Mu kwana lafiya
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Ahmad Bawage ke cewa asuba ta gari.

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 28/11/2024
Haruna Kakangi, Abdullahi Bello, Isiyaku Muhammed, da Ahmad Bawage
Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.
Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.
Ahmad Bawage ke cewa asuba ta gari.


Asalin hoton, Kharkiv region emergencies department
Shugaba Putin ya ce mummunan harin da Rasha ta kai kan cibiyar makamashin Ukraine, martani ne ga harin roka mai cin dogon zango ƙirar Birtaniya da Amurka, da abokan faɗan nasa suka harba cikin Rasha.
Vladimir Putin ya ce Rasha ta harba rokoki 90 cikin dare, ta kuma kai ɗaruruwan harin jirage mara matuƙi a kan Ukraine.
Mutane fiye da miliyan ɗaya ne aka katsewa wutar lantarki a Ukraine, bayan hare-haren na ranar Laraba da dare, lamarin da ya janyo rashin ruwa da katsewar harkokin sufuri.
Gwarzuwar gasar Hikayata ta 2024 Hajara Ahmad Hussain ta ce bai wuce mako biyu ba kafin rufe shiga gasar lokacin da fara shirin rubuta nata labarin.
A wannan bidiyon na sama, ta bayyana yadda ta samo jigon labarin Amon 'Yanci, wanda ya lashe gasar tare da samun kyautar naira miliyan ɗaya.
Hikayata gasa ce ta ƙagaggu kuma gajerun labarai cikin harshen Hausa da BBC Hausa ke shirya wa mata zalla duk shekara, kuma wannan ne karo na tara.

Asalin hoton, AFP
Tsohon shugaban ƙasar Najeriya, Goodluck Ebele Jonathan ya yi wani gargaɗin cewa ana buƙatar haɗin-kai tsakanin ‘yan Najeriya, domin samun zaman lafiya.
Jonathan ya ce yadda ƴan ƙasar ke fifita kabilunsu fiye da biyayya ga Najeriya na da matukar barazana ga zaman lafiya da ci gaban ƙasa.
Tsohon shugaban ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su sake duba abubuwan da suka sa a gaba da kuma ƙoƙarin samar da haɗinkai.
'Biyayya ko fifita kabilanci na kawo cikas ga ci gaban Najeriya, don haka ya kamata shugabanni su aiwatar da manufofin da za su karfafa haɗin-kai maimakon neman suna ko yabo na kankanin lokaci," in ji Jonathan.
Haka kuma ya nuna cewa akwai buƙatar sauya tunanin ƴan ƙasar, inda ya buƙaci ƴan majalisar tarayya da su ɗauki kowane ɗan Najeriya a matsayin nasu, ba wai ga jihohinsu ko kabilunsu kaɗai ba.

Asalin hoton, Uganda Red Cross Society
An tabbatar da mutuwar mutum 13, ciki har da jariri a wata zaftarewar ƙasa da ta afku cikin dare ranar Laraba, a wasu ƙauyuka biyar da ke kudancin Uganda.
Gidaje aƙalla 40 ne lamarin ya shafa, kuma har yanzu ana ci gaba da aikin zaƙulo mutanen da ƙasa ta rufta da su.
Mazauna yankin sun ce suna cikin fargaba saboda mamakon ruwan saman da ake ci gaba da yi, yayin da hukumomi ke cewa suna bakin ƙoƙarin su wajen kai ɗauki.

Asalin hoton, NAFDAC/X
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna na Najeriya - NAFDAC ta yi gargaɗin cewa akwai jabun maganin malaria (Artemether + Lumefantrine 20/120mg) da ke yawo a cikin ƙasar.
NAFDAC ta bayyana haka ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na X ranar Alhamis, inda ta ce wani kamfani daga Indiya ne mai suna Strides Arcolab Limited, ya samar da maganin.
“An gano maganin na jabu a Abuja, babban birnin tarayya da jihar Ribas yayin aikin sa ido na jami'an mu," in ji sanarwar NAFDAC.
Ta ce binciken da ta yi a ɗakin gwaje-gwaje kan maganin ya nuna cewa ba shi da inganci. Kuma akwai kura-kurai kan yadda aka yi rubuta a jikin kwalin maganin na jabu.
Hukumar ta ce maganin ya daina aiki kuma lambar rijistar NAFDAC da ke jikinsa shi ma na bogi ne.
Don haka ta yi gargaɗin cewa jabun maganin na da illa ga lafiyar ɗan'adam, saboda ba shi da ingancin da ya kamata.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, Getty Images
Magoya bayan Everton da Liverpool da Manchester City da United sun haɗa ƙarfi wuri daya domin gudanar da zanga-zanga a wannan makon kan tashin farashin tikitin shiga kallon kwallo.
Sun samu goyon bayan ƙungiyar magoya bayan kwallon ƙafa ta Ingila kan hakan, Magoya bayan United da na Everton sun yi shirin ɗaga kwalaye ɗauke da 'Ku dakata da tatsar magoya bayanku' gabanin wasan da za su yi a Old Trafford a ranar Lahadi.
A Anfield da Liverpool za ta karbi baƙungin Manchester City, magoya bayan ƙungiyoyin biyu za su ɗaga kwalaye kamar na takwarorinsu Everton da Man Utd.

Asalin hoton, X/Bayo Onanuga
Majalisar wakilan Najeriya ta tabbatar da naɗin Laftanar Janar Olufemi Oluyede a matsayin babban hafsan sojin ƙasa na Najeriya.
Hakan na zuwa ne bayan gabatar da rahoton kwaitin da aka kafa domin tantance shi ranar Laraba.
Tun da farko, shugaba Bola Tinubu ya naɗa Janar Oluyede a matsayin muƙaddashin babban hafsan sojin ƙasa bayan mutuwar Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.
Shugaban kwamitin da ya tantance shi, Babajimi Benson, wanda ya gabatar da rahoton, ya ce an yi wa Oluyede tambayoyi kan batutuwan tsaro na ƙasa kuma ya amsa su yadda ya kamata.
Ya ce kwamitin ya gamsu da kwarewarsa kuma saboda haka zai iya rike ofishin da aka ba shi.

Asalin hoton, State Emergency Service of Ukraine
Dubban mutane na zaune cikin duhu a Ukraine bayan wani harin Rasha ya faɗa a kan cibiyoyin makamashin ƙasar da kuma yin sanadiyyar ɗaukewar lantarki.
Shugaba Zelensky ya ce Rasha ta yi amfani da manyan makamai wajen kai hare-haren, kuma hakan ya ƙara janyo wahala a gyara cibiyoyin makamashin da ke gudana.
Mutane sun ce suna tsananin buƙatar lantarki a yanzu.
Ukraine dai ta sha yin ƙorafin cewa Rasha ta na saɓa dokokin yaƙi wajen kai hare-hare a cikin ƙasar ta.

Ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Amnesty International ta ce ƴansanda sun yi amfani da ƙarfi a kan waɗanda suka yi zanga-zangar a tsakanin ranakun 1 zuwa 10 ga watan Agusta.
Rahoton ƙungiyar ya ƙara da cewa an kashe aƙalla mutum 24 a jihohin Borno da Kaduna da Kano da Katsina da Jigawa da Neja, kamar yadda rahoton ƙungiyar ya bayyana.
"Ƴan Najeriya sun fuskanci rashin amfani da doka, inda jami'an tsaro suka yi amfani harsasai a kan masu zanga-zangar tsadar rayuwa. Daga cikin waɗanda aka kashe matasa guda 20, da wani dattijo da ƙananan yara guda biyu," in ji shi sanarwar, wadda Isa Sanusi, daraktan ofishin a Najeriya ya sa wa hannu.
Rahoton ya ƙara da cewa waɗanda aka kashe za su iya haura 24 "saboda gwamnatin ta ɓoye ainihin abin da ya faru.
A cewar rahoton: "Dole ne gwamnatin Najeriya ta tuhumi ƴansanda da jami'an tsaro bisa amfani da ƙarfi a kan masu zanga-zangar lumana. Akwai mamaki yadda ƴansanda suke cewa ba su aikata laifin komai ba, duk da dalilan da suka bayyana.
"Dole shugaban ƙasa Bola Tinubu da gwamnatinsa su gabatar da bincike akan zargin cin zarafin masu zanga-zangar, sannan a tabbatar a hukunta waɗanda aka kama da laifi.
"An kashe mutum 12 a Rijiyar Lemo da Ƙofar Nasarawa. A Jigawa an kashe mutum 3 a Hadejia, sannan aka kashe mutum 1 a Ƙofar Sauri a Katsina. A Kaduna wani soja ya kashe wani ƙaramin yaro a Zaria, sannan ƴansanda sun kashe mutum a cikin Kaduna. A Maiduguri an kashe mutum 3 a gidan man A.A Kime da ke mahaɗar Bolori. A Neja, an kashe mutum uku a titin Abuja-Kaduna."

Asalin hoton, AFP
Shugaban mulkin sojin ƙasar Mali, Janar Assimi Goita, ya yi kira ga sabon firaministan ƙasar, Janar Abdoulaye Maifa ya fara shirye-shiryen zaɓe a nan gaba domin kawo ƙarshen mulkin soji.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jagorantar taron majalisar ministocin ƙasar, duk da bai bayyana lokacin da za a yi zaɓen ba.
Janar Goita ya shaida wa sabon firaiministan cewa akwai buƙatar ya fara tsara hanyoyi da za a yi zaɓen, inda ya ce "akwai buƙatar a gudanar da zaɓe sahihi kuma cikin lumana."
Kafin sanarwar, an daɗe ana nuna shakku kan shirin jagororin mulkin sojin ƙasar, inda ake tunanin da wahala su gudanar da zaɓe sahihi, musamman kasancewar ana tunanin shugaban mulkin sojin zai tsaya takara.
Da farko, jagororin mulkin sojin sun ce za a gudanar da zaɓe ne a watan Fabrairun bana, amma suka ɗage saboda "wasu dalilai.
Sai dai sanya kuɗin zaɓen a cikin kasafin kuɗin 2025 ya sa ana tunanin za a yi zaɓen a baɗi, duk da cewa babu tabbas.

Asalin hoton, Reuters
Tsohon jagoran mayaƙa kuma sanata a Liberiya, Prince Johson ya rasu yana da shekara 72 a duniya.
Ya zuwa yanzu ba a san musabbabin mutuwarsa ba, amma rahotanni sun ce ya mutu a wata cibiyar lafiya a safiyar yau Alhamis.
Prince Johnson dai ya taka muhimmiyar rawa a yaƙin basasar ƙasar da aka yi tsakanin shekarar 1989 da 2003.
A matsayinsa na magudun yaƙi, ana tsoron Prince Johnson kamar wani dodo.
Wani bidiyonsa yana kwankwaɗar giya a daidai lokacin da yaransa ke ganawa tsohon shugaban Liberia, Samuel Doe azaba har suka kashe shi a 1990, ya ƙara nunan irin rawar da Prince Johnson ya taka a yaƙin basasar ƙasar na farko.
Bayan ya yi gudun hijira zuwa Najeriya na tsawon shekaru, Johnson ya koma Liberiya a shekara ta 2004 domin cimma burinsa na siyasa.
Daga bisa an zaɓe shi a matsayin sanata a mazaɓarsa ta Nimba kuma ya taka muhumiyar rawa wajen zaɓen shugaban Liberia mai ci, Joseph Boakai.
A yayin da ƙasar Liberiya ke ci gaba da jimamin mutuwar mutane kusan dubu 250 lokacin yaƙin baasasa biyu da aka yi a ƙasar, wataƙila mutuwar Johnson za ta haifar da sabuwar muhawara game da irin rawar da ya taka a lokacin yana raye.

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin Australia za ta haramta wa yara ƴan ƙasa da shekara 16 amfani da shafukan sada zumunta bayan majalisar dattawar ƙasar ta amince da ƙudurin da ta miƙa.
Haramcin - wanda ba zai fara aiki ba sai nan da aƙalla wata 12- zai ba gwamnatin damar cin kamfanonin kafofin sadarwa tara na kuɗin da zai iya kai wa har zuwa A$50m ($32.5m; £25.7m) idan ba su ɗauki matakan hana yaran amfani da kafofin ba.
Firaiministan ƙasar, Anthony Albanese, ya ce ana buƙatar dokar domin kiyaye ƙananan yara daga "cutarwa" a kafofin sadarwa.
Sai dai masu sukar matakin suna tambayoyin ta yaya za a iya tabbatar da dokar, tambayoyin da har yanzu ba a fayyace amsoshinsu ba.
Bayan amincewa da ƙudurin a majalisar dattawa, yanzu za a kai majalisar wakilai - inda mafi rinjayen mambobinta ƴan jam'iyyar gwamnati ne - kafin ya zama doka.
Sai dai ƙudurin bai fayyace waɗanne kafofin ne za a hana ƙananan yara amfani da su ba. Amma ministan sadarwa na ƙasar ya ce za su bayyana su daga baya.

Asalin hoton, X/Bayo Onanuga
Muƙaddashin babban hafsan sojin ƙasan Najeriya, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, ya sha alwashin tabbatar da zaman lafiya mai ɗaurewa a Najeriya idan aka tabbatar masa da muƙamin shugabancin shugabancin rundunar sojin ƙasan ƙasar.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya bayyana a gaban kwaminitin tsaro na majalisar wakilai ta Najeriya a ranar Laraba, kamar yadda shafin intanet na tashar Chanells ya ruwaito.
Ya ce matsalar tsaron Najeriya a yanzu na buƙatar haɗin kai daga dukkan masu ruwa da tsaki domin tabbatar da zaman lafiya a lungu da saƙon ƙasar.
Ya ce, "a sama da shekara 30 da na yi ina aikin soja, na yi aiki a wurare daban-daban a rundunar sojin ƙasan Najeriya. Don haka ba zan tsame hannuna daga dukkan nasarori ko rashinsa da aka samu a baya ba, amma idan aka tabbatar da ni, zan samu wata dama jan ragamar rundunar tare da kawo wasu dabarun da za su taimaka domin rundunar ta samu ƙarin nasarori."
Al'ummar arewacin Najeriya mazauna Legas sun gudanar da taro domin tantance irin ci gaban da suka samu da koma-baya wajen samun rabon dimokradiyya da haɗin kai.
Sun ce a yanzu sun fahimci cewa dole ne su zauna domin gano wuraren da za su inganta da kuma gyara kura-kurai na baya don tabbatar da kyakkyawar makomar al’ummar arewa mazauna Legas da ma kudancin ƙasar baki ɗaya.

Asalin hoton, EPA
Shugaban ƙasar Rasha, Vladimir Putin, ya ce ƙasarsa za ta cigaba da gwada makamanta masu linzami a kan Ukraine.
Putin ya kuma yi ikirarin cewa Rasha ta ruɓanya haka makamanta masu linzami, inda a cewarsa suna haɗa kusan ninki goma na makaman, sama da na ƙasashen ƙungiyar Nato, sannan ya ƙara da cewa zuwa shekarar 2025, haɗa makamansu masu cin dogon zango zai ƙaru da kashi 25 zuwa 30.
Shugaban ƙasar ya ƙara da cewa Rasha na da wasu makamai masu aiki irin Oreshnik - sabon makami mai linzami da ta harba wa Ukraine a makon jiya - wanda shi ma ya kammalu.
Ya ƙara da cewa za a iya kwatanta ƙarfin Oreshnik ne da makamnin nukiliya, sannan ya ƙara da cewa za su cigaba da gwajin makaman ne a matsayin martani ga "maƙiyansu."

Asalin hoton, Getty Images
Shugaban Najeriya na yin wata ganawa da shugaban ƙasar Faransa Emmanuel Macron a ranar farko ta ziyarar aiki da shugaban na Najeriya ke yi a ƙasar.
A yau Alhamis, Tinubu ya isa fadar shugaban Faransa ta Elysee tare da tawagarsa, wadda ta hada da ministan harkokin wajen Najeriya, Yusuf Tugga da ministan kuɗi, Wale Edun da na tsaro Badaru Abubakar.
A ɓangare ɗaya shugaban Faransa ya shiga ɗakin taron ne tare da ƙaramin ministan harkokin waje na ƙasar, Thani Mohamed Soilihi da kuma ministan tsaro na Faransa, Sebastien Lecornu da sauran jami'ai.
Ana sa ran Najeriya da Faransa za su ƙulla hulɗoɗi na diflomasiyya da kasuwanci a lokacin ziyarar ta shugaba Tinubu, wadda take zuwa bayan ragin tagomashi da Faransa take samu a Afirka.
Dangantaka ta yi tsami tsakanin Faransa da ƙasashen da ta rena a yammacin Afirka, kamar Nijar da Burkin Faso da Mali.
Ƙasashen sun yanke huldar diflomasiyya da Yamma tare da karkata akalarsu zuwa ɓangaren Rasha.
A matsayinsa na shugaban ƙungiyar ƙasashen yammacin Afirka, Tinubu ya yi ƙoƙarin ganin ƙasashen Nijar da Mali da Bukina Faso sun koma tafarkin dimokuraɗiyya sai dai har yanzu abin ya ci tura.

Asalin hoton, Getty Images

Asalin hoton, Getty Images
Ruud van Nistelrooy na daf da zama sabon kociyan Leicester City mai buga Premier League.
Mai shekara 48, ɗan kasar Netherlands zai maye gurbin Steve Cooper wanda ta kora, bayan kwana 157 a kan aikin horar da ƙungiyar King Power.
Ranar Asabar Leicester City ta yi rashin nasara 2-1 a hannun Chelsea a Premier League karawar mako na 12.