Beckham ya zama biloniya na farko daga Burtaniya a fannin wasanni

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga 11 zuwa 16 ga watan Mayun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. , Manchester City 2-0 Crystal Palace

    Jefferson Lerma ya kusa yin kuskure mai haɗari daga wani bayar da kwallo daga baya, wanda zai iya bai wa Antoine Semenyo damar kai hari a cikin akwatin fanareti.

    Sai dai Maxence Lacroix ya yi saurin kai ɗauki, inda ya isa gaban ɗan wasan Manchester City ya kawar da haɗarin kuma ya ceci kuskuren abokin wasansa.

  2. , Manchester City 2-0 Crystal Palace

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  3. Man City ce ta fara canjin yan wasa, Man City 2-0 Crystal Palace

    Jeremy Doku da Nathan Ake suka maye gurbin Josko Gvardiol da kuma Matheus Nunes.

  4. An kusan cin kwallo, Manchester City 2-0 Crystal Palace

    Ismaïla Sarr, wanda shi ne ɗan wasan da ya fi zura kwallaye a Crystal Palace, ya kusa samun dama mai kyau bayan shigowarsa a matsayin canji.

    Sai dai kwallon da ya buga ya je kai tsaye ga mai tsaron raga, Gianluigi Donnarumma, wanda ya kama cikin sauƙi ya hana Palace rage tazara.

  5. , Manchester City 2-0 Crystal Palace

    Oliver Glasner ya fara sauya ƴan wasa na Crystal Palace a minti na 60 yayin da suke ƙoƙarin komawa cikin wasan.

    Jørgen Strand Larsen ya maye gurbin Jean-Philippe Mateta a gaba, yayin da Adam Wharton ya shiga maimakon Will Hughes a tsakiyar fili.

  6. , Manchester City 2-0 Crystal Palace

    Bayan riƙe kwallo da ta dade a hannunsa, Matheus Nunes ya samu ƙwallon a ƙafarsa yayin da abokan wasansa na Manchester City ke jiran a bshi a lokacin da yake cikin gidan Palace.

    Sai dai ɗan wasan na City ya yi ƙoƙarin yin bugun kusurwa, amma mai tsaron bayan Crystal Palace ya dakatar da shi ta hanyar kawar da ƙwallon zuwa bugun kwana.

  7. , Manchester City 2-0 Crystal Palace

    Crystal Palace ta kusa samun wata dama mai hatsari, inda Brennan Johnson ya bai wa Jefferson Lerma kwallo shi kuma ya ja zuwan gida City

    Lerma ya samu sarari mai kyau, amma taɓawar farko ɗinsa ba ta yi kyau ba, wanda ya sa damar ta ɓaci kafin Manchester City ta tsira daga haɗarin.

  8. , Manchester City 2-0 pALACE

    LIV

    Asalin hoton, Reuters

  9. Katin gargadi, Man City 2-0 Crystal Palace

    Katin gargadi na farko a wasan nan da aka bai wa dan wasan Crystal Palace, Tyrick Mitchell, saboda ketar da ya yi wa Savinho.

  10. , Manchester City 2-0 Crystal Palace

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  11. , Manchester City 2-0 Crystal Palace

    Phil Foden ya yi tasiri a farkon minti 45 da bayar da kwallo biyu aka zura a raga kenan biyar jimillaa da ya fuskanci Palace da yake samar da damarmaki .

    Rahoton ya nuna cewa babu wani ɗan wasa da ya ƙirƙiri dama fiye da haka a cikin mintuna 45 na farko na wani wasan Premier League a wannan kakar.

  12. , Manchester City 2-0 Crystal Palace

    Babu wani sauyi da aka yi a farkon wasan zagaye na biyu, domin dukkan bangarorin biyu — Manchester City da Crystal Palace — sun ci gaba da karawa da ƴan wasan da suka fara, kuma babu wani wanda ya ji rauni.

  13. An koma zagaye na biyu, Man City 2-0 Palace

    Idan Manchester City ta samu maki uku a karawar nan kenan da saura yaki a gaban Arsenal a fatan lashe kofin bana.

    Liv

    Asalin hoton, Getty Images

  14. , Manchester City 2-0 Crystal Palace

    An tafi hutun rabin lokaci a Etihad, inda Manchester City ke jagoranci da kwallaye 2-0 a kan Crystal Palace.

    Zaɓin ‘yan wasan farko da Pep Guardiola ya yi ya ɗan haifar da tambayoyi kafin fara wasa, amma ‘yan wasansa sun tabbatar da cewar suma suna kan ganiya.

    A yanzu, Manchester City ce ke da rinyaje a wasan yayin da suka shiga hutun rabin lokaci suna kan gaba.

  15. , Man City 2-0 Crystal Palace

    An yi karin lokacin minti ɗaya daga nan za a je hutu.

  16. GOAL - Man City 2-0 Crystal Palace, Omar Marmoush

    Babu Erling Haaland a wasan ba matsala a wajen Manchester City!

    Phil Foden ya sake nuna hazaka inda ya sauke kwallon da ta fito daga Joško Gvardiol a cikin akwatin da'ira ta 18.

    Kwallon ta faɗa hannun Omar Marmoush, wanda ya juya cikin sauri ya buga ta kuma fada cikin raga.

    Foden ya bayar da kwallo biyu kenan aka zura a raga a wasan, kuma Manchester City ta ƙara tazarar kwallaye zuwa 2-0, tana ƙara karfafa matsayinta a wasan.

    Live

    Asalin hoton, Getty Images

  17. , Man City 1-0 Palace

    Liv

    Asalin hoton, Reuters

  18. GOAL - Man City 1-0 Crystal Palace, Antoine Semenyo

    Phil Foden ne ya bayar da ƙwallon aka zura a raga.

    Ɗan wasan tawagar Ingila ya buga wata kwallo mai kyau a bakin akwatin raga da hakn ya buɗe hanya ga Antoine Semenyo, wanda ya zura ƙwallo cikin raga cikin sauƙi, wanda sai da ya wuce Dean Henderson, ya bai wa Manchester City jagorancin fafatawar.

    Wannan shi ne bugun farko da Manchester City ta yi daidai da raga a duk daren, amma ya isa ya canza sakamakon wasan zuwa 1-0.

    Liv

    Asalin hoton, Reuters

  19. , Manchester City 0-0 Crystal Palace

    Yanayin wasan a Etihad yana ƙara zama mai tsauri sosai. Ƴan wasan Manchester City sun san muhimmancin karawar nan, kuma magoya baya ma suna jin wannan a tare da su.

    Idan har aka ci gaba da kasancewa babu ci, to matsin lamba da tashin hankali zai ƙara ƙaruwa a dukkan bangarorin biyu yayin da wasan ke tafiya.

  20. , Manchester City 0-0 Crystal Palace

    Abokin wasan Marc Guéhi a tsaron baya, Abdukodir Khusanov, ya gwada sa’arsa da buga kwallon da karfi, bayan da Crystal Palace ta kasa kawar da wata kwallo yadda ya kamata ta fada gabansa kimanin yadi 25 daga raga.

    Sai dai bugun bai kasance mai hatsari ba, kuma ba matsala daga wajen mai tsaron ragar Palace.