Labaran wasannin BBC Hausa kai-tsaye daga 26/07 zuwa 01/08/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 26 ga watan Yuli zuwa 1 ga watan Agusta 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Abdu, Umar Mika'il

  1. Sancho

    Asalin hoton, Getty Images

    Burnley na zawarcin mai tsaron gidan Ingila Sam Johnstone, mai shekara 32, da ke taka leda a Wolves, a wani mataki na neman wanda zai maye gurbin mai tsaron gidanta da zai bar ƙungiyar James Trafford (Sun)

    Newcastle da Tottenham na sha'awar ɗaukar Gabriel Jesus, mai shekara 28, daga Arsenal amma ɗanwasan gaban Brazil ɗin na samun tayi daga wasu ƙungiyoyin da suka haɗa da Barcelona da AC Milan da kuma Inter Milan. (Caught Offside)

    West Ham na bibiyar mai tsaron gidan Sheffield United kuma ɗan Ingila mai shekara 25, Michael Cooper.(Sun)

    Toulouse ta shiga cinikin ɗanwasan Brighton mai shekara 19 kuma ɗan ƙasar Mali, Malick Yalcouye. (Fabrizio Romano)

    Fulham ta gabatar da tayi kan ɗanwasan tsakiyar Chelsea da Ingila mai shekara 25, Kiernan Dewsbury-Hall. (GiveMeSport)

    Manchester United da Newcastle da kuma Tottenham za su fafata wajen zawarcin ɗanwasan gaban Serbia mai taka leda a Al-Hilal, Aleksandar Mitrovic, mai shekara 30. (Caught Offside)

  2. Ƴanwasan da Real Madrid ta saya masu tsada a tarihi

    Real Madrid

    Asalin hoton, Getty Images

    Cikin watan Agusta za a fara gasar La Liga kakar 2025/26, bayan da Barcelona ta lashe kofin kakar da aka kammala, Real Madrid ta yi ta biyu a teburi da Atletico Madrid ta uku.

    Hakan ya sa Real ta yi cefane don ganin ta taka rawar gani a kakar bana, inda ta ɗauki Dean Huijsen da Trent Alexander-Arnold da Franco Mastantuono da kuma Álvaro Carreras daga Benfica.

    Har yanzu Eden Hazard ne ɗan wasan da Real Madrid ta saya mafi tsada a tarihi.

    Tsohon ɗan wasan tawagar Belgium ya koma buga La Liga daga Chelsea a 2019 kan €121m.

    Jude Bellingham ne na biyu da ta saya mai tsada daga Borussia Dortmund a 2023 kan €113m.

    Ga jerin ƴanwasan biyar da Real Madrid ta saya mafi tsada a tarihi:

    • Eden Hazard – €121m
    • Jude Bellingham – €113m
    • Gareth Bale – €101m
    • Cristiano Ronaldo – €94m
    • Aurélien Tchouaméni – €80m
  3. Arsenal za ta buga wasan sada zumunta da Tottenham

    Arsenal

    Asalin hoton, Getty Images

    Ranar Alhamis Arsenal za ta buga wasan sada zumunta da Tottenham a Hong Kong a shirin da take na fuskantar kakar bana da za a fara a cikin watan Agusta.

    Shi ne wasa na uku da za ta buga a Nahiyar Asia, bayan da ta fara doke AC Milan 1-0 da cin Newcastle United 3-2 ranar Lahadi.

    Kawo yanzu Arsenal ta kashe kusan kimanin fam miliyan 204, wajen sayen sabbin yan wasa har da Victor Gyokeres daga Sporting da zai yi kaka biyar a kungiyar Arewacin Landan.

    Sauran da Gunners ta ɗauka har da Martin Zubimendi da Kepa Arrizabalaga da Christian Norgaard da Noni Madueke da kuma Cristhian Mosquera.

  4. Gossip

    Asalin hoton, Getty Images

    Chelsea na nazarin rage kudin Raheem Sterling mai shekara 30, domin bada damar tafiyar sa Fulham. (Football Insider)

    West Ham na duba yiwuwar saye ɗan wasan Werder Bremen, Romano Schmid, wanda aka kiyasta kuɗinsa kan £13m. Aston Villa da Fulham na sa ido kan ɗan wasan Austriamai shekara 25 da ke buga tsakiya. (Guardian)

    West Ham da Benfica na shirin gabatar da tayi kan ɗan wasan Cagliari mai shekara 24 daga Italiya, Roberto Piccoli, wanda aka yiwa kuɗi £26m. (Calciomercato - in Italian)

    Leeds na shirin biyan £28m kan ɗan wasan Feyenoord, Igor Paixao mai shekara 26, amma tana fuskantar kalubale daga Marseille da Roma. (Sky Sports)

  5. Usyk zai dambata da Joseph Parker domin kare kambinsa

    Usyk

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar damben boksin ta duniya WBO, ta umarci Oleksandr Usyk ya yi shirin fuskantar Joseph Parker a wasan cin kambun duniya ajin babban nauyi.

    A makon da ya gabata Usyk ya yi wa Daniel Dubois bugun kwaf daya a turmi na biyar ya zama gagaraba dau karo na biyu a wasan da suka yi a Wembley.

    Nasara ta 24 da dan damben Ukraine ya yi mai shekara 38, wanda ya sake karbr kambun IBF, wanda dama yana da na WBA da WBC da na WBO.

    Ana kuma sa ran nan gaba Usyk zai iya dambatawa da ko dai Derek Chisora ko Tyson Fury ko Anthony Joshua ko kuma Parker.

  6. Gossip

    Asalin hoton, Getty Images

    Benfica ta matsa ƙaimi kan Joao Felix daga Chelsea, inda matashin mai shekara 25 daga Portugal ke fatan komawa ƙungiyarsa ta yaranta. (Florian Plettenberg)

    Fulham ta yi nisa a tattaunawar sake saye ɗan wasan Arsenal mai shekara 25, Reiss Nelson, ko a matsayin aro ko yarjejeniya ta dindindin. (Athletic - subscription required)

    Everton na tattaunawa da Lyon kan saye ɗan wasan Belgium mai shekara 20, Malick Fofana. (Fabrizio Romano)

    Manchester United da Burnley sun bi sahun Brentford da Southampton da Borussia Dortmund a fafutikar saye ɗan wasan Metz mai shekara 18 daga Senegal, Idrissa Gueye. (Sun)

  7. Fifa ta buɗe ofis a Morocco don bunkasa ƙwallon kafar mata

    Infantino

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban hukumar ƙwallon kafa ta duniya, Fifa Gianni Infantino ya buɗe katafaren ofis a karshen mako a Morocco, domin bunkasa ƙwallon kafar matan Afirka

    An buɗe ofis din ne a kusa da makarantan koyon tamaula ta Mohammed VI Football Academy dake birnin Rabat a Morocco.

    Bayan aikin da za ake gudanarwa a ofis, za ake tsara hanyoyin bunkasa ƙwallon kafar mata tun daga tushe da kuma taimaka musu wajen samar da kayayyakin atisaye na zamana da gine-gine.

    Morocco tana daga cikin kasashen da za suyi haɗakar shirya gasar cin kofin duniya na maza da ya haɗa da Sifaniya da kuma Portugal.

  8. Gibbs-White zai ci gaba da taka leda a Nottingham Forest

    White

    Asalin hoton, Getty Images

    Ɗan wasan Nottingham Forest, Morgan Gibbs-White ya saka hannu kan kwantiragin ci gaba da taka leda a ƙungiyar zuwa karshen kakar 2028 - hakan ya kawo karshen cewar zai koma Tottenham.

    Wasu rahotanni daga kafafen yaɗa labaran Burtaniya sun ce Tottenham ta yi niyyar sayen ƙunshin yarjejeniyar ɗan wasan da ta rage a City Ground tun farko.

    Forest ta kare a mataki na bakwai a teburin Premier League a kakar da ta wuce, hakan ya sa za ta buga wasannin neman gurbin shiga UEFA Conference League.

  9. Arsenal ta kashe fam miliyan 204 wajen sayen sabbin ƴanwasa

    Arsenal

    Asalin hoton, Getty Images

    Arsenal ta kashe kusan kimanin fam miliyan 204, wajen sayen sabbin ƴan wasa don tunkarar kakar bana da za a fara a cikin watan Agusta.

    A karshen mako gunners ta kammala sayen Gyokeres daga Sporting kan fam miliyan 64.

    Kuma tuni ɗan ƙwallon mai shekarar 27 ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka biyar a ƙungiyar ta Emirates.

    Sauran da Arsenal ta ɗauka har da Martin Zubimendi da Kepa Arrizabalaga da Christian Norgaard da Noni Madueke da kuma Cristhian Mosquera.

  10. Arsenal

    Asalin hoton, Getty Images

    Manchester United da Manchester City kowannesu na zawarcin ɗan wasan Paris St-Germain mai shekara 26 Gianluigi Donnarumma, yayinda ƙungiyarsa ta Lig 1 ke fatan maye gurbin mai tsaron ragar da Lucas Chevalier, mai shekara 23, idan ya zaɓi sauya sheka. (L'Equipe - in French)

    Galatasaray ita ma na shirin gabatar da tayinta kan Donnarumma, wanda ke shirin shiga wa'adin karshe na yarjejeniyarsa a Paris. (Footmercato - in French)

    Arsenal na fatan cimma yarjejeniya ta fam miliyan 60 da ɗan wasan, Crystal Palace Eberechi Eze, mai shekara 27. (Independent)

    Everton na tattaunawa da Bayern Munich kan kwantiraginsa fam miliyan 7.8 da dan wasan Moroko mai shekara 19, Adam Aznou. (Athletic - subscription required)

  11. Bayern Munich ta kusan kammala sayen Diaz daga Liverpool

    Diaz

    Asalin hoton, Getty Images

    Liverpool ta kusan sallama tayin fam miliyan 75 da Bayern Munich ta yi, domin a sayar mata da Luis Diaz.

    Wannan shi ne tayi na biyu da Bayern ta yi, bayan da Liverpool ba ta amince da tayin fam miliyan 59 da tun farko ƙungiyar dake buga Bundesliga ta yi ba.

    Kawo yanzu Liverpool tana shirye-shiryen tunkarar kakar bana da yin atisaye a nahiyar Asia, kuma ta je Tokyo da Diaz ranar Lahadi.

    To sai dai kuma ƙungiyar Anfield ba ta sa Diaz ba a karawar da ta yi nasara 4-2 a kan AC Milan a ranar Asabar, hakan ya sa ake ta cece-kucen cewar Diaz na daf da barin Liverpool.

    Liverpool ta yi cefanen da ta kara karfin ƙungiyar, ta ɗauki Florian Wirtz - wanda ya buga karawar ranar Asabar da kuma Hugo Ekitike.

    Haka kuma ƙungiyar Mersyside ta ɗauki Jeremie Frimpong da Milos Kerkez da Giorgi Mamardashvili, dukkansu sun yi wasan na sada zumunta ranar Lahadi.

  12. Arsenal ta doke Newcastle a wasan sada zumunta a Asia

    Arsenal

    Asalin hoton, Reuters

    Arsenal ta yi nasara a kan Newcastle United da cin 3-2 a wasan sada zumunat da suka buga a nahiyar Asia a shirin tun kakar kakar bana da za a fara a cikin watan Agusta.

    Newcastle ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Anthony Elanga, daga baya Arsenal ta farke ta kara na biyu ta hannun Mikel Merino da kuma Alex Murphy da ya ci gida.

    Daga baya Jacob Murphy ya farke wa Newcastle, sai Martin Odegaard na Arsenal ya zura na uku a raga a bugun fenariti, bayan da aka yi wa matashi mai shekara 15, Max Dowman keta.

  13. Rashford ya buga wa Barcelona wasa a karon farko

    Rashford

    Asalin hoton, Getty Images

    Marcus Rashford ya buga wa Barcelona wasa a karon farko a karawar da ta doke Vissel Kobe 3-1 a Japan a wasan shirin tunkarar kakar da za a fara a cikin watan Agusta.

    Mai shekara 27, wanda ya koma Sifaniya da taka leda daga Manchester United kan yarjejeniyar buga wasannin aro zuwa karshen kakar bana, ya shiga karawar bayan da aka koma zagaye na biyu daga baya aka sauya shi a minti na 78.

    Rashford ya nemi raga, amma aka tare ƙwallo a ƙungiyar Hansi Flick, wadda ta ci ƙwallayenta ta hannun Eric Garcia da Roony Bardghji da matashi Pedro Fernandez.

    Bardghji, wanda Barca ta ɗauaka a bana daga Copenhagen, shi ne ya ci na biyu, bayan da Taisei Miyashiro ya farke ƙwallon da aka fara cin Kobe.

    An gabatar da fitatcen ɗan wasan Sifaniya, Lamine Yamal, mai shekara 18 da riga mai lamba 10 tun kan a take leda- lamba ce da wasu daga manyan tsoffin ƴan wasan Barcelona da suka saka ciki har da Diego Maradona da kuma Lionel Messi.

  14. Najeriya ta lashe kofin Afirka na mata karo na 10

    Ƴan wasan Super Falcons na Najeriya lokacin da suka ɗaga kofi bayan lashe gasar ƙwallon ƙafa ta mata ta 2024 a Morocco

    Asalin hoton, X/CAFonline

    Bayanan hoto, Ƴan wasan Super Falcons na Najeriya lokacin da suka ɗaga kofi bayan lashe gasar ƙwallon ƙafa ta mata ta 2024 a Morocco

    FT: Morocco 2 - 3 Najeriya

    Najeriya ta lashe kofin ƙwallon Afirka na mata karo na 10 bayan ta doke mai masaukin baƙi Morocco a wasan ƙarshe da aka buga na gasar ta shekara ta 2024.

    Wasan ya tashi ne Najeriya tana da ci uku yayin da Morocco ke da biyu.

    Morocco ce ta fara shiga gaba a wasan inda ta zura ƙwallo biyu tun kafin a je hutun rabin lokaci ta ƙafar ƴan wasanta Ghizlane Chebbak da kuma Sanaa Mssoudy.

    Sai dai bayan komawa daga hutun rabin lokaci Najeriya ta farke ƙwallon farko ta ƙafar ƴar wasa Esther Okoronkwo kafin daga bisani Folashade Ijamilusi ta zura ƙwallo ta biyu.

    Jennifer Echegini ce ta shafa fatiha da zura ƙwallo ta uku a minti na 88.

  15. Arsenal ta kammala ɗaukar Viktor Gyokeres daga Sporting

    Viktor Gyokeres lokacin da ya sanya hannu kan kwantaragin komawa Arsenal ranar 26 ga watan Yulin 2025

    Asalin hoton, Arsenal

    Bayanan hoto, Viktor Gyokeres lokacin da ya sanya hannu kan kwantaragin komawa Arsenal ranar 26 ga watan Yulin 2025

    Ƙungiyar ƙwallaon ƙafa ta Arsenal ta kammala ɗaukar ɗan wasan Sweden Viktor Gyokeres daga Sporting da ke Portugal kan kuɗi fam miliyan 63 (Yuro miliyan 73).

    Ɗan wasan mai shekara 27 a duniya ya sanya hannu kan kwantaragin shekara biyar a ƙungiyar ta Arsenal bayan shafe dogon lokaci ana turka-turka tsakanin ƙungiyoyin biyu game da wasu kudaɗe.

    Yanzu jimillar kuɗin sun kama yuro miliyan 63 na sayen ɗan wasan sai kuma yuro miliyan 10 na tsarabe-tsarabe.

    Hakan na nufin ya zuwa yanzu Arsenal ta kashe kuɗi fam miliyan 240 wajen sayen ƴan wasa a wannan kasuwar musaya da aka buɗe.

    Ƴan wasan da ƙungiyar ta saya sun haɗa da Martin Zubimendi da Kepa Arrizabalaga da Christian Norgard da Noni Madueke da kuma Christhian Mosquera.

    “Viktor na da nagarta sosai. Ɗan wasa ne mai hanzari da nuna kuzari a gaba, yana da ƙwarewa wajen jefa ƙwallo a raga kamar yadda alƙaluma suka nuna a ƙungiya da kuma ƙasarsa,” in ji kocin Arsenal Mikel Arteta.

    Arsenal ta mayar da hankalinta kan Viktor Gyokeres ne bayan gaza samun ɗan wasan RB Leipzig Benjamin Sesko.

    Wannan sanya hannu da Gyokeres ya yi ta kawo ƙarshen taƙaddamar da aka daɗe ana yi kan makomar ɗan wasan, bayan da aka alaƙanta shi da Manchester United a baya.

  16. Tinubu ya faɗa wa ƴanmatan Najeriya 'ku ciyo mana kofi'

    ...

    Asalin hoton, Backpage Pix

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya nemi tawagar ƙwallon ƙafa ta matan ƙasar da ta kai masa kofin gasar ƙasashen Afirka yayin da suke shirin buga wasan ƙarshe a yau Asabar.

    Najeriya za ta kara da mai msaukin baƙi Morocco a birnin Rabat domin neman lashe kofin a karo na 10 jimilla, yayin da Moroccon ke neman kofin a karon farko.

    "A madadin ƙasar nan baki ɗaya, muna goyon bayanku tare da yin addu'ar ku yi nasara a daren yau, yayin da kuke neman kafa tarihin cin kofi na 10," a cewar Tinubu cikin sanarwar da fadar shugaban ta fitar.

  17. Liverpool za ta gina butumbutumin Diogo Jota

    Diogo Jota

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Diogo Jota

    Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Liverpool ta sanar da cewa za ta ƙirƙiri wani abu na dindindin da za a riƙa tunawa da tsohon ɗan wasanta Diogo Jota wanda ya rasu sanadiyyar hatsarin mota a farkon wannan wata.

    Ƙungiyar wadda ta lashe gasar Premier a kakar da ta gabata ta ce za ta sarrafa abubuwan da masu alhini suka ajiye a jikin filin wasanta na Anfield domin samar da wani butumbutumi na tunawa da marigayin.

    Tuni dai ƙungiyar ta sanar da daina amfani da riga mai lamba 20 domin karrama Jota.

    Diogo Jota mai shekara 28 a duniya, wanda kuma ɗan wasan Portugal ne, ya rasu ne a kan hanyarsa ta komawa ƙungiyarsa a Birtaniya, kwana 11 bayan ɗaura aurensa da masoyiyarsa Rute Cardoso.

    Ya ci ƙwallo 65 a wasanni 182 da ya buga wa Liverpool, inda ya taimaka wa ƙungiyar lashe kofin ƙalubale (FA) a shekarar 2022 da kuma kofin Premier a kakar wasa da ta gabata.

  18. An dakatar da Messi a gasar MLS

    Lionel Messi

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Lionel Messi

    Hankalin Messi ya yi “matuƙar tashi” bayan da aka dakatar da shi tare da takwaransa na ƙungiyar Inter Miami, Jordi Alba daga buga wasa ɗaya bisa laifin ƙin buga wasan taurarin gasar ƙwallon ƙwafa ta Amurka – MLS All-Stars, a cikin mako.

    Ƴan wasan biyu sun gaza halartar wasan da aka yi ranar Laraba a birnin Austin na jihar Texas, inda tawagar MLS All-Stars ta yi nasara kan tawagar taurarin gasar ƙungiyoyin Mexico, wato Liga MX.

    “A tsarin doka duk ɗan wasan da ya ƙi harlartar wasan taurarin gasar ba tare da samun sahhalewa ba daga farko, to bai cancanci buga wasan ƙungiyarsa na gaba ba,” kamar yadda masu gudanar da gasar ƙungiyoyin Amurka ta MLS suka sanar a ranar Juma’a.

    Saboda haka a yanzu Messi da Jordi Alba ba za su buga karawar da Inter Miami za ta yi da FC Cincinnati ba a gida, ranar Asabar mai zuwa.

    A wani martani da ya mayar kan dakatarwar, mamallakin ƙungiyar Inter Miami, Jorge Mas ya ce hankalin Messi ya tashi game da dakatarwar.

    “Hankalinsa ya tashi, ya tashi sosai. Ina fatan hakan ba zai shafe shi ba na tsawon lokaci”.

    MLS dai ta ce matakin da ta ɗauka abu ne mai “matukar wahala”.

  19. Wasan ƙarshe na Wafcon 2024: Morocco za ta kara da Najeriya

    Ƴar wasan gaba da Morocco Sakina Ouzraoui da ta Najeriya Rasheedat Ajibade dukkaninsu sun ci ƙwallaye a wasan kusa da na ƙarshe

    Asalin hoton, Getty Images/Backpage Pix

    Najeriya za ta nemi ƙara yawan kofin nahiyar Afirka na ƙwallon mata da ta lashe zuwa 10 a karawar da za ta yi yau da Morocco mai masaukin baƙin gasar ta 2024.

    Har yanzu babu ɗaya daga cikin tawagogin biyu da ta yi rashin nasara tun daga fara gasar ta wannan karo, kuma an zura ƙwallo ɗaya ce tal a ragar Najeriya daga farko zuwa yanzu.

    Za a yi karawar ƙarshen ne a filin wasa na Olympic Stadium mai cin ƴan kallo 21,000 da ke birnin Rabat.

    A shekara ta 2022, Morocco ta zo ta biyu a gasar a wannan filin bayan ta sha kashi hannun Afirka ta kudu.

    Idan har tawagar mata ta Morocco, wato Atlas Lionesses suka ci kofin a karawar, wannan zai zamo tamkar kwalliya ta fara biyan kuɗin sabulu a irin kuɗin da ƙasar ke narkarwa domin bunƙasa ƙwallon mata a ƙasar.

    Ita kuwa Najeriya, wadda take ta ɗaya a jerin ƙasashen da suka fi iya ƙwallon mata a a Afirka, ta zura ƙwallon da ta ba ta nasara ne a gab da tashi wasa a karawarta da Afirka ta Kudu.

  20. Barka da zuwa!

    Barka da zuwa shafinmu na labaran wasanni kai-tsaye na BBC Hausa daga ranar 26 ga watan Yuli zuwa 1 ga watan Agustan 2025.