, Man City 0-0 Crystal Palace
Marc Guehi ya gwada sa'a ko zai samu cin kwallo.
Sai dai daga yadda ya kai harin kasan mai tsaron baya ne, domin ta yi sama sosai.
Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga 11 zuwa 16 ga watan Mayun 2026.
Mohammed Abdu
Marc Guehi ya gwada sa'a ko zai samu cin kwallo.
Sai dai daga yadda ya kai harin kasan mai tsaron baya ne, domin ta yi sama sosai.
Crystal Palace ta sake zama barazana daga bugun kusurwa, inda Chris Richards ya saka kai mai kyau amma kwallon ta wuce saman ragar Manchester City.
Ko da yake Manchester City ce ke yawan rike kwallo, Crystal Palace ce ta fi samun damar cin kwallo masu hatsari zuwa yanzu.

Asalin hoton, Reuters
Rayan Aït-Nouri ya fara wasan da kuzari sosai a gefen hagu a Manchester City tun farkon mintuna.
Dan wasan na ta kawo hari da matsa lamba, inda ya taimaka wa City samun bugun kusurwa daa huɗu cikin mintuna 10 na farko a wasan.

Asalin hoton, PA Media
Magoya bayan City suna ta rera “Come on, City!” yayin da tawagar Pep Guardiola ke ci gaba da matsa lamba a gaba.
Matheus Nunes ya nemi a ba su bugun fenariti bayan kwallon da ya daga ta bugi hannun Jaydee Canvot.
Sai dai alkalin wasa bai ga laifin da zai kai ga fenariti ba, inda ya bai wa Manchester City bugun kusurwa kawai.
Brennan Johnson ya samu sarari a bayan masu tsaron bayan Manchester City kafin ya bai wa Jean-Philippe Mateta kwallo mai kyau, inda Mateta ya buga kai tsaye zuwa raga.
Mai tsaron gidan City, Gianluigi Donnarumma, ya yi saurin kokarin tare kwallon, kuma da alama kwallon ta ketare layin raga.
Sai dai ba za a kirga kwallon ba, domin mataimakin alkalin wasa ya daga tuta yana nuna satar gida. Wannan ya zama babban gargadi na farko ga Manchester City tun farkon wasan nan ta kara kula..

Asalin hoton, Reuters
Manchester City sun fara kai hari a kokarin da Omar Marmoush lokacin da ya nemi Antoine Semenyo daga tsakiyar fili.
sai dai kuma Jaydee Canvot ya bata kwallon ba wani hadari..
An take wasan a Etihad, Manchester City na bukatar samun maki uku a karawar nan.
Ismaïla Sarr kuma ya ci ƙwallaye tara a wasanni 10 na baya bayan nan, kuma yana da jimillar 20 a raga a kakar nan — mafi yawa da ɗan wasan Palace ya yi tun Glenn Murray a 2012–13.
Barcelona ta sanar da ƴan wasa 23 domin buga La Liga a gidan Deportivo Alavés a garin Vitòria, yayin da take ci gaba da fafutukar kammala kakar da kafa tarihi, bayan lashe kofin La Liga na biyu a jere..
Babban labari daga ƙungiyar shi ne dawowar Andreas Christensen, bayan da ya warke daga raunin gwiwa da ya hana shi buga wasa tun daga ranar 21 ga watan Disamba 2025—wannan shi ne karon farko da ya koma cikin jerin ƴan wasa bayan kwana 143 yana jinya.
Sai dai koci, Hansi Flick bai je karawar ba da Raphinha, saboda hukuncin dakatarwa, haka kuma Lamine Yamal na jinya.
Barcelona ta je wasan tare da manyan ƴan wasa kamar Pedri da Robert Lewandowski da Ferran Torres da Frenkie de Jong da kuma Joan García.
Haka kuma akwai João Cancelo da Alejandro Balde da Ronald Araújo da Jules Koundé da sauran matasa.
Barcelona na neman ƙarin nasara domin kusantar cimma maki 100 a kakar bana, yayin da wasan da za su buga da Alavés ke zama ɗaya daga cikin wasannin ƙarshe na kakar - yanzu tana maki 91.

Asalin hoton, Getty Images
Har yanzu Barcelona murna bayan da ta doke abokiyar hamayya Real Madrid a wasan El Clásico, tare da tabbatar da lashe kofin La Liga karo na biyu a jere kuma na 29 a hukumance.
Bayan wannan nasara, ta yi shagalin murna a birnin Barcelona, inda ‘ƴan wasa suka jagaye birnin a buɗaɗɗiyar motar bus.
Yanzu kuma hankali ya koma yadda za ta kafa tarhin hada maki 100, yanzu tana da 91, saura karawa uku-uku a kammala kakar bana - za ta je Alaves domin buga La Liga ranar Laraba.
Kociyoyin da suka haɗa maki 100 a gasar La Liga sun haɗa da José Mourinho da kuma Tito Vilanova.

Asalin hoton, Getty Images
Jean-Philippe Mateta yana da ƙwallaye 49 a Premier League, kuma yana dab da zama ɗan wasan Palace na biyu da ya zura ƙwallaye 50 a kungiyar tun bayan Wilfried Zaha mai 68.
Dan wasan Crystal Palace, Jean-Philippe Mateta, yana daf da kafa tarihi a kungiyar yayin da yake da kwallaye 49 a raga a gasar Premier League.
Idan ya sake zura kwallo guda ɗaya, zai zama ɗan wasa na biyu a tarihin Crystal Palace da ya kai kwallaye 50 ko fiye da haka a Premier League bayan Wilfried Zaha wanda ke da 68.
Sai dai alkaluma sun nuna cewa Mateta ba ya yawan cin kwallaye idan kungiyar tana buga wasa a waje. Kashi 35% kacal na kwallayensa (17 daga cikin 49) sun zo ne a wasannin waje.
A wannan kakar ma, biyu kacal daga cikin kwallaye 11 da ya ci sun kasance a wajen gida, abin da ke nuna cewa yana fin kwallaye a gida a Selhurst Park.

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City ta fi kowace ƙungiya zura kwallaye a zagayen farko da ta ci 38, kuma ta fi kowace ƙungiya farke ƙwallaye har guda tara da ta yi tun kan hutu a kakar bana, amma duk ƙwallayenta biyar na baya bayan nan ta yi nasara a zagaye na biyu..

Asalin hoton, BBC Sport
Crystal Palace tana daga cikin ƙungiyoyin da suka fi yin nasara a waje a wannan kakar, tare da nasara bakwai a waje – waɗanda ke gabanta sune Arsenal da Manchester City.
Yayin da saura rabin awa kafin fara wasa, hankali ya koma kan abokan karawar Manchester City — wato Crystal Palace.
Kakar wasa ta kasance mai cike da hawa da sauka ga Crystal Palace da kocinta Oliver Glasner.
Sun fara da manyan nasarori kamar lashe FA Cup da FA Community Shield, tare da samun gurbin buga gasar zakarun Turai. Amma daga baya aka samu babban labari cewa Glasner zai bar kungiyar a ƙarshen kakar 2025-26.
Duk da haka, Glasner har yanzu na da damar barin Selhurst Park cikin tarihi idan ya kawo wa kungiyar wata babbar nasara kafin tafiyarsa.
Fatan Crystal Palace na samun gurbin Turai a kakar wasa mai zuwa yanzu ya rataya ne sosai a kan nasarar da za ta samu a kan Rayo Vallecano, wadda ke matsayi na 10 a gasar cikin gida ta Spain a halin yanzu.

Asalin hoton, Getty Images
Jérémy Doku yana da hannu a cin ƙwallaye bakwai a wasa shida a baya bayan nan a dukkan fafatawa (ya zura biyar ya kuma bayar da biyu aka ci), bayan da a baya yake da bakwai a wasa 24 da suka gabata

Asalin hoton, Getty Images
Erling Haaland ya zura ƙwallo a dukkan wasa biyar da ya buga da Crystal Palace, inda ya tara ƙwallaye takwas gaba ɗaya—kuma yana cikin ƴan wasan da suka fi yin hakan cikin tarihin gasar.