Kwale-kwale ya kife da ƴan cirani 25 a Comoros

Hukumar kula da ƴan cirani ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce aƙalla mutane ashirin da biyar ne suka mutu bayan da masu safarar mutane suka kifar da wani kwale-kwale da gangan a tsibirin Comoros.
Kwale-kwalen mai ɗauke da mutane kusan talatin daga kasashe daban-daban, ciki har da jarirai biyu, yana kan hanya ne daga Anjouan zuwa yankin Mayotte na Faransa.
Masunta sun ceto mutane biyar da suka tsira da safiyar Asabar.
Hukumar kula da ƴan cirani ta duniya ta ce wannan hanya ta yi sanadin mutuwar dubban mutane, yayin da mutanen da ke gudun hijira a yankin Afirka ke ƙoƙarin tafiya mai haɗari zuwa nahiyar Turai.



















