Labarin wasanni daga 16 zuwa 22 ga watan Agustan 2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 16 zuwa 22 ga watan Agustan 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu da Umar Mikail

  1. Calafiori ne ya ci wa Arsenal ƙwallo a Old Trafford, Manchester United 0-1 Arsenal

    Calafiori

    Asalin hoton, Getty Images

    Arsenal ta yi nasarar cin Manchester United 1-0 a ranar Lahadi a Old Trafford a wasan makon farko a Premier League, inda Calafiori ne ya ci mata ƙwallon.

    Sai dai an yi ta batun ƙwazon golan United, Altay Bayindir, wanda ya maye gurbin Andre Onana, wanda ke jinya.

    United ta taka rawar gani sosai da kai hare-hare masu haɗari, amma mai tsaron ragar Arsenal, David Raya ya hana ƙwallo ya shiga raga.

  2. Gossip

    Asalin hoton, Getty Images

    Atalanta na fatan cimma yarjejeniya da Fulham kan ɗan wasan gaba a Brazil, Rodrigo Muniz mai shekara 24, kan yuro miliyan 40. (Teamtalk)

    Ɗan wasan gaba a Faransa, Randal Kolo Muani mai shekara 26, ya amince da ya rage albashinsa domin komawa Juventus daga Paris St-Germain, a yarjejeniyar yuro miliyan 60. (Corriere dello Sport in Italian)

    Tottenham na nazari kan ɗan wasan nan mai shekara 24 daga Real Sociedad da Japan, Takefusa Kubo yayinda Thomas Frank ke kokarin raba kafa. (Fichajes - in Spanish)

    Burnley da Sunderland kowanne na son ɗan wasan FC Copenhagen da Brazil Gabriel Pereira mai shekara 25. (Teamtalk)

    Arsenal na son ɗauko ɗan wasan tsakiya a Barcelona, Frenkie de Jong mai shekara 28. (Fichajes - in Spanish)

  3. Sakamakon wasannin makon farko a Premier League

    Ranar Juma'a

    • Liverpool 4-2 Bournemouth

    Ranar Asabar

    • Aston Villa 0-0 Newcastle
    • Brighton 1-1 Fulham
    • Sunderland 3-0 West Ham
    • Tottenham 3-0 Burnley
    • Wolves 0-4 Manchester City

    Ranar Lahadi

    • Chelsea 0-0 Crystal Palace
    • Nott'm Forest 3-1 Brentford
    • Manchester United 0-1 Arsenal

    Wasan ranar Litinin

    • Leeds v Everton
  4. Za a karasa wasan Premier tsakanin Leeds da Everton ranar Litinin, Premier League

    Premier League

    Asalin hoton, Getty Images

    Ranar Litinin za a kammala wasan makon farko a Premier League, inda Leeds United za ta karɓi bakuncin Everton.

    Tun daga ranar Juma'a aka buɗe labulen gasar bana ta 2025/26, inda Liverpool mai rike da kofin ta doke Bournemouth da ci 4-2 a Anfield

  5. Arsenal ta fara da samun maki uku a kan United a Premier League

    Arsenal

    Asalin hoton, Getty Images

    Arsenal ta fara da samun maki uku a Premier League, bayan da ta doke Manchester United 1-0 a Old Trafford.

    Da wannan sakamakon Mikel Arteta ya yi nasara a kan United karo na takwas a Premier League daga karawa 12 daga ciki ya yi canjaras biyu aka doke shi wasa biyu.

    Shi kuwa Ruben Amorin ya sha kashi karo na 15 a Premier League daga wasa 28 a United daga ciki ya yi nasara bakwai da canjaras shida.

    To sdai dai United ta kai hari sau 20 a karawar, karon farko a Premier League da ta fuskanci Arsenal da yin wannan ƙwazon tun bayan da ta doke Gunners 8-2 a Agustan 2011.

  6. Palace tana sa ran Eze zai kara buga mata wasa

    Eze

    Asalin hoton, Getty Images

    Kociyan Crystal Palace, Oliver Glasner na sa ran Eberechi Eze zai kara buga musu wasa, duk da cewar ana kan cinikinsa zuwa Tottenham.

    Bayan da Palace ta tashi 0-0 ranar Lahadi a gasar Premier League, Glasner ya sanar da manema labarai cewar ana yawan jita-jita kan makomar Eberechi Eze da kuma Marc Guehi, sai dai har yanzu ƴan wasan mune.

    Ranar Alhamis, Palace za ta kara da Fredrikstad a wasan cike gurbin shiga Conference League.

    Palace ta samu damar shiga gasar zakarun Turai a karon farko a tarihi, bayan da ta lashe FA Cup, sai dai ta rasa gurbin shiga Europa League, sakamakon shugaba da yake da wani hannun jarin a wata ƙungiya da itama za ta shiga wasannin.

  7. Brentford ta kammala sayen Ouattara daga Bournemouth

    Gossip

    Asalin hoton, Getty Images

    Brentford ta kashe fam miliyan 42.5 wajen sayen Dango Ouattara daga Bournemouth.

    Ɗan wasan tawagar Burkina Faso ya amince da ƙunshin yarjejeniyar kaka biyar da cewar za a tsawaita masa da zarar ya taka rawar gani.

    Ana cewa mai shekara 23, wanda ya ci ƙwallo tara a wasa 37 a dukkan karawa a kakar da ta wuce, shi ne madadin Bryan Mbeumo, wanda ya koma Manchester United a watan Yuli..

  8. Sunderland ta ɗauki Mukiele daga PSG

    Mukiella

    Asalin hoton, Getty Images

    Sunderland ta kammala sayen ɗan wasan tawagar Faransa mai tsaron baya, Nordi Mukiele daga Paris St-Germain kan fam miliyan 12, kenan ta kashe fam miliyan 141.5 wajen sayen ƴan ƙwallo a bana.

    Mai shekara 27 ya amince da ƙunshin yarjejeniyar kaka huɗu, ya kuma koma Sunderland kwana ɗaya da ta dfoke West Ham 3-0 a makon farko da fara Premier League ta kakar nan.

    Mukiele, wanmda ya buga wasannin aro a gabaki ɗayan kakar da ta wuce a Bayer Leverkusen, shi ne na 12 da Sunderland ta ɗauka a kakar nan.

    Daga cikin waɗanda ta ɗauka a bana har da tsohon ɗan wasan Arsenal, Granit Xhaka da Simon Adingra daga Brighton da Habib Diarr daga Strasbourg.

    Nottingham Forest ce kan gaba a yawan sayen ƴan wasa a kaka ɗaya da ta ɗauki 21 kan fam miliyan 142.

  9. Sancho

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester United na shirin karɓan tayin Roma kan ɗaukan aron ɗan wasanta na Ingila Jadon Sancho, amma tana jiran ɗan wasan mai shekara 25 ya kammala shawararsa. (Fabrizio Romano)

    Everton na duba zaɓin da suke da shi kan Tyler Dibling mai shekara 19, bayan rashin nasara a tayin da suka gabatar har sau uku - na karshen ya kai fam miliyan 37 - wanda Southampton ke fatali da shi. (Liverpool Echo)

    Galatasaray ta gabatar da tayinta kan ɗan wasan Manchester City da Brazil, mai tsaron raga, Ederson mai shekara 31 kan fam miliyan 8.6. (Fabrizio Romano)

    Chelsea na iya sayen ɗan wasan Argentina, Alejandro Garnacho mai shekara 21, daga Manchester United da mai buga tsakiya a Netherlands, Xavi Simons mai shekara 23, daga RB Leipzig idan sun shirya rabuwa da 'yan wasa biyu. (Sky Sports)

  10. Hojlund ba zai buga wa United wasa da Arsenal ba

    Rasmus Hojlund ba zai buga wa Manchester United wasan Premier League ba da za ta kara da Arsenal a Old Trafford ranar Lahadi.

    An ce Ruben Amorin ya ɗauki wannan hukuncin, sakamakon raɗe_raɗi da ake yi kan makomar ɗan wasan mai shekara 22.

    Hojlund ya fayyace cewar yana son ci gaba da taka leda a United, sai dai sayen Benjamin Sesko daga RB Leipzig da United ta yi, ya sa shakku kan makomar ɗan ƙwallon.

    Amorim ya ajiye Hojlund a benci a wasan sada zumunta da Fiorentina a Amurka, inda ya yi amfani da Mason Mount a gurbin mai cin ƙwallaye.

    Mason ne zai yi lamba tara a wasa da Arsenal yayin da Joshua Zirkzee zai yi zaman benci.

    Ana cewa AC Milan ce ke son ɗaukar Hojlund, amma har yanzu ƙungiyar Serie A ba ta ce komai ba kan batun.

  11. gossip

    Asalin hoton, Getty Images

    Roma ta amince da yarjejeniyar saye ɗan wasan Aston Villa da Jamaica, Leon Bailey mai shekara 28, kan zaman aron da aka yi wa kuɗi fam miliyan 1.7 da kuma zaɓin saye shi kan fam miliyan 20. (La Gazzetta dello Sport)

    Nottingham Forest ta amince da yarjejeniya kan ɗan wasan Rennes mai shekara 23 daga Faransa, Arnaud Kalimuendo kan fam miliyan 25. (Telegraph)

    Crystal Palace ta tuntuɓi Leicester City kan saye Bilal El Khannouss mai shekara 21, daga Moroko wanda ake son ya maye gurbin Eberechi Eze. (Athletic - subscription required)

    Manchester United za ta sake farfaɗo da farautarta kan ɗan wasan tsakiya a Brighton da Kamaru, Carlos Baleba a kakar 2026. (Fabrizio Romano)

    Chelsea ta shiga tattaunawa da Bayern Munich kan sayar da ɗan wasan Faransa, Christopher Nkunku mai shekara 27. (Mail)

    Fenerbahce na shirin saye ɗan wasan Arsenal da Ukraine, Oleksandr Zinchenko mai shekara 28. (Sporx - in Turkish)

  12. Forest ta gabatar da sabbin ƴan wasan da ta ɗauka a bana

    Forest

    Asalin hoton, Getty Images

    Nottingham Forest ta gabatar da sabbin ƴan wasanta, Omari Hutchinson da James McAtee a City Ground, sai dai ba za su buga mata wasa da Brentford ba.

  13. Me ya sa Chelsea ba ta tallan kamfani a rigarta a bana, Chelsea

    Chelsea

    Asalin hoton, Getty Images

    Chelsea ce kaɗai dake Premier League da fara kakar bana ba tare da kamfanin da take yiwa talla ba, ko mai ya sa?

    Koda yake yanzu kamfanoni da yawa na rubibin ganin sun yi hulɗa da Chelsea, wadda ke fatan fayyace kamfanin da za ta yi hulɗa da shi lokaci mai tsawa.

    Ƙungiyar Stamford Bridge na fatan ƙulla yarjejeniyar fam miliyan 60 zuwa fam miliyan 65 a duk kaka, bayan da ta samu gurbin shiga Champions League da za a yi a bana.

    Ana ta alakanta kamfanin zirgin sama na Saudiyya, Riyadh Air da cewar shi ne zai kulla yarjejeniya da Chelsea.

    Ko a bara Chelsea ba ta tallata kowanne kamfani ba a gaban rigarta ba a farkon kakar tamaula, sai a watan Afirilu ne ta samu cimma yarjejeniya da wani kamfanin Dubai mai suna Damac.

    Haka ma a 2023/24 Chelsea ba ta samu wani kamfanin da ta yiwa talla ba, kafin daga baya ta kulla yarjejeniyar fam miliyan 40 da wani kamfanin Amurka Infinite Athlete.

  14. United za ta karɓi bakuncin Arsenal a Premier League

    Premier League

    Asalin hoton, Getty Images

    Arsenal za ta je Old Trafford, domin buga wasan makon farko a Premier League ranar Lahadi.

    Wannan shi ne karo na tara da United za ta fara wasan farko a babbar gasar tamaula ta Ingila.

    Wannan shi ne kaka ta 100 da Arsenal za ta buga gasar Lik a Ingila, ta kuma yi nasara biyar daga shida baya a wasan makon farko.

    Haka kuma Gunners ta yi wasa 14 a jere a waje ba tare da rashin nasara ba tun bayan da Tottenham ta yi nasara a kanta da ci 1-0 a watan Nuwamba a St James Park.

    United ta yi nasarar cin karawa 22 a ranar buɗe gasar lik, kuma wannan shi ne karon farko da za a fafata tsakanin United da Arsenal a makon farko, bayan da ƙungiyar Old Trafford ta ci Gunners 4-1 a 1989/90.

    Sabon ɗan wasan da Arsenal ta ɗauka bana Viktor Gyokeres ya zama kan gaba a cin ƙwallaye kaka biyu tsakanin manyan gasar Turai 10. ya ci ƙwallo 68 a wasa 66 a Sporting tsakanin 2023/24 da 2024/25.

    United ta yi nasara a kan Arsenal sau 99 a karawa 243 a dukkan fafatawa daga ciki ta yi canjaras 55 aka doke ta 89, kenan United na fatan cin Arsenal karo na 100 a tarihi.

  15. Baleba

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester United ta dakatar da zawarcin da take yi wa dan wasan tsakiya na Kamaru Carlos Baleba, mai shekara 21 a wannan bazarar, inda ake ganin fan miliyan 115 da Brighton ta ke so kan dan wasan ya yi yawa. (Athletic - subscription required)

    Golan Manchester City Ederson, mai shekara 31, yana tunanin makomarsa a kulob din tare da yiwuwar komawa Galatasaray. Idan dan wasan na Brazil ya bar City, City za ta koma siyan dan wasan Paris St-Germain Gianluigi Donnarumma, mai shekara 26 (Guardian)

    Newcastle Newcastle ta shirya tsaf domin kulla yarjejeniya da dan wasan gaba na Brentford da DR Congo Yoane Wissa, mai shekara 28.(Sky Sports), external

    Kungiyar Al-Nassr ta Saudi Pro League tana gab da kammala cinikin fan miliyan 25.8 don siyan dan wasan gefe na Faransa Kingsley Coman daga Bayern Munich.(Talksport)

  16. Frank ya fara da samun maki uku a kan Burnley

    Thomas Frank ya fara jan ragamar Tottenham da kafar hagu, bayan da ya doke Burnley 3-0 a wasan makon farko a Premier League.

    Richarlison ne ya ci ƙwallo biyu daga ciki, inda Frank ya zama koci na shidfa da ya fara nasara a ranar farko a Premier League daga tsakanin masu horar da tamaula tara, uku daga ciki suka yi canjaras.

    A tsakiyar mako Tottenham ta yi rashin nasara a bugun fenariti a hannun Paris St Germain bayan da suka tashi 2-2 a Uefa Super Cup a Udinese.

    Richarlison

    Asalin hoton, Getty Images

  17. Gossip

    Asalin hoton, Getty Images

    Wolves na dab da daukar dan wasan bayan Verona da Kamaru Jackson Tchatchoua, mai shekara 23.(Athletic - subscription required)

    Sunderland ta amince da yarjejeniyar siyan dan wasan bayan Paris St-Germain da Faransa Nordi Mukiele, mai shekara 27, kan fam miliyan 9.5 a matakin farko tare da karin fam miliyan 2.5.(Northern Echo)

    Dan wasan tsakiya na Juventus da Argentina Nicolas Gonzalez, mai shekara 27, yana sha'awar komawa Atletico Madrid kan Yuro miliyan 30 a bazara. (La Gazzetta dello Sport - in Italian)

  18. United ta daina zawarcin Baleba na Brighton

    Baleba

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester United ta daina zawarcin Carlos Baleba daga Brighton.

    Tun farko ba a taya ɗan ƙwallon ba, amma United ta tambaya ko nawa ne farashin mai shekara 21, kuma ko Brighton za ta amince ta saki ɗan wasan.

    Wata majiya ta ce Brighton ba ta shirya sayar da ɗan wasan ba, sannan koci, Fabian Hurzeler ya ce yana tabbaci ɗan kasar Kamaru bai shirya barin Brighton ba.

    United ƙungiyar da Ruben Amorin ke jan ragama za ta karɓi bakuncin Arsenal ranar Lahadi a gasar Premier League, sai ta fuskanci Chelsea da Manchester City a wasannin gaba.

  19. Barcelona ta yi rijistar Rashford da wuri don buga La Liga

    An kammala yi wa Marcus Rashford rijista da wuri, domin ya samu buga wa Barcelona wasan La Liga da Mallorca ranar Asabar.

    Domin ganin an bi dokar kashe kuɗi daidai samu ta La Liga, Barcelona ta ci karo da cikas a yiwa wasu ƴan wasanta rijista a kakar da wuce.

    A kakar da ta gabata, Barcelona ta kashe kuɗi da yawa wajen sayen ƴan ƙwallo da biyan albashi, fiye da abinda ta samu na kuɗin shiga.

    Har a ranar Juma'a ba a kammala yi wa Rashford Rijista ba, inda Hantsi Flick ya bayyana ɓacin ransa, daga baya komai ya daidata.

    A ranar Asabar da sanyin safiya an ga sunan Rashford da mai tsaron raga Joan Garcia a jerin ƴan wasan Barcelona da ta wallafa a kan Intanet.

    Rashford

    Asalin hoton, Getty Images

  20. Ana tsare da wanda ya yi wa Semenyo kalaman wariya

    Semenyo

    Asalin hoton, FC Bournemouth/Getty Images

    Ana tsare da wani mutum, bayan da ɗan wasan Bournemouth, Antoine Semenyo ya yi korafin an ci zarafinsa a Anfield a wasan da Liverpool ta ci 4-2 ranar Juma'a a makon farko na fara Premier League.

    A wasan sai da aka dakata na ƴan mintuna, bayan da ɗan ƙwallon ya yi korafi ga Rafli.

    Ƴansanda Merseyside sun ce suna tsare da wani mai shekara 47 daga Liverpool, wanda aka fito da shi daga filin Anfield bayan da aka tabbatar shi ne ya aikata laifin.

    An kuma tsare shi ranar Asabar, inda ake zarginsa da cin zarafin ɗan wasan.