Man City na son Tijjani, Diaz ya ce yana nan darandam a Liverpool

Asalin hoton, Getty Images
Pep Guardiola na son kawo dan wasan AC Milan Tijjani Reijnders zuwa Manchester City, dan wasan gefe na Liverpool Luis Diaz ya yi alkawarin makomarsa a Reds, yayin da Manchester United za ta ci gaba da yin imani da kocinta Ruben Amorim.
Manchester City za ta yi zawarcin dan wasan tsakiyar Netherlands Tijjani Reijnders mai shekara 26 daga AC Milan a bazara, wanda zai yi la'akari da tayin sama da fam miliyan 57 kawai. (Telegraph)
Shugabannin Manchester United ba su da wani shiri na maye gurbin Ruben Amorim a matsayin koci (Talksport)
Dan wasan gefe na Colombia Luis Diaz, mai shekara 28, ya yi alkawarin ci gaba da zama a Liverpool duk da cewa a baya ana alakanta shi da Barcelona. (Express)
Har yanzu Real Madrid ba ta yi wa Liverpool tayin sayen dan wasan baya na kasar Ingila Trent Alexander Arnold da wuri ba, mako guda bayan da ta tambayi kungiyar ta Premier ko dan wasan mai shekaru 26 zai iya buga mata gasar cin kofin duniya na kungiyoyi da za a yi a wata mai zuwa. (Sky Sports)
Liverpool na iya neman maye gurbin Alexander-Arnold da dan wasan bayan Netherlands Jeremie Frimpong, mai shekara 24, wanda farashinsa ya kai (€35-40m). (Sky Germany)
Dan wasan baya na Newcastle Sven Botman yana son ci gaba da zama a kungiyar duk da sha'awar dan wasan na Netherlands, mai shekara 25, daga Paris St-Germain. (The I)
Napoli ta tattauna da wakilan Kevin de Bruyne game da sanya hannu kan yarjejeniyar kyauta idan kwantiraginsa ya kare da Manchester City a bazara. (Sky Switzerland)
Atletico Madrid na shirin tattaunawa da Manchester United kan cinikin dan wasan Brazil Antony, wanda ke zaman aro a Real Betis, yayin da suma Juventus da Villarreal ke zawarcin dan wasan mai shekaru 25. (Football Espana)
Real Madrid na sha'awar sake siyan dan wasan bayan Faransa Theo Hernandez, mai shekara 27, daga AC Milan, shekaru shida bayan ya bar su. (Calciomercato)











