Chelsea da Galatasaray na sha'awar sayen ɗan wasan gaban Ingila Jonathan Rowe mai shekara 23 daga Bologna. (Gazzetta dello Sport)
Ɗan wasan gaban Jamus Nick Woltemade ba ya jin daɗin zamansa a Newcastle kuma Atletico Madrid na cikin ƙungiyoyin da ke sanya ido kan lamarin ɗan wasan mai shekara 24. (Bild)
Marseille ba za ta yi amfani da zaɓin da ta ke da shi na ɗaukar ɗan wasan baya na Faransa Benjamin Pavard mai shekara 30 ba, wanda a halin yanzu yake zaman aro daga Inter Milan. (Bild)
Tottenham na neman ɗan wasan bayan Sassuolo da Bosnia-Herzegovina Tarik Muharemovic, mai shekara 23. (Caught Offside)
Asalin hoton, Getty Images
Ancelotti zai tsawaita kwantiragi a Brazil, aikin koci na karshe da zai yi, Brazil
Kocin Brazil, Carlo Ancelotti, ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa akwai yiwuwar ya tsawaita kwantiraginsa har zuwa shekarar 2030, duk da cewa wannan na iya zama aikinsa na ƙarshe a matsayin koci.
Ancelotti ya je Brazil ne da tarihin lashe Champions League sau biyar a matsayin koci, tare da ɗaukar kofunan lig a manyan ƙasashen Turai biyar, da kuma yin suna wajen iya sarrafa manyan ƴan wasa cikin nutsuwa.
Sai dai shekara guda bayan karɓar ragamar tawagar Brazil, ya fahimci cewa wannan aiki ya bambanta — ba kamar yadda ake shan wahalar horar da kungiya a kullum ba, sai dai cike yake da matsin lamba ga al’ummar da ke matukar ƙaunar ƙwallon ƙafa.
A yanzu, ɗan ƙasar Italy yana jin daɗin aikin horar da tawagar ƙasa, kuma ya ce batun tsawaita kwantiraginsa har zuwa 2030 ya kusa kammala.
Ancelotti ya rattaba hannu kan yarjejeniyar shekara ɗaya ne lokacin da ya zama kocin Brazil a watan Mayun bara, amma yanzu ana sa ran zai ci gaba da aikin bayan FIFA World Cup a Amurka da Canada da kuma Mexico..
Rahotanni sun ce Ancelotti na fuskantar matsin lamba wajen zaɓen tawagar Brazil da zai da su kofin duniya, musamman saboda yawaitar raunuka da kuma rashin tabbas kan lafiyar Neymar.
Kocin ya kuma jaddada muhimmancin aikin horaswa, yana cewa dole ne koci ya iya zama jagora, mai ba da shawara, da kuma wanda ƴan wasa za su iya yarda da shi.
Asalin hoton, Getty Images
An dakatar da wasan tennis a Rum, saboda hayaki da ya turnuke sararin samaniya, Inter Milan
An dakatar da wani wasa a Italian Open na kusan minti 20 saboda wani hayaƙi da ya turnuke sararin samaniya, sakamakon Coopa Italia da Inter Milan ta lashe a Stadio Olimpico.
A gasar ta tennis ɗan kasar Italy, Luciano Darderi ya samu nasara a kan ɗan ƙasar Sifaniya, Rafael Jodar da kaiwa karawar daf da karshe a lokacin da agogo ke cewa ƙarfe biyu na dare agogon Foro Italico.
Jodar mai shekara 19 yana cin wasan 6-5 a zagayen farko lokacin da hayaƙin ya mamaye babban filin wasan sakamakon murnar nasarar da Inter ta ci 2-0 a kan Lazio, inda filin wasan yake kusan mita 500 kacal daga wajen da ake buga gasar tennis.
An dakatar da wasan saboda ba a gani sosai a cikin fili, sannan hayaƙin ya kuma kawo matsala ga tsarin na’urar tantance layin ƙwallo ta lantarki.
Asalin hoton, Getty Images
, Daga Jarida
Ɗan wasan gaba na Ivory Coast Yan Diomande, wanda rahotanni suka ce farashinsa zai kai fam miliyan 80, na jan hankalin Chelsea da Liverpool amma ɗan wasan mai shekara 19 ba zai yi gaggawar barin RB Leipzig ba. (The Athletic)
Leeds na zawarcin ɗan wasan gaban Belgium Lois Openda, wanda ke shirin komawa Juventus daga RB Leipzig, amma kulob ɗin na Italiya na fatan cefanar da ɗan wasan mai shekara 26, sakamakon rashin tagomashi da ya samu a zaman aron da ya ke yi a ƙungiyar. (TeamTalk)
Manchester United na neman matsuguni na dindindin ga golan Kamaru Andre Onana, mai shekara 30, wanda a halin yanzu ya ke zaman aro a ƙungiyar Trabzonspor ta Turkiyya. (ESPN)
Har ila yau United a shirye take ta miƙa sabuwar yarjejeniya ga mai tsaron gida Tom Heaton, mai shekara 40. (Caught Offside)
Asalin hoton, Getty Images
Fifa ta yi haɗin gwiwa da kamfanin zuba jari na Saudiyya, Gasar kofin duniya
Saudi Arabia ta hannun Asusun Zuba Jari na Ƙasa, wato Public Investment Fund (PIF), zai tallafa gasar cin kofin duniya da za a gudanar a bana.
Masu shirya gasar, FIFA, ya sanar a ranar Alhamis cewa an cimma yarjejeniya da kamfanonin PIF guda biyu — Savvy Games Group da Qiddiya City — domin yankunan Arewacin Amurka da Asiya.
Wannan yarjejeniya ta ƙara gina alaƙar da aka fara tun gasar FIFA Club World Cup, tare da ƙarfafa haɗin kai kafin Saudi Arabia ta karɓi baƙuncin FIFA World Cup.
Sabuwar yarjejeniyar ta zo ne makonni biyu bayan PIF ta sanar da kawo ƙarshen tallafinta ga LIV Golf a ƙarshen shekarar nan.
PIF ta bayyana cewa ci gaba da zuba kusan fam biliyan 4 cikin LIV Golf bai dace da sabon tsarin dabarunta na zuba jari ba.
A wata sanarwa da FIFA ta fitar, ta ce haɗin gwiwar na da nufin bunƙasa ƙwallon ƙafa a duniya daga matakin yara har zuwa na ƙwararru, ƙara kusanci da magoya baya, da samar da sabbin damar shiga harkar wasan.
Sanarwar ta ƙara da cewa: “A yayin gasar, PIF da kamfanoninta za su samar da abubuwan tunawa na musamman tare da ƙaddamar da sababbin hanyoyin haɗa magoya baya da al’ummar ƙwallon ƙafa a babban dandalin wasan duniya.”
Haka kuma sanarwar ta bayyana Savvy Games Group a matsayin “babban jagoran Saudiyya a harkar wasanni na bidiyo da esports a duniya”, yayin da Qiddiya City aka bayyana shi a matsayin “babban birnin nishaɗi, wasanni da al’adu na nan gaba” a ƙasar.
Asalin hoton, Getty Images
Inter Milan ta lashe kofi biyu a bana karon farko bayan shekara 16, Inter Milan
Inter Milan ta lashe kofi biyu a gasar cikin gida a karo na farko cikin shekaru 16, bayan da ta doke Lazio da ci 2-0 a wasan ƙarshe a Coppa Italia.
Ƙungiyar da Cristian Chivu ke jan ragama ta riga ta ɗauki kofin Serie A na kakar nan na 21 jimilla a farkon wannan watan, saura wasanni uku a kare kakar.
Ƙwallon da Adam Marusic ya ci gida da kuma wadda Lautaro Martinez ya zura a raga suka taimaka wajen tabbatar wa Inter lashe kCoppa Italia na 10 a filin Stadio Olimpico a ranar Laraba.
Karo na ƙarshe da Inter ta lashe kofunan gida biyu, shi ne a zamanin nasarar kofuna uku tare da Jose Mourinho a shekarar 2010 a lokacin Chivu ya kasance cikin ƴan wasan tawagar.
Asalin hoton, Getty Images
Wasannin mako na 37
Asalin hoton, BBC Sport
Yadda aka taka leda a karawar, Manchester City 3-0 Crystal Palace
Asalin hoton, BBC Sport
An tashi wasa, Manchester City 3-0 Crystal Palace
An tashi wasan kuma yanzu saura wasa biyu a kammala kakar nan, har yanzu Arsenal ce ta daya da kuma Manchester City ta biyu.
Tuni dai Wolverhampton da Burnley suka faɗi daga gasar bana.
, Manchester City 3-0 Crystal Palace
Phil Foden na Manchester City ne ya zama gwarzon dan wasan a karawar ta Premier Laegue.
, Manchester City 3-0 Crystal Palace
Asalin hoton, BBC Sport
Karin lokaci, Man City 3-0 Crystal Palace
Manchester City ta ci kwallo uku, kuma a wasan farko da suka kara a bana irin yawan wanda ta ci kenan a Selhurst Park.
City za ta buga wasan karshe a FA Cup da Chelsea, itakuwa Palace za ta yi karawar karshe a Conference League da Rayo Vallecano
, Manchester City 3-0 Crystal Palace
Asalin hoton, Getty Images
Goal - Man City 3-0 Crystal Palace, Savinho
Rayan Cherki ya fara tasiri nan take bayan shigowarsa daga benci, inda cikin ƙasa da mintuna biyar ya kauce ketar da ak zo masa, ya ci gaba da gudun da kwallon, sannan ya bai wa Savinho, wanda bai bata lokiaci ba ya zura a raga.
Asalin hoton, Getty Images
Katin gargadi, Manchester City 2-0 Crystal Palace
Daichi Kamada ya samu katin gargadi, bayan an hukunta shi da faduwa da gangan a minti na 80.
Hakan ya biyo bayan kuskuren buga ƙwallo daga Gianluigi Donnarumma, wanda ya bai wa Crystal Palace dama cikin sauri. Kamada ya kutsa cikin gidan City, amma bayan ɗan taɓawar Mateo Kovačić ya faɗi ƙasa, alƙali ya ga bai isa a ba shi fenariti ba, sai dai ya ba shi katin gargadi.
Canji da Man City, Man City 2-0 Crystal Palace
Mateo Kovacic da Rayan Cherki daga Manchester City sun maye gurbin Omar Marmoush da Bernardo Silva.
, Manchester City 2-0 Crystal Palace
Wata babban dama ga Manchester City bayan Savinho ya hango Antoine Semenyo a gefen dama, ya ba shi kwallo mai kyau ya shiga cikin gidan Palace.
Jérémy Doku kuwa ba kowa a wajensa yana jiran a bashi kwallon, amma Semenyo ya yi mummunan kuskure wajen yin pass daga nan damar ta lalace.
, Manchester City 2-0 Crystal Palace
Wani canji kuma a Crystal Palace — shi ne na huɗu a wasan nan.
Daichi Kamada ya shigo filin wasa domin maye gurbin Brennan Johnson, wanda ya koma benci.
, Manchester City 2-0 Crystal Palace
Ko da yake Manchester City na cin 2-0 a wasan, kocinta Pep Guardiola bai nuna gamsuwa.
An gan shi a fusace a gefen fili, duk da cewa City na da cikakken iko a wasan da kuma alamar cewa suna kan hanya mai kyau zuwa nasara.
, Manchester City 2-0 Crystal Palace
Brennan Johnson ya samu damar gudu da kwallo daga gefen hagu bayan da aka tura masa kwallo daga gaba mai kyau, amma nugun da ya yi zuwa cikin gidan City bai yi kyau ba.
Crystal Palace za ta ji cewa ya kamata ya yi abin da ya fi haka, domin damar na iya zama mai hatsari idan an aiwatar da ita da kyau.