An kusa fara dakon sakamakon zaɓen Namibia

Asalin hoton, AFP
Nan bada jimawa ba ake sa ran rufe rumfunan zabe a zaben shugaban kasar Namibiya, wanda ake ganin shi ne mafi zafi tun bayan da ƙasar ta samu ƴancin kai daga ƙasar Afrika ta kudu a 1990.
Sai dai an samu korafe korafen dogayen layuka da karancin katin zabe a wasu rumfunan zabe.
Jamiyar SWAPO mai mulki ta tsayar da mace ta farko a matsayin yar takarara shugaban kasa.
Netumbo Nandi Ndaitwah na fatan maye gurbin Hage Gaingob wanda ya mutu a watan Fabairarun daya gabata bayan ya shafe shekaru tara kan karagar mulki





















