Haruna Kakangi, Isiyaku Muhammed da Aisha Babangida
Zelensky zai gana da Erdogan gabanin tattaunawa da Putin
Shugaban Ukraine Vlodymyr Zelensky, zai je Ankara, babban birnin Turkiyya domin ganawa da Shugaba Erdogan gabanin tattaunawar zaman lafiyar da za a yi da Shugaba Putin.
Shugaban na Rasha ya buƙaci a tattauna kai-tsaye a ranar Alhamis a Santanbul tsakanin ƙasarsa da kuma Ukraine, to amma bai bayyana ko zai samu damar halartar tattaunawar ba.
Da yake jawabi a Kyiv, Shugaba Zelensky, ya jaddada aniyarsa ta halartar tattaunawar, to amma ya ce sai idan har Mista Putin ya je wajen domin su gana ido da ido.
A ɓangare guda kuma shugaba Trump ya tabbatar da cewa sakataren harkokin wajen Amurka, Marco Rubio, zai halarci tattaunawar a madadin gwamnatin Amurka.
Harin Isra'ila ya kashe mutum shida a asibitin Gaza
Rahotonni daga Gaza na cewa akalla mutum aka kashe, tare da raunata wasu 40 a wani hari ta sama da Isra'ila ta kai kan harabar wani asibiti a yankin.
Bayani sun ce an ajiye bama-bamai shida a asibitin da ke Khan Younis.
Rundunar sojin Isra'ila ta ce ta kai harin kan matattarar da 'yan Hamas suke da cibiyoyin da suke iko da su sannan kuma ta dauki matakai don rage yawan fararen hular da harin zai shafa.
Boko Haram: Majalisar dattawa ta buƙaci rundunar soji ta aika dakaru Borno da Yobe
Majalisar dattawan Najeriya ta buƙaci rundunar sojin ƙasar ta gaggauta aika ƙarin dakaru zuwa jihohin Borno da Yobe, bayan sake ɓullar hare-haren Boko Haram a yankunan.
Matakin na zuwa ne bayan sake ɓullar sabin hare-haren ƙungiyar a yankunan arewa maso gabashin ƙasar.
Ko a ranar Litinin ma wani ari da ƙungiyar ta kai kan barikin sojoji da ke garin Marte a ƙaramar hukumar Munguno ya kashe sojoji masu yawa.
Cikin wani ƙudiri da babban mai tsawatarwa na majalisar, Sanata Tahir Munguno ya gabatar, majalisar ta yarda cewa idan aka haɗa kai tsakanin jamai'an tsaro da masu sa kai za a iya kawar da ayyukan ƙungiyar.
'Trump zai gana da shugaban Syrian a gobe Laraba'
Wani jami'i Fadar Whote House ya ce Shugaba Trump zai gana da sabon shugaban Syria Ahmed al-Sharaa.
Trump ya ce zai janye wa ƙasar takunkuman da Amurka ta sanya mata, yana mai cewa zai ''bai wa ƙasar damar inganta kanta''.
Jami'in ya ce a gobe Laraba ne Shugaban na Syria, Ahmed al-Sharaa zai halarci Saudiyya domin ganawa da Trump wanda ke ziyara a ƙasar.
Majalisar Wakilan Najeriya ta yi watsi da ƙudirin karɓa-karɓa a kujerar shugaba ƙasa
Asalin hoton, Hon Tajudeen Abbas/X
Bayanan hoto, Shugaban Majalisar Wakilan Najeriya, Hon Tajudeen Abbas
Majalisar Wakilan Najeriya ta yi fatali da ƙudirin karɓa-ƙarba a kujerar shugabancin ƙasar.
Ƙudirin ya ƙunshi tanadin zagayawa da kujarar shugabancin ƙasar da ta mataimakinsa zuwa yankunan ƙasar shida.
A lokacin zamanta na yau Talata, majalisar ta kuma yi watsi da wasu ƙudurori shida da suka kasa tsallake karatu na biyu.
Ciki har da ƙudirin neman cire wa hukumar zaɓen ƙasar ikon yi wa jam'iyyun siyasa rajista da tsara musu dokoki.
Amurka da Saudiyya sun ƙulla yarjejeniyar kasuwanci ta dala biliyan 600
Asalin hoton, Reuters
Shugaban Amurka Donald Trump da Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman sun sanya hannu kan yarjejeniyar kasuwanci tsakaninsu da ta kai fiye da dala biliyan 600.
Yarjejeniyar - wadda ta ƙunshi tsaro ta fiye da dala biliyan 140 - ita ce cinikayya da aka ƙulla mafi girma a tarihi.
Sauran fannonin da yarjejeniyar ta shafa sun ƙunshi fannin makamashi, da ma'adinai da fasahar ƙirƙirarriyar basira ta AI.
Duka ƙasashen biyu sun amince da waɗannan yarjejeniyoyin a lokacin ziyarar Trump ta farko zuwa ƙasashen Larabawa tun bayan komawarsa fadar White House.
Nan gaba kaɗan Mista Trump zai wuce zuwa Qatar daga nan ya zarce ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.
WHO ta yi gargaɗin samun mummunan tasirin yunwa kan ƙananan yara a Gaza
Asalin hoton, WHO
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi gargaɗin cewa ƙaruwar matsalar yunwa ka iya yin mummunan tasiri kan rayuwar maso tasowa a Gaza.
WHO ta ce rashin abinci a yankin zai shafi girman ƙananan yara da ginuwar tunanin ƙwakwalensu.
Isra'ila ta hana shigar da kayan agaji zuwa cikin Gaza na kusan tsawon wata biyu tana mai cewa ta ɗauki matakin ne domin matsa wa Hamas lamba ta saki duka Isra'ilawan da take garkuwa da su.
Isra'ila ta zargi Hamas na sace kayan agajin a baya, zargin da ƙungiyar ta musanta.
Wani rahoto da aka fitar ranar Litinin ya ce mutum 500,000 a yankin na fuskantar matsananciyar yunwa.
Hotunan ƙaddamar da littafin Sule Lamido a Abuja
Toshon gwmanan jihar Jigawa Sule Lamido ya ƙaddamar da littafin da ya rubuta kan tarihitin rayuwarsa.
Taron ƙaddamar da littafin - da aka gudanar a Abuja - samu halartar jiga-jigan ƴansiyasa da tsoffin ma'aikatan gwamnati.
Littafin ya ƙunshi tarihin rayuwar ɗan siyasar da wasu bayanai game da wasu abubuwan da suka faru a tarihin siyasar Najeriya
Yadda aka yi wa Donald Trump tarbar ƙasaita a Saudiyya
Ga wasu hotuna daga ziyarar da shugaban Amurka Donald Trump ke yi, karon farko a Gabas ta tsakiya, inda yanzu haka yake a ƙasar Saudiyya.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Mahaya dawaki ɗauke da tutocin Amurka da na ƙasar Saudiyya na yi wa motar da ke dauke da Donald Trump rakiya a lokacin da ya isa Saudiyya.
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Trump na sarawa tare da yarima Mohammed Bn Salman
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Donald Trump ya tattauna da yarima Bn Salman jim kaɗan bayan isar sa
Asalin hoton, Getty Images
Kotu ta fara shari'ar dakatar da Sanata Natasha daga majalisa
Asalin hoton, others
Sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya a majalisar dattijan Najeriya, Natasha Akpoti-Uduaghan ta halarci zaman kotu a shari'ar da take ƙalubalantar dakatarwar da aka yi mata daga majalisar.
A watan Maris ne majalisar dattijan ta dakatar da Natasha bisa zargin rashin ɗa'a bayan taƙaddamar da ta kaure tsakaninta da shugaban majalisar Godswill Akpabio.
A cikin ƙorafinta, Natasha ta haɗa majalisar tarayya da majalisar dattawa da shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, da kuma Sanata Neda Imasuen, shugaban kwamitin majalisar dattawa kan ladabi da haƙƙoƙi da ɗabi’a a matsayin waɗanda ake ƙara.
Lokacin da aka kira shari’ar, wadda aka mayar a hannun Justice Binta Nyako bayan Justice Obiora Egwuatu ya janye daga sauraron ta, lauyan Sanata Natasha, Jibrin Okutekpa, ya shaida wa kotu cewa sun gabatar da dukkan takardun da za su dogara da su a shari’ar, kamar yadda kotu ta umarta a zaman da ya gabata.
Lauyoyin da ke wakiltar majalisar dattawa, Paul Daudu, da na shugaban majalisar, Ekwo Ejembi, su ma sun shaida wa kotu cewa sun gabatar da takardun da za su dogara da su. Amma sun jawo hankalin kotun kan wani buƙata da suka shigar dangane da rashin bin umarnin kotu da suke zargin wanda ke karar da aikatawa.
Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, a cikin wa’adin martaninta na ƙari, ta zargi shugaban majalisar dattawa da ƙoƙarin tauye mata haƙƙinta na faɗin albarkacin baki
Ta ce wasikar da ta rubuta kwanan nan zuwa ga shugaban majalisar dattawa ba ta karya umarnin kotu ba, wanda ya haramta wa ɓangarorin da ke cikin shari’ar yin magana da kafafen yaɗa labarai.
Rikici da sauyin yanayi sun tarwatsa sama da mutum miliyan 80 a duniya
Sabbin alƙaluma sun bayyana cewa yanzu haka akwai sama da mutum miliyan 80 da aka raba da muhallansu a faɗin duniya, kuma wannan ne mafi yawa da aka taɓa samu a tarihi.
Alƙaluman da cibiyar sanya ido kan yadda ake raba mutane da muhallansu da kuma hukumar kula da ƴan gudun hijira ta Norweian Refugee Council suka wallafa sun nuna cewa yawan mutanen ya nunka fiye da sau biyu a cikin shekara shida.
Rahoton ya ce kimanin mutum miliyan 74 ne rikice-rikice suka tursasa wa barin gidajensu.
Yaƙin Sudan kawai ya tarwatsa mutum sama da miliyan 11 - wanda shi ne mafi yawa da aka samu a ƙasa ɗaya.
Sai kuma bala'o'in da sauyin yanayi ke haifarwa waɗanda suka yi sanadin korar kimanin mutum miliyan 45 daga gidajensu.
Yawan marasa aikin yi ya ƙaru a Afirka ta Kudu
Asalin hoton, Getty Images
Ɓangaren samar da aikin yi na Afirka ta Kudu na ƙara shiga cikin matsi bayan yawan marasa aikin yi a ƙasar ya ƙaru zuwa kashi 32.9 a cikin ɗari a watanni uku na farkon shekarar 2025.
Yawan marasa aikin yin ya ƙaru ne daga kashi 31.9 cikin ɗari a watanni uku na ƙarshen shekarar 2024 da ta gabata.
Alƙaluma sun nuna cewa a yanzu mutanen da ba su da aikin yi a ƙasar sun kai miliyan takwas ta dubu ɗari biyu da ashirin da takwas (8.228).
Sai dai idan aka faɗaɗa alƙaluman domin haɗawa da waɗanda suka saduda da neman aiki, yawan marasa aikin yi a ƙasar ya ɗaga ne zuwa sama da kashi 43 cikin ɗari.
Ɓangaren da ya fi fama da hasarar guraben aikin yi shi ne ɓangaren kasuwanci da gine-gine, yayin da aka samu ƙarin guraben ayyukan yi a ɓangaren sufuri da harkar kuɗi.
Tattalin arziƙin Najeriya ya haɓɓaka fiye da yadda ake tsammani - Bankin Duniya
Asalin hoton, TINUBU/FACEBOOK
Bankin Duniya ya ce tattalin arzikin Najeriya haɓɓaka fiye da kowanne lokaci cikin shekara goma da ta gabata, sakamakon wasu muhimman gyare-gyaren da gwamnati ta aiwatar sai dai kuma Bankin Duniyan ya gargadi cewa hauhawar farashin kayayyaki na ci gaba da addabar miliyoyin ƴan ƙasar.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Bankin Duniya ya fitar wa manema labarai, inda ya bayyana cewa ƙarfin tattalin arziƙin Najeriya na cikin gida ya ƙaru da kashi 4.6 cikin 100 a zangon ƙarshe na shekara ta 2024.
Wannan, in ji Bankin Duniya ya kai jimillar ci gaban tattalin arziki na shekara zuwa kashi 3.4 cikin 100 – mafi girma tun shekarar 2014, baya ga farfaɗowar da aka samu daga lokacin annobar korona.
Rahoton ya danganta wannan cigaba ne ga ci gaban da ake samu a ɓangaren man fetur da iskar gas, da kuma ƙaruwar zuba jari da bunƙasar fasahar zamani da harkar kudi.
"Duk da wannan ci gaba, ɓangaren noma ya ci gaba da tafiyar hawainiya, inda ya karu da kashi 1.2 cikin 100 kacal a shekarar 2024," in ji Bankin.
Bankin ya kara da cewa, "Wannan ƙarancin ci gaba ya samo asali ne daga rashin tsaro a yankin tsakiyar ƙasar da aka fi yin noma, da kuma hauhawar farashin kayayyakin noma kamar taki da man fetur."
"Wadannan kalubalen suna da tasiri kai tsaye ga samar da abinci da kuma hauhawar farashin kayan masarufi, wanda ke ƙara matsin rayuwa ga miliyoyin ‘yan Najeriya," in ji rahoton.
Bankin Duniya ya yaba wa gwamnatin shugaban Bola Ahmed Tinubu saboda ɗaukar matakan gyaran tattalin arziki tun bayan hawansa mulki a watan Mayun 2023.
Daga cikin wadannan gyare-gyare har da cire tallafin man fetur da ƙoƙarin farfaɗo da darajar Naira. Sai dai kuma rahoton ya ce waɗannan matakan sun haifar da matsin rayuwa ga al’umma da dama, musamman talakawa.
Trump ya sauka a Saudiyya domin ziyararsa ta farko a Gabas ta Tsakiya
Asalin hoton, Reuters
Shugaban Amurka Donald Trump ya isa ƙasar Saudiyya a ziyararsa ta farko a yankin Gabas ta Tsakiya, inda tuni ya sauka a Riyadh a jirgin Air Force One.
Tuni shugaban na Amurka ya yi zaman farko da Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman, kafin su shiga wani zaman sirri.
Trump zai gana ne da Mohammed bin salman a filin jirgin sama na sarki Khalid da ke Riyadh a kusa da hotunan wasu daga ckin mambobin iyalan sarauta na Saudiyya
Sakataren harkokin waje, Marco Rubio, ma zai kasance a cikin taron.
Hana shigar da kayan agaji Gaza laifin yaƙi ne - UNRWA
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban hukumar kula da Falasɗinawa ta Majalisar Ɗinkin Duniya ya shaida wa BBC cewa hana shigar da kayan jin-ƙai Gaza da Isra'ila ta yi, daidai yake da laifin yaƙi.
Philippe Lazzarini na UNRWA ya ce gwamnatin Isra'ila na amfani da abinci a matsayin makamin yaƙi, sakamakon hana shigar da shi tsawon wata biyu ke nan.
Ya ce mutane sun gaji, suna jin yunwa, "nan da makwa masu zuwa za su fara mutuwa ba wai saboda ruwan bama- bamai kaɗai ba, face don rashin abinci."
Ya koka da yadda duniya ta nuna halin ko-in-kula ga abun da ke faruwa.
Isra'ila dai ba ta ce komai ba kan zargin na Mista Lazzaraini, tana bayyana hukumar ta UNRWA dungurungum a matsayin ta yan Hamas ita ma.
Buɗewa
Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Talata daga nan sashen Hausa na BBC, inza da mu ɗora daga inda muka tsaya a jiya na kawo muku labaran kai-tsaye game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.
Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin karanta wasu labaran da tafka muhawara.