Leicester City za ta bai wa Nistelrooy aikin kociyanta

Asalin hoton, Getty Images
Ruud van Nistelrooy na daf da zama sabon kociyan Leicester City mai buga Premier League.
Mai shekara 48, ɗan kasar Netherlands zai maye gurbin Steve Cooper wanda ta kora, bayan kwana 157 a kan aikin horar da ƙungiyar King Power.
Ranar Asabar Leicester City ta yi rashin nasara 2-1 a hannun Chelsea a Premier League karawar mako na 12.
Nistelrooy zai horar da Leicester ne, sakamakon mako biyu da ya kammala aikin riƙon kwarya a Manchester United, bayan da aka kori Erik ten Hag cikin watan Oktoba.
Van Nistelrooy ya ja ragamar United, wadda ta yi nasara uku da canjaras ɗaya a matakin riƙon ƙwarya.
Ya kuma bar Old Trafford ne, sakamakon da sabon koci, Ruben Amorin ya ce ba zai yi aiki da ɗan kasar Netherlands ba.
Leicester tana ta 16 a kasan teburin Premier League da maki 10, bayan cin wasa biyu da canjaras huɗu aka doke ta wasa shida daga karawa 12.
Ranar Asabar 30 ga watan Nuwamba, Leicester za ta je Brentford, domin buga wasan mako na 13 a babbar gasar tamaula ta Ingila.










