isra'ilar ta kai kusa da fadar shugaban ƙasa a birnin Damacus a jiya Juma'a.

  2. Buɗewa

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Asabar, inda za mu ɗaura daga inda aka tsaya a jiya Juma'a wajen kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Ku kasance tare da mu