An gano maganin cutar asthma

Asalin hoton, Getty Images
Masu bincike a Burtaniya sun ce sun samu sabon maganin cutar asma na farko cikin shekara 50.
Binciken ya bayyana cewa maganin, mai suna ben-ralizu-mab, ya kasance mafi tasiri kan cutar kuma ba shi da wata mummunar illa.
Tawagar masu biniken da ke a King's College a birnin London ta bayyana maganin a matsayin babban lamari ga masu fama da cutar asma.
Amma dai, sun yi gargaɗin cewa ana buƙatar ci gaba da gwaji a kansa, gami da tantance ko tasirinsa ya daidaita da farashinsa.


