Liverpool ta sa rai kan Frompong, Real Madrid na nazari kan Alexander Arnold

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool za ta yi zawarcin ɗan wasan Bayer Leverkusen da Netherlands Jeremie Frimpong, mai shekara 23, idan ɗan wasan Ingila Trent Alexander-Arnold, mai shekara 26, ya koma Real Madrid a bazarar mai zuwa. (Bild)
Liverpool da Real sun tattauna kan makomar Alexander-Arnold kafin wasan ƙungiyoyin biyu na gasar zakarun Turai a Anfield ranar Laraba. (Marca)
Ɗan wasan bayan Bournemouth ɗan ƙasar Hungary Milos Kerkez mai shekaru 21 yana jan hankalin Manchester United da Liverpool. (Sky)
Manchester United na nazari kan jerin sunayen ƴan wasan baya guda uku da suka haɗa da Ben Chilwell ɗan ƙasar Ingila da Chelsea mai shekara 27 da ɗan wasan Wolves Rayan Ait-Nouri ɗan ƙasar Algeria mai shekara 23 da kuma Alvaro Carreras ɗan ƙasar Sifaniya mai shekaru 21 da ya ke bugawa Benfica. (Rudy Galetti)
Chelsea na zawarcin ɗan wasan Ipswich ɗan ƙasar Ingila Liam Delap mai shekaru 21, amma tana iya fuskantar hamayya daga tsohuwar ƙungiyarsa Manchester City. (Football Insider)
Ɗan wasan Barcelona da Netherlands Frenkie de Jong, mai shekara 27, zai iya komawa Liverpool a bazara mai zuwa. (Fichajes)
Kocin Manchester City Pep Guardiola ya bayyana ɗan wasan tsakiyar Real Sociedad dan ƙasar Sifaniya Martin Zubimendi mai shekaru 25 da ɗan wasan Bayer Leverkusen ɗan ƙasar Jamus Florian Wirtz mai shekaru 21 da kuma ɗan ƙasar Uruguay Maximiliano Araujo na Sporting mai shekaru 24 a matsayin waɗanda zai yi zawarci a watan Janairu. (Fichajes)
Aston Villa na sha'awar daukar ɗan wasan tsakiya na Mainz da Jamus Nadiem Amiri mai shekaru 28. (Bild)
Manchester United da Manchester City da Liverpool na shirin kai ruwa rana kan ɗan wasan Atalanta da Brazil, Ederson, amma ba ƙaramin tayi ne zai ja hankalin ɗan wasan mai shekaru 25 ba. (Talk)
Fiorentina da Napoli na nazarin mika tayin kwantiragin aro kan ɗan wasan bayan Arsenal Jakub Kiwior amma da wuya kociyan Mikel Arteta ya bar ɗan ƙasar Poland ɗin mai shekara 24 ya bar Gunners a watan Janairu. (Tuttomercato)
Arsenal ta tattauna da Crystal palace kan yiwuwar siyan ɗan wasan tsakiya na Ingila Adam Wharton, sai dai ƙungiyar ta kudancin Landan ta ƙaƙabawa ɗan wasan mai shekaru 20 farashin Yuro miliyan 65. (Caught Offside)










