Man Utd na son Kvaratskhelia, Chelsea za ta ɗauko Eboue

Asalin hoton, Getty Images
Napoli a shirye take ta sayar da Khvicha Kvaratskhelia a wannan bazara idan har ɗanwasan gaban na Georgia ya ƙi sabunta kwangilarsa, yayin da Manchester United ke son ɗanwasan mai shekara 23. (Sportmediaset - in Italian)
Sabon kocin United Ruben Amorim ya tura wakilai domin sa ido kan ƴanwasan Sporting uku, Geovany Quenda na Portugal mai shekara 17 da ɗanwasan gaba na Sweden Viktor Gyokeres da kuma Pedro Goncalves, na Portugal mai shekara 26. (Mail - subscription required)
Manchester United na son ɗauko ɗanwasan baya na gefen hagu kuma tana nazari tsakanin ɗanwasan Bayern Munich da Canada Alphonso Davies da na AC Milan Theo Hernandez, mai shekara 27. (Florian Plettenberg)
Real Madrid na son ɗauko ɗanwasan baya na Tottenham da Spain mai shekara 25 Pedro Porro. (Sport - in Spanish)
Brighton za ta bayar da aron ɗanwasan Jamhuriyyar Ireland mai shekara 20 Evan Ferguson a Janairu. (Telegraph - subscription required)
Ruud van Nistelrooy, mai shekara 48, ana ganin shi Leicester za ta ɗauko matsayin sabon koci bayan tattaunawa da shugabannin ƙungiyar. (Football Insider)
Arsenal na sa ido kan ɗanwasan gaba na Atalanta Mateo Retegui, wanda darajarsa ta kai fam miliyan 38. (Calciomercato - in Italian)
Manchester United na tunanin sayar da Joshua Zirkzee watanni shida bayan sayen shi, yayin Juventus ta nuna buƙatarsa kan ɗanwasan na gaban Netherlands mai shekara 23. (Corriere Dello Sport - in Italian)
Arsenal na tattauna da ɗanwasan tsakiya na Ingila Ethan Nwaneri mai shekara 17 domin tsawaita yarjejeniya. (Fabrizio Romano)
Chelsea na shirin ɗauko ɗanwasan tsakiya na Watford mai shekara 15 Mathis Eboue, ɗan tsohon ɗanwasan Arsenal Emmanuel Eboue. (Mail)











