Labaran wasannin BBC Hausa kai-tsaye daga 26/07 zuwa 01/08/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni daga Asabar 26 ga watan Yuli zuwa 1 ga watan Agusta 2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Muhammad Abdu, Umar Mika'il

  1. Diaz ya kammala komawa Bayern Munich daga Liverpool

    Diaz

    Asalin hoton, ge

    Luis Diaz ya kammala komawa Bayern Munich daga Liverpool kan fam miliyan 65.5.

    Ɗan ƙwallon tawagar Colombia ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka huɗu da ƙungiyar Jamus, hakan ya kawo karshen shekara uku da rabi da ya yi a Liverpool.

    Mai shekara 28 ya bar sansanin Liverpool a nahiyar Asia lokacin da za ta kara da AC Milan ranar Asabar, saboda jita-jitar da ta yi yawa kan makomar ɗan wasan a Anfield.

    Tun farko Liverpool ba ta amince da tayin fam miliyan 58.6 da Bayern ta fara yi ba, hakan ya sa aka kara kuɗin sayen Diaz daga baya ƙungiyar Anfield ta amince ta kuma yadda yaje Jamus aka auna koshin lafiyarsa.

    Diaz ya koma Liverpool daga Porto kan fam miliyan 37 a Janairun 2022, ya ci ƙwallo 41 a wasa 148 a ƙungiyar Anfield.

    Ya lashe FA Cup da League Cup a kakarsa ta farko a Liverpool, yana cikin ƴan wasan da suka yi rashin nasara a hannun Real Madrid a Champions League a 2022.

    Diaz ya taka rawar gani a kakar da ta wuce a babbar gasar tamaula ta Ingila, wanda ya ci ƙwallo 17 da ɗaukar kofin Premier League.

    Tafiyar da Diaz ya yi, Liverpool ta sayar da ƴan wasa kan fam miliyan 115 a bana.

    Ta kuma sayi ƴanwasa kan fam miliyan 270 da ya haɗa da Florian Wirtz da Hugo Ekitike da Jeremie Frimpong da kuma Milos Kerkez.

    Har yanzu Liverpool na son yin zawarcin ɗan ƙwallon Newcastle, Alexander Isak, wanda bai bi ƙungiyarsa wasannin atisaye da take yi a nahiyar Asia ba.

  2. Sunderland ta ɗauko ƴanƙwallo bakwai a kakar bana

    Granit Xhaka

    Asalin hoton, Sunderland/Facebook

    Granit Xhaka ya zaman ɗan ƙwallo na bakwai da ƙungiyar Sunderland ta ɗauko a kaka wasa ta bana da za a soma.

    Ya Bayer Leverkusen inda ya lashe kofin gasar Bundesliga a kakar wasa ta 2023 zuwa 2024.

    Ga jerin ƴanƙwallon:

    • Enzo le Fee - daga Roma - £19.3m
    • Habib Diarra - daga Strasbourg - £30m
    • Noah Sadiki - daga Royale Union Saint-Gilloise - £15m
    • Reinildo Mandava - daga Atletico Madrid
    • Chemsdine Talbi - daga Club Brugge - £18m
    • Simon Adingra - daga Brighton - £18m
    • Granit Xhaka - daga Bayer Leverkusen - £13m
  3. Frank na murna da har yanzu Son yake Tottenham

    Son

    Asalin hoton, Getty Images

    Sabon kociyan Tottenham, Thomas Frank yana cike da murna da har yanzu ƙyaftin Son Heung-Min yake tare da ƙungiyar.

    Ana ta alakanta ɗan ƙwallon tawagar Koriya ta Kudu da cewar zai koma Los Angeles da taka leda da cewar har an taya shi sama da fam miliyan 20

    Son, mai shekara 33 ya je Tottenham tun 2015, yana da sauran ƙunshin yarjejeniya zuwa karshen kakae 2026.

    Ya ci ƙwallo 11 da bayar da 12 a ka zura a bara a wasa 46 a kakar da ta wuce da Tottenham ta lashe Europa League, bayan cin Manchester United.

    Kawo yanzu Son ya ci ƙwallo 173 da bayar da 101 aka zura a raga a Tottenham tun bayan da ya koma ƙungiyar daga Bayern Leverkusen a 2015.

    Tottenham za ta fafata da Arsenal a Hong Kong a wasan hamayya na ƙungiyoyin Arewacin Landan da za su fara a bana a wajen Burtaniya.

  4. Ɗan wasan Chelsea Joao Felix ya koma Al-Nassr

    Felix

    Asalin hoton, Getty Images

    Chelsea ta tabbatar da cewar ɗan ƙwallon tawagar Portugal, Joao Felix ya kammala komawa Al-Nassr mai buga babbar gasar tamaula ta Saudiyya kan yarjejeniyar kaka biyu..

    Sai dai ƙungiyoyin biyu ba su fayyace kuɗin cinikin ɗan wasan ba, amma Sky Sports ta ce cinikin ya kai kusan fam miliyan 58.17 har da tsarabe-tsarabe.

    Felix ya koma Atletico Madrid daga Benfica a 2019 lokacin yana da shekara 19 da haihuwa daga nan ya je Chelsea buga wasannin aro a 2022-23 kaka ɗaya tsakani ya je ya buga wasannin aro a Barcelona.

    Daga nan Chelsea ta mallake shi a Agustan 2024 daga nan wata shida tsakani Chelsea ta bayar da aronsa AC Milan, yanzu ta sayar da shi Al-Hilal ta Saudiyya.

    Felix zai buga wasa tare da Cristiano Ronaldo a Al-Nassr.

    Al-Nassr za ta fuskanci Al-Ittihad a Saudi Super Cup zagayen daf da karshe ranar 19 ga watan Agusta.

  5. Ta ina Jack Grealish ya ci karo da cikas?

    Grealish

    Asalin hoton, Getty Images

    Jack Grealish ya koma taka leda a Manchester City kan fam miliyan 100 a matakin mafi tsada da aka saya a Burtaniya a 2021.

    Inda ɗan wasan tawagar Ingila ya nuna kansa shi ne lokacin da ƙungiyar Etihad ta lashe kofi uku a 2023, ya kuma taka rawar gani a kakar.

    A kaka ɗaya tsakani sai ya yi ta fama da jinya, hakan ya sa Grealish ya dunga zama a benci da ta an fara wasa da shi sau 10 a Premier League, wanda ya ci ƙwallo uku ya bayar da ɗaya aka zura a raga.

    A kakar da ta wuce ya buga wasa bakwai da cin ƙwallo ɗaya da bayar da ɗaya aka zura a raga.

    Mai shekara 29 bai buga wasan karshe ba da City ta yi da Fulham a Premier League, bai kuma bi ƙungiyar ba a fafatawar da ta yi a Fifa Club World Cup da aka yi a Amurka.

  6. Za a fara wasan hamayya a bana a Asia tsakanin Arsenal da Tottenham

    Tokyo

    Asalin hoton, BBC Sport

    Wannan shi ne filin wasa na Kai Tak Stadium a Hong Kong, inda za a yi wasan hamayya na ƙungiyoyin Arewacin Landan tsakanin Arsenal da Tottenham.

    A wasan ne ake sa ran sabon ɗan wasan da Gunners ta ɗauka a bana, Viktor Gyokeres zai fara taka mata leda.

  7. Barau FC za ta fara wasan Premier da Enyimba a Kano

    Barau

    Asalin hoton, Barau FC

    Ƙungiyar ƙwallon kafa ta Barau FC za ta fara karawa da Enyimba a wasan makon farko a Premier League ta Najeriya a kakar bana a cikin watan Agusta a jihar Kano, kamar yadda aka fitar da jaddawali.

    Barau FC ta samu wannan matakin ne, bayan da ta yi ta biyu a rukunin Arewacin Nigeria da ta kara tsakani ƙungiya huɗun da suka yi fafatawar cike gurbi daga gasa mai daraja ta biyu wato NNL.

    Domin ganin Barau FC ta taka rawar gani tuni ta ɗauki Ladan Bosso, wanda zai ja ragamar kociyoyin da ya tarar daga ciki har da Rabiu Tata.

    Ƙungiyar mai cin gashin kai na fatan ta wakilci Najeriya a gasar ƙwallon kafar zakarun Afirka a baɗi a kakarta ta farko.

    Ita kuwa mai rike da kofin Remo Stars za ta fafata da Rivers United, shi ne wasan da za a fara ranar 22 ga watan Agusta, mako ɗaya tsakani a buga saura karawa tara daga ciki Kano Pillars za ta ziyarci Abia Warriors.

    Ƙungiya 20 ce za ta kece raini, kuma kowacce za ta buga wasa 38 - 19 a gida da 19 a waje, kenan duk mako za a yi fafatawa 10.

    Haka kuma an tsara cewar jihar da take da ƙungiiya biyu a gasar, duk mako ɗaya na gida ɗayar kuma za ta je karawar waje, misali Kano Pillars da Barau FC daga jihar Kano da Abia Warriors da Enyimba daga jihar Abia.

    Jadawalin makon farko a Premier ta Najeriya:

    • Abia Warriors vs Kano Pillars
    • Wikki Tourists vs Plateau United
    • Katsina United vs Warri Wolves
    • Kwara United vs Ikorodu City
    • El-Kanemi Warriors vs Bendel Insurance
    • Shooting Stars vs Bayelsa United
    • Niger Tornadoes vs Nasarawa United
    • Barau FC da Enyimba FC
    • Kun Khalifat FC da Rangers
    • Remo da Rivers United

    Sabbin kungiya huɗun da za ta buga Premier League a bana ta haɗa da Kun Khalifat da Warri Wolves da Wikki Tourists da kuma Barau FC.

  8. Diaz yana Jamus domin kammala komawa Bayern Munich daga Liverpool

    Diaz

    Asalin hoton, Getty Images

    Ranar Lahadi mun kawo muku labarin cewar Liverpool ta amince da tayin fam miliyan 65 daga Bayern Munich, domin ta sayar da Luis Diaz.

    Liverpool, wadda ta kashe sama da fam miliyan 250 kawo yanzu a bana, ta yadda za ta sayar da ɗan wasan tawagar Colombia, domin ya koma buga babbar gasar tamaula ta Jamus.

  9. Jerin ƴanwasan da aka saya a Premier League a bana kawo yanzu

    Arsenal

    Asalin hoton, Getty Images

    Arsenal

    • Kepa Arrizabalaga - from Chelsea - £5m
    • Martin Zubimendi - from Real Sociedad - £60m
    • Christian Norgaard - from Brentford - £10m (£5m)
    • Noni Madueke - from Chelsea - £48.5m
    • Cristhian Mosquera - from Valencia - £13m
    • Viktor Gyokeres - from Sporting - £55m (£9m)

    Aston Villa

    • Yasin Ozcan - from Kasimpasa - £5.9m (£6.7m)
    • Zepiqueno Redmond - from Feyenoord - Free
    • Marco Bizot - from Brest - Undisclosed

    Bournemouth

    • Adrien Truffert - from Rennes - £11.4m (£14.4m)
    • Djordje Petrovic - from Chelsea - £25m

    Brentford

    • Michael Kayode - from Fiorentina - £14.8m
    • Caoimhin Kelleher - from Liverpool - £12.5m (£18m)
    • Romelle Donovan - from Birmingham City - £3m
    • Antoni Milambo - from Feyenoord - Undisclosed
    • Jordan Henderson - from Ajax - Free

    Brighton

    • Charalampos Kostoulas - from Olympiakos - £29.8m (£31.5m)
    • Diego Coppola - from Hellas Verona - £8.5m
    • Olivier Boscagli - from PSV Eindhoven - Free
    • Maxim de Cuyper - from Club Brugge - Undisclosed

    Burnley

    • Bashir Humphreys - from Chelsea - £12m (£14.7m)
    • Marcus Edwards - from Sporting - £8.5m
    • Jaidon Anthony - from Bournemouth - £7.5m
    • Zian Flemming - from Millwall - £7m
    • Max Weiss - from Karlsruher - £4.3m
    • Quilindschy Hartman - from Feyenoord - Undisclosed
    • Axel Tuanzebe - from Ipswich - Free
    • Loum Tchaouna - from Lazio - Undisclosed
    • Kyle Walker - from Manchester City - £5m
    • Jacob Bruun Larsen - from Stuttgart - Undisclosed

    Chelsea

    • Liam Delap - from Ipswich - £30m
    • Estevao Willian - from Palmeiras - £29m (£48.5m)
    • Dario Essugo - from Sporting - £18.5
    • Mamadou Sarr - from Strasbourg - £12m
    • Kendry Paez - from Independiente del Valle - £8.3m (£16.6m)
    • Joao Pedro - from Brighton - £60m
    • Jamie Gittens - from Borussia Dortmund - £48.5m

    Crystal Palace

    • Walter Benitez - from PSV Eindhoven - Free
    • Borna Sosa - from Ajax - Undisclosed

    Everton

    • Charly Alcaraz - from Flamengo - £12.6m (£15.2m)
    • Thierno Barry - from Villarreal - £27m
    • Mark Travers - from Bournemouth - Undisclosed

    Fulham

    • Benjamin Lecomte - from Montpellier - Reported £500k

    Leeds

    • Jaka Bijol - from Udinese - £15m
    • Lukas Nmecha - from Wolfsburg - Free
    • Sebastiaan Bornauw - from Wolfsburg - £5.1m
    • Gabriel Gudmundsson - from Lille - £10m
    • Sean Longstaff - from Newcastle - £12m
    • Anton Stach - from Hoffenheim - £17m

    Liverpool

    • Florian Wirtz - from Bayer Leverkusen - £100m (£116m)
    • Jeremie Frimpong - from Bayer Leverkusen - £29.5m
    • Armin Pecsi - from Puskas Akademia - £1.5m
    • Milos Kerkez - from Bournemouth - £40m
    • Hugo Ekitike -from Eintracht Frankfurt £69m (£79m)

    Manchester City

    • Tijjani Reijnders - from AC Milan - £46.3m (£60m)
    • Rayan Ait-Nouri - from Wolves - £31m (£36.3m)
    • Rayan Cherki - from Lyon - £30.5m (£35.6m)
    • Marcus Bettinelli - from Chelsea - Nominal
    • Sverre Nypan - from Rosenborg - £12.5m

    Manchester United

    • Matheus Cunha - from Wolves - £62.5m
    • Diego Leon - from Cerro Porteno - Undisclosed
    • Bryan Mbeumo - from Brentford - £65m (£6m)

    Newcastle

    • Antonio Cordero - from Malaga - Free
    • Anthony Elanga - from Nottingham Forest - £55m
    • Park Seung-soo - from Suwon Bluewings - Undisclosed

    Nottingham Forest

    • Igor Jesus - from Botafogo - £10m
    • Jair Cunha - from Botafago - Undisclosed

    Sunderland

    • Enzo le Fee - from Roma - £19.3m
    • Habib Diarra - from Strasbourg - £30m
    • Noah Sadiki - from Royale Union Saint-Gilloise - Reported £15m
    • Reinildo Mandava - from Atletico Madrid - Free
    • Chemsdine Talbi - from Club Brugge - Reported £18m (£2.5m)
    • Simon Adingra - from Brighton - £21m

    Tottenham

    • Kevin Danso - Lens - £20.9m
    • Mathys Tel - from Bayern Munich - £29.8m (£34.1m)
    • Kota Takai - from Kawasaki Frontale - £5m
    • Mohammed Kudus - from West Ham - £55m

    West Ham

    • Jean-Clair Todibo - from Nice - £36.3m
    • El Hadji Malick Diouf - from Slavia Prague - £19m
    • Kyle Walker-Peters - from Southampton - Free

    Wolves

    • Fer Lopez - from Celta Vigo - £19.6m (£21.3m)
    • Jorgen Strand Larsen - from Celta Vigo - £23m
    • Jhon Arias - Fluminense - £15m
  10. Man United na son sayen Sesko da Watkins

    Sesco

    Asalin hoton, Getty Images

    Ollie Watkins da Benjamin Sesco suna daga cikin ƴanwasan da Manchester United za ta ɗauka, idan ta yanke shawarar sayen karin masu cin ƙwallaye.

    Sai dai hakan ba zai yiwuba har sai ta sayar da wasu ƴanƙwallon kuma watakila sai kusan shiga watan Satumba.

    Newcastle ba ta kai ga yanke matasaya ba kan waɗanda za ta saya, bayan da Alexander Isak ke son barin ƙungiyar kan fara kakar bana - hakan ya sa take harin ɗan wasan RB Leipzig, Sesko yayin da Aston Villa ta ce ba ta shirya sayar da Watkins ba.

  11. Za a fara gasar cin kofin nahiyar Asia ta mata a cikin watan Maris

    Mai rike da kofi China za ta fuskanci Koriya ta Arewa da Bangladesh da Uzbekistan a gasar cin kofin ƙwallon kafar mata ta nahiyar Asia da za a yi a Australia a cikin watan Maris.

    Mai masaukin baƙi Austalia za ta fara wasa da Philippines ranar 1 ga watan Maris a Perth a gasar da za a kara a cikin mako uku a 2026.

    Haka kuma Australia tana cikin rukunin da ya haɗa da Korea ta Kudu da Iran a fafatawar ta tawaga 12, ita kuwa Japan tana rukunin da ya ƙunshi Taiwan da Vietnam da kuma India.

    China na fatan lashe kofi na 10 jimilla, wadda rabonta da shi tun 2022.

    Haka kuma a gasar za a tsamo waɗanda za su wakilci Asia a gasar cin kofin duniya ta mata da za a yi a Brazil a 2027.

    Saboda haɗa huɗun da za su kai zagayen daf da karshe, za su samu tikitin shiga gasar da za a yi a Brazil.

    Za kuma a samo biyu daga cikin waɗanda suka kai kwata fainal da za su buga karawar cike gurbi.

  12. Har yanzu Newcastle ba ta samu ƙungiyar da ta taya Isak ba

    Isak

    Asalin hoton, Getty Images

    Newcastle ba ta samu tayi daga wata ƙungiyar dake son sayen Alexander Isak ba, in ji koci Eddie Howe.

    Ɗan wasan tawagar Sweden na son komwa wata ƙungiyar da taka leda, musammam Liverpool, bai je nahiyar Asia ba, inda Newcastle ke buga wasannin sada zumunta, sai dai ƙungiyar ta ce yana ɗan yin jinya ne.

    Wata majiya ta ce har yanzu Liverpool tana son sayen ɗab wasan mai shekara 25, duk da cewar ta ɗaukiHugo Ekitike kan fam miliyan 69, mai buga gurbi iri ɗaya da na Isak.

    Isak ya koma Newcastle United da taka leda a 2022 kan fam miliyan 60, yana da sauran yarjejeniyar kaka uku.

    Ya ci ƙwallo 62 a wasa 109 a Newcastle har da 27 da ya zura a raga a kakar da ta wuce.

  13. Wasannin da za a buga ranar Talata

    Wasan cike gurbin buga UEFA Europa Conference League karawar zagaye na biyu

    • FC 03 Differdange da The New Saints FC
    • Iberia 1999 da Levadia
    • Inter D'Escaldes da Olimpija Ljubljana

    Wasan cike gurbin shiga UEFA Champions League karawar zagaye na biyu

    • Dynamo Kiev da Hamrun
    • FC Drita da Copenhagen
    • Kairat Almaty da KuPS
    • Red Star Belgrade da Lincoln Red Imps
    • Zrinjski Mostar da Slovan Bratislava

    Wasan share fagen shiga gasar Carabao Cup

    Barnet da Newport County

    Wasannin sada zumunta

    • Altrincham da Port Vale
    • Braintree Town da Colchester
    • Chatham Town da Bromley (1.00)
    • Hull City da Sunderland
  14. Osaka ta raba gari da kociyanta Mouratoglou

    Naomi Osaka ta raba gari da kociyanta, Patrick Mouratoglou kasa da shekara ɗaya da suka fara aiki.

    Mai rike da Grand Slam huɗu ta sanar da hakan kwana ɗaya tsakani da Emma Raducanu ta doke ta a Washington Open.

    Mai shekara 27 ta fara aiki da Mouratoglou a China Open a cikin Satumbar bara, bayan ta yi hutu mai tsawo, sakamakon haihuwa.

  15. Diaz ya bar sansanin Liverpool domin kammala shirin komawa Bayern Munich

    Diaz

    Asalin hoton, Getty Images

    Luis Diaz ya bar sansanin Liverpool a Japan domin kammala shirye-shiryen komawa Bayern Munich.

    Tuni Liverpool ta sallama tayin ɗan wasan tawagar Colombia kan fam miliyan 65.

    Liverpool, wadda ke buga wasannin shirin tunkarar kakar bana a Tokyo za ta kara da Yokohama F. Marinos, ranar Laraba.

    Tun cikin watan Janairu Diaz, mai shekara 29 ke son barin Liverpool, wadda ta ce sai idan ta samu mai sayensa darajar kasuwar cinikayyar ƴan ƙwallo.

    Tuni Liverpool ta sayi Hugo Ekitike, hakan ya sa ta kara karfin gurbin masu ci mata ƙwallaye, tana kuma fatan saye Alexander Isak daga Newcastle United.

  16. Gossip

    Asalin hoton, ge

    Aston Villa ta shirya fafatawa da AC Milan da kuma Newcastle a kan ɗanwasan gaban Ingila, Dominic Calvert-Lewin, mai shekara 28, wanda kwangilarsa ta ƙare da Everton. (Sun)

    Ana sa ran Newcastle za ta karɓi tayi daga Liverpool a kan ɗanwasan gabanta kuma ɗan Sweden mai shekara 25, Alexander Isak a mako mai zuwa. (Mail)

    Manchester United ta shiga zawarcin ɗanwasan gaban PSG da Faransa mai shekara 26, Randal Kolo Muani, wanda Juventus ki bibiya. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

    Ɗanwasan Ecuador mai shekara 23, Jeremy Sarmiento, ya shirya barin Brighton a bana, kuma ya ja hankalin ƙungiyoyi da dama a Kudancin Amurka da kuma Turai. (Athletic - subscription required)

  17. Sunderland ta kusan kammala sayen Xhaka daga Bayern Leverkusen

    Xhaka

    Asalin hoton, Getty Images

    Sunderland ta kusan kammala sayen Granit Xhaka daga Bayer Leverkusen kan fam miliyan 13 da karin tsarabe-tsaraben da zai kai fam miliyan huɗu.

    Ana sa ran mai shekara 32 zai je Ingila a auna koshin lafiyarsa daga nan ya saka hannu kan yarjejeniyar kaka uku a ƙungiyar ta Stadium of Light.

    Kenan ɗan kasar Switzerland zai sake komawa buga Premier League, bayan kaka bakwai da ya yi a Arsenal.

    Ya buga wa Gunners karawa 297 a Gunners a dukkan fafatawa da lashe FA Cup biyu da yin ƙyaftin na ƙwarya-ƙwarya daga nan ya koma Leverkusen a 2023.

    A kaka biyun da ya taka leda a Jamus, ya bayar da gudunmuwar da Leverkusen ta lashe Bundesliga a 2024 a karon farko a tarihi.

    Idan Xhaka ya kammala komawa Sunderland, zai zama na na takwas da Sunderland ta ɗauka, bayan Enzo Le Fee da Habib Diarra da Noah Sadiki da Reinildo Mandava da Chemsdine Talbi da kuma Simon Adingra.

  18. Guardiola zai huta da zarar ya kammala horar da Manchester City

    Pep Guardiola

    Asalin hoton, Getty Images

    Pep Guardiola ya ce zai huta lokaci mai tsawo da zarar ya kammala aikin horar da Manchester City.

    Guardiola, mai shekara 54, ya fara kociyan City tun daga 2016, sai dai kuma bai taka rawar gani ba a kakar da ta wuce, bayan da ya sa hannu kan yarjejeniyar ci gaba da jan ragamar City zuwa karshen kakar 2027.

    Tun can baya ɗan kasar Sifaniya ya sanar cewar yana son kociyan tawagar wata kasar, amma kafin nan zai huta kafin daga baya ya koma fagen fama.

    Guardiola ya huta shekara ɗaya, bayan da ya bar Barcelona, sannan ya koma Bayern Munich.

    A kakar da ta wuce Guardiola ya kasa lashe kofin Premier League a karon farko bayan huɗu da ya ɗauka a jere kuma na shida a kaka bakwai.

    Da kyar da gumin goshi City ta kare a mataki na uku a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila.

  19. Newcastle na son sayen Ramsdale daga Southampton

    Ramsdale

    Asalin hoton, Getty Images

    Newcastle ta fara tattaunawa da Southampton domin ta samu damar ɗaukar mai tsaron ragar tawagar Ingila, Aaron Ramsdale.

    Tuni batun ya yi nisa, inda Newcastle ke fatan ɗaukar golan a matakin aro ko kuma ta mallake shi.

    Sai dai ƙungiyar da za ta buga Championship a bana ta zaɓi ta sayar da Ramsdale, wanda ta saya daga Arsenal kan fam miliyan 18 a Agustan 2024.

    Newcastle tana son ɗaukar golan ne domin yake kalubalantar Nick Pope, idan ya koma St Jame's Park, zai kara aiki tare da Eddie Howe, wanda ya horar da shi a Bournemouth.

    Ramsdale wanda ya fara tsare ragar tawagar Ingila a karon farko a watan Maris, zai sake buga Premier League, wanda ya yi wasa 30 a kakar da ta wuce da ta kai Southampton ta faɗi daga babbar gasar tamaula ta Ingila.

    Newcastle United, wadda za ta buga Champions Legue na fatan kara karfin ƙungiyar, bayan da Alexander Isak ke son komawa Liverpool, yayin da Newcastle ke son maye gurbinsa da ɗan wasan RB Leipzig, Benjamin Sesko.

  20. Saliba na fatan tsawaita kwantiragin ci gaba da taka leda a Arsenal

    Saliba

    Asalin hoton, Getty Images

    William Saliba ya ce yana fatan zai saka hannu kan yarjejeniyar ci gaba da taka leda a Arsenal.

    Mai tsaron bayan yana da sauran ƙunshin kwantiragin kaka biyu a Gunners, wanda zai ta kare a 2027.

    Tuni wanda suke tsare bayan Arsenal tare, Gabriel ya sa hannu kan yarjejeniyar taka leda a Emirates zuwa karshen kakar 2029.

    Haka kuma Arsenal na sa ran Bukayo Saka zai sa hannu kan kwantiragin ci gaba da wasa a Gunners, bayan da saura kaka biyu yarjejeniyarsa ya kara a ƙungiyar.

    Saliba yana tare da Arsenal a Asia, inda take buga wasannin sada zumuntar tunkarar kaka bana, kuma tuni ta fara da cin AC Milan 1-0 da doke Newcastle United 3-2, za kuma ta fuskanci Tottenham ranar Alhamis.