Ta yaya sabbin dokokin zama a Birtaniya za su shafi yan Najeriya?

Firaministan Birtaniya Keir Starmer ya zayyana wasu matakai da za a bi domin tsaurara dokokin shiga da zama a ƙasar, da zimmar rage kwarorowar baƙi masu zuwa zama da karatu da neman aiki.
Daga cikin matakan akwai gwajin Ingilishi ga dukkan masu neman izini shiga ƙasar da kuma tsawaita lokacin da ake ɗauka a ƙasar kafin samun izinin zama na dindindin.
Firaministan yana kuma so a rage ɗaukar ma'aikatan jinya daga ƙasashen ƙetare, matakin da zai taimaaka wajen rage yawan ƴan ƙsashen waje da ake ɗauki aiki a ƙasar ta sahihiyar hanya.
Sai dai bai ce komai ba game da masu shiga ƙasar ta ɓarauniyar hanya, kamar masu shiga ta teku.
Adadin baƙin da suka shiga ƙasar a shekarar 2024 sun kai 728,000 zuwa watan Yunin shekarar.
Hukumomin ƙasar za su fitar da gamsasshen bayani mai ɗauke da sababbin tsauraran matakan, waɗanda za su ƙunshi na mallakar izinin karatu da aiki a Birtaniya.
Sakataren harkokin baƙi na Birtaniya Yvette Cooper ta bayyana wa BBC cewa lokaci ya yi da za su rage ɗaukar ma'aikatan jinya daga ƙasashen waje.
Ta ce wannan matakin zai taimaka wajen rage kusan mutum 50,000 waɗanda ba ƙwararru ba ne sosai da suke shiga ƙasar daga ƙasashen ƙetare a duk shekara.
Firaministan ya ce sababbin matakan za su taimaka wajen "sake mallake bakin iyakokin ƙasarmu."
Idan aka ɗabba sabbin matakan nan da gwamnatin ƙasar za ta ɗauka, ƴan ƙasashenmutane daga ƙasashen Najeriya da Pakistan da Sri Lanka za su fuskanci ƙalubale wajen samun izinin shiga ƙasar Birtaniya domin karatu.
Abin da hakan ke nufi
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Starmer ya ce Birtaniya za ta riƙa neman waɗanda suka fi ƙwarewa ne a duniya wajen ɗaukar aiki, sannan za su bincika me ya sa wani ɓangaren aikin ƙasar ya fi mayar da hanakali kan "neman sauƙi wajen ɗaukar aiki."
Firaministan ya ce sabbin matakan za su fayyace komai da komai game da tsare-tsaren shige da fice a ƙasar - iyali da karatu da aiki.
"Zan tabbatar da matakan nan saboda za su tabbatar da adalci, kuma abin da ya dace ke nan," in ji Starmer a wani taron manema labarai.
Ya ce bai kamata a riƙa mayar da hankali kan neman sauƙi wajen ɗaukar ma'aikata ba, maimakon mayar da hankali kan horar da matasan ƙasar.
Starmer ya ƙara da cewa baƙin da suke shigowa ƙasar a gwamnatin baya sun kai kusan miliyan 1 a shekarar 2023, wanda shi ne adadi mafi yawa.
Ya ce adadin baƙin ya kai adadin mutanen birnin Birmingham baki ɗaya, wanda kuma shi ne birni na biyu mafi girma a Birtaniya.
"Wannan ba ci gaba ba ne, kasada ce. Ba zai yiwu a ce da kuskure hakan ya faru ba, wannan ganganci ne"
Yadda matakan suka shafi ƴan Najeriya
Tun bayan sanarwar ta fako, wadda a ciki aka ambaci Najeriya da Sri Lanka da wasu ƙasashe, sai lamarin ya fara jawo muhawara a tsakanin ƴan ƙasar a ciki da wajenta.
Domin jin irin yadda sauye-sauyen za su shafi ƴan Najeriya, BBC ta tuntuɓi Barista Audu Bulama Bukarti, inda ya ce matakan za su cutar da ƴan ƙasar.
Ya ce, "Akwai waɗanda suka yi shekaru, suna tunanin sun kusa zama ƴan ƙasa, amma yanzu abin ya ƙara tsaro. Waɗanda suke son zuwa aikin kula da masu rauni yanzu ba kowa zai iya zuwa ba. Haka kuma waɗanda suke can ma an ƙara musu kuɗaɗen da suke kashewa kafin zama ƴan kasa, su kuma masu sha'awar shigowa, ƙalubalen sun ƙara yawa."
Lauyan wanda yake zaune a Ingila ya ce ƴan Najeriya sun yi ƙaurin suna, "amma yawancin ƴan kudancin ƙasar ne suka fi aikata haka. Idan sun je karatu sai su tsaya neman aiki. Wasu kuma sai su nemi mafaka ta hanyar cewa su masu neman jinsi ne idan suka koma Najeriya za a cutar da su, mata kuma su ce za a yi wa yaransu kaciya ko kuma mazansu na dukansu da sauransu."
A game da dalilan da suka sa aka kawo waɗannan matakan a yanzu, Bukarti ya ce siyasa ce kawai.
Ya ce "an yi zaɓen ƙananan hukumomi, sai jam'iyyar Reform mai tsanar baƙi ta bayar da mamaki, inda ta ƙwace kansiloli sama da 1000 daga jam'iyyar Conservative, sannan ta karɓi kujeru kusan 400 daga jam'iyyar Labour mai mulki."
Lauyan ya ce zaɓen ne ya sa sauran manyan jam'iyyu, "suka fara tunanin ɗaukar mataki ganin cewa mutane sun fara goyon bayan jam'iyya mai tsanar baƙi. Sannan masu ƙiyayyya ga baƙi suna ikirarin cewa kwararar baƙi ne ke jawo yawa aikata laifuka da dogon layi a asibitoci da sauransu, alhali sakacin ƴan siyasa ne kawai da gazawarsu."
Manyan sauye-sauyen
Barista Audu Bulama Bukarti ya ce akwai manyan sauye-sauye guda biyar da za a fuskanta.
- Ƙara tsawon lokacin da ake buƙata kafin mutum ya zama ɗan ƙasa daga shekara biyar zuwa goma.
- Canja mafi ƙarancin karatun da ake buƙata domin aikin kula da tsofaffi da masu rauni zuwa matakin digiri.
- Rage lokacin zama bayan karatu daga shekara biyu zuwa wata 18.
- Dakatar da ɗaukar masu aikin kula da tsofaffi - sai dai aka cigaba da amfani da na cikin ƙasar da kuma ƴan ƙasar masu neman aiki.
- Tsaurara gwajin ƙwarewar Ingilishi ga baƙi.











