Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 27/11/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 27/11/2024

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Annur Muhammad Annur da Isiyaku Muhammed

  1. Cire tallafin mai ya sa kashi 40% na kanikawan mota a Kano sun rasa aikinsu - NATA

    Kanikawa

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban ƙungiyar kanikawan mota ta Najeriya (NATA) reshen jihar Kano, Yahya Ibrahim, ya ce, cre tallafin mai da gwamnati ta yi ya raba kashi 40 cikin ɗari na kanikawan da aikinsu.

    Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da kakakin shiyya na kungiyar Rabiu Kura ya fitar, yau Laraba, wadda ke ɗauke da kokawar da shugaban ƙungiyar tasu yake yi kan illar cire tallafin man a kan sana'arsu, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

    Ya ce sakamakon cire tallafin makanikai sun shiga yanayi na talauci sosai, saboda yawan masu motocin da ke kawo musu aiki ya ragu matuƙa.

    A don haka ya yi kira ga gwamnatin jihar da ta shiga lamarin nasu tare da bayar da tallafi na taimaka wa kanikawan su ci gaba da sana'ar.

  2. Ana murna a Lebanon kan yarjejeniyar tsagaita wuta

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyo

    Dandazon mutane sun rika murna a Lebanon bayan cimma sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da ƙungiyar Hezbollah.

    Mutane na nuna farin ciki yayin da wasu ke tababar ɗorewar yarjejeniyar.

    Dubban ƴan ƙasar Lebanon sun fara komawa garuruwansu da ke kudanci, sai dai Isra'ila ta yi gargaɗin cewa har yanzu babu tabbacin tsaro a wasu yankunan.

  3. Yahaya Bello ya musanta zargin rashawa a gaban kotu

    Yahaya Bello

    Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello tare da wasu mutane biyu da Hukumar EFCC ta gurfanar a gaban kotu a yau Laraba sun musanta zarge-zargen rashawa na Naira biliyan 80 da ake yi musu.

    Yahaya Bello, wanda shi ne na farko a cikin mutanen da ake tuhuma tare da sauran mutanen biyu Shuaibu Oricha da Abdulsalami Hudu, sun musanta duka tuhuma 16 da aka fara karanto musu a gaban mai shari'a Maryanne Anenih ta babbar kotun ta Abuja.

    Yahaya Bello da jami'an EFCC

    Joseph Daudu, (SAN - babban lauya) shi ne jagoran lauyoyin da ke kare toshon gwamnan da sauran waɗanda ake tuhuma, yayin da Kemi Pinhero (shi ma babban lauya - SAN), ke jagorantar masu gabatar da ƙara.

    Bayan musanta aikata laifukan, lauyan waɗanda ake tuhumar ya nemi a bayar da belin Bello amma lauyan EFCC ya nemi kada a bayar da cewa wa'adi ya wuce tun watan Oktoba.

    To amma bayan sauraron ɓangarorin biyu kotun ta tsayar da ranar 10 ga watan Disamba mai kamawa domin duba buƙatar belin.

    Yahaya Bello

    EFCC ta yi nasarar gurfanar da tsohon gwamnan na jihar ta Kogi a gaban kotun ta tarayya da ke Abuja a yau Laraba bayan wata da watanni na gaza hakan, kasancewar ya ƙi amsa gayyatar hukumar kuma duk yunƙurinta na kama shi ya ci tura.

    A jiya Talata ne aka ce tsohon gwamnan ya kai kanshi hukumar ta EFCC da rakiyar lauyoyinsa - amma daga baya hukumar ta ce tana tsare da shi.

  4. Farar hula na tururuwar komawa gidajensu a Lebanon bayan yarjeniyar zaman lafiya

    Mutane a motoci da kaya

    Fararen a Lebanon na ta ƙoƙarin komawa gidajensu a kudancin ƙasar bayan da yarjejeniya dakatar da buɗe wuta tsakanin Isra'ila da Hezbollah ta fara aiki.

    Sai dai sojojin Isra'ila sun gargaɗe su da cewa har yanzu fa yanayi bai kai na yadda za a koma wasu yankuan ba - domin akwai haɗari a cewar sojin.

    Sojin sun ce sun yi harbin gargaɗi a kan wasu da suke zargin mayaƙan Hezbollah ne, da sukace suna ƙoƙarin komawa ƙauyen Kfarkela, da ke kusa da iyakar ƙasashen biyu.

    A ƙarƙashin yarjejeniyar sojin Isra'ila za su janye daga kudancin Lebanon tsawon kwana 60, inda su kuma sojojin Lebanon za su je yankin su kuma tabbatar babu sauran wani abu na Hezbollah a wajen.

    Shugaba Biden na Amurka ya ce yarjejeniyar dakatar da buɗe wutar wadda ƙasarsa da Faransa suka jagora ta nuna cewa za a iya cimma zaman lafiya.

    Masar da Jordan sun bayyana fatan yarjejeniyar za ta ka ga gagarumin ƙuduri na cimma dakatar da buɗe wuta a Gaza.

    Jami'an Hamas sun ce yanzu suna fatan za a cimma irin wannan yarjejeniya a yankin Falesɗinawa.

  5. Sarkin Saudiyya ya nemi a yi sallar roƙon ruwa gobe a ƙasar

    Sarki Salman bin Abdulaziz na Saudiyya

    Asalin hoton, OTHERS

    Sarkin Salman na Saudiyya ya yi kira da a yi sallar ne a faɗin ƙasar baki ɗaya a gobe Alhamis, kamar yadda gidan sarautar ƙasar ya fitar a wata sanarwa jiya Talata.

    Sarkin ya yi kiran da a yi sallar ta Istisqa, kamar yadda yake a Sunnar Annabi Muhammad (SAW), idan ana cikin buƙatar ruwan sama.

    Haka kuma Sarkin ya buƙaci dukkan Musulmi da su yi addu'o'in neman gafara da tuba ga Allah (SWT), kamar yadda kamfanin dillacin labarai na Sudiyyar ya ruwaito a sanarwar.

    Sannan kuma ya yi kira ga jama'a su ƙara abubuwa na alheri da neman kusanci ga Allah (SWT), kamar sadaka da addu'o'i don neman rahama da sauƙin rayuwa da kuma jinƙai daga Ubangiji.

  6. Kotu na sauraron ƙarar neman dawo da shirin tsige shugaban Afirka ta Kudu

    Cyril Ramaphosa

    Asalin hoton, Getty Images

    Kotun tsarin mulki ta Afirka ta Kudu na sauraron wata ƙara da wasu jam'iyyu biyu na hamayya suka shigar gabanta inda suke neman a dawo da maganar tsige shugaban ƙasar Cyril Ramaphosa.

    Ƙarar a kan wasu maƙudan kuɗaɗe ne da aka sace a gonar Mista Ramaphosa a Limpopo a 2020, da kuma yadda aka yi rufa-rufa a kan maganar.

    Jam'iyyar EFF ( Economic Freedom Fighters ) wadda Julius Malema, ke jagoranta ta ce majalisar dokokin ƙasar ta nuna rashin ya kamata shekara biyu da ta wuce lokacin da ta daƙile ci gaba da bincike a kan lamarin.

    Shugaban na Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya musanta aikata wani abu da ya saɓa doka.

  7. Ana zargin tsohon shugaban Brazil da hannu a yunƙurin juyin mulki

    Jair Bolsonaro

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani rahoton ƴansanda da kotun ƙolin Brazil ta fitar ya zargi tsohon shugaban ƙasar Jair Bolsonaro da hannu kai tsaye wajen yunƙurin juyin mulki domin ci gaba da kasancewa kan mulki bayan zaɓen 2022.

    Rahoton ya ce Mista Bolsonaro yana da masaniya kan yunƙurin kashe,Luiz Inácio Lula da Silva wanda yake shi ne zaɓaɓɓen shugaban ƙasa a lokacin.

    Yanzu dai ya rage ga babban mai shigar da ƙara a Brazil ya yanke hukunci ko zai tuhumi mutanen da rahoton ya ambato.

  8. Gwamnatin Anambra ta yafe wa masu ƙananan sana'o'i haraji

    Charles Soludo

    Gwamnatin jihar Anambra ta cire masu ƙananan sana'o'i da jarinsu yake ƙasa da Naira N100,000 daga biyan haraji.

    Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Law Mefor, ne ya bayyana haka a wata sanarwa a jiya Talata, inda ya ce gwamnatin ta zartar da hakan ne a ƙarshen taron majalisar zartarwar jihar karo na 37, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

    Mefor ya jaddada cewa har yanzu dokar yaƙi da zaman-banza da kashe wando da yawon tasha ta jihar har yanzu tana nan da ƙarfinta, a don haka ya shawarci matasa su shiga shirin koyar da sana'o'i da bayar da jari na gwamnatin jihar domin cin guminsu ta halaliya.

    Kwamishinan ya kuma yi kira ga masu zuba jari da su karɓi kamfanonin gwamnati na jihar, inda yake cewa bayar da su haya ko jinginar da su ga 'yan kasuwa ya fi a ce gwamnati na tafiyar da su.

  9. Hotuna: EFCC ta gabatar da Yahaya Bello a kotu

    Yahaya Bello a kotu
    Bayanan hoto, Lokacin da yake shigowa kotun
    Yahaya Bello a kotu
    Bayanan hoto, Bayan ya shigo ya samu wuri ya zauna
    Yahaya Bello a kotu
    Bayanan hoto, A nan yana zaune ne yana gaisawa da wani yana murmushi
    Yahaya Bello a kotu
    Bayanan hoto, A nan Yahaya Bello tare da lauyoyi
  10. Bayan shekara 17 an yi nasarar haɗa wata giwa da 'yan uwanta a India

    Giwaye

    Asalin hoton, Getty Images

    An yi nasarar sada wata giwa a wani gidan namun daji a Pakistan da 'yan uwanta biyu da ta rabu da su tsawon shekara goma sha biyar.

    An sanya Madhu 'yar shekara 17 a cikin namun daji tare da wata 'yar uwarta da ta mutu a shekarar da ta gabata.

    A jiya Talata ne aka mayar da ita cikin wani wurin shakatawa inda 'yan uwanta mata biyu ke rayuwa.

    Shugaban ƙungiyar kula da namun daji, Josef Pfa-bi-gan ne ya jagoranci aikin, inda ya ce giwaye na da ƙoƙarin riƙe abu na tsawon lokaci shi yasa ba su sha wahala ba wajen hada giwayen.

  11. Za a ware ranakun da dabbobi za su iya ketawa ta gonaki a Nijar

    Makiyaya

    Asalin hoton, Getty Images

    A jamhuriyar Nijar hukumomi sun saka ranar da za a ba makiyaya damar ketawa ta cikin gonaki domin ganin an samu zaman lafiya tsakanin al'ummomi.

    Gwamnan jihar Maraɗi Issoufou Mamman ne ya jagoranci taron tuntuɓar masu ruwa da tsaki kan sanya rana.

    Bayan taron, an tsayar da ranar 31 ga watan Disamba a matsayin ranar sakin gonakin a faɗin jihar.

  12. Tinubu zai tafi Faransa ziyarar aiki

    Tinubu

    Asalin hoton, state house

    A yau Laraba ne shugaban ƙasa Bola Tinubu zai tafi ƙasar Faransa domin ziyarar aiki.

    A wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar, ya ce shugaban ƙasar Faransa, Emmanuel Macron, ne ya gayyaci shugaban na Najeriya.

    Onanuga ya ce ziyarar ta kwana uku ce, kuma za ta mayar da hankali ne, "kan inganta alaƙar tattalin arziki da dimokuraɗiyya da noma da tsaro da ilimi da kiwon lafiya da samar da aikin yi ga matasa da sauran abubuwa muhimmai."

    Sanarwa ta ƙara da cewa Tinubu zai yi tafiyar ce tare da matarsa, Sanata Oluremi Tinubu, inda shugaban na Faransa ta matarsa za su tarbe su.

    Haka kuma Oluremi Tinubu da uwargidan shugaban ƙasar ta Faransa, Brigitte Macron za su gana game da shirin uwargidan shugaban Najeriya na Renewed Hope Initiative na inganta rayuwar matasa.

  13. An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hezbollah

    Hezbollah

    Asalin hoton, AFP

    An cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hezbollah a Lebanon bayan kwashe sama da shekara guda ana rikici.

    Gabanin cimma yarjejeniyar, Isra'ila ta kai wasu hare-hare ta sama birnin Beirut.

    Isra'ila za ta janye dakarunta na tsawon kwana sittin. Sai dai duk da wannan yarjejeniya da aka cimmawa, Isra'ila ta gargaɗi dubun dubatar mazauna yankunan iyakokin Lebanon da rikicin ya raba da muhallansu da cewa har yanzu babu tabbas kan tsaronsu.

    Wakilin BBC ya ce an fara cimma yarjejeniyar ce tun makon da ya gabata a wajen wani taro da aka yi a yankin Gabas ta tsakiya, har zuwa wannan sanarwa.

  14. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Laraba daga nan sashen Hausa na BBC, ind za mu riƙa kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za kuma ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo.

    Ku kasance tare da mu.