Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 24/12/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 24/12/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Isiyaku Muhammed da Aisha Aliyu Jaafar

  1. An gurfanar da wanda ake da zargi da almundahanar taki a Kano

    EFCC

    Asalin hoton, @officialEFCC

    Hukumar EFCC ta gabatar da wani mutum mai suna Sanusi Hashim bisa zargin almundahanar taki ta naira miliyan 108.

    An gabatar da Hashim ne a babbar kotun tarayya da ke Zaria a gaban Mai shari'a Kabiru Dabo kan zargin rashawa, wanda ya saɓa da sashe na 293, wanda kuma ya cancani hukunci a ƙarƙashin sashe 294 na kundin laifuka.

    An zarge shi ne da karɓar naira miliyan 108 daga Ahmad Mohammad Liman da Bashiru Mohammad domin ya kawo musu taki, amma ya ƙi kai musu, zargin da ya ƙaryata.

    A ƙarshe Mai shari'a Dabo ya ɗage sauraron shari'ar zuwa ranar 10 ga Fabrairun 2025, sannan ya buƙaci a ajiye wanda ake ƙara a kurkuku.

  2. Ƴanbindiga sun ƙwace kayan abincin Kirsimeti a Kaduna

    Bindiga

    Asalin hoton, NPF

    Ƴanbindiga sun tare da ƙwace kayayyakin abinci da na sha da wani mutum ya sayo a kan babur a garin Gidan Abe da ke ƙaramar hukumar Kachia ta jihar Kaduna.

    Wani dattijon garin ne ya tabbatar wa jaridar Daily Trust hakan, inda ya ce lamarin ya auku ne a ranar Asabar da misalin ƙarfe biyar 5:23 na yamma.

    "Mutumin ya tafi sayo buhun shinkafa da sauran kayan abinci domin bikin Kirsimeti a garin Katari. Da yake dawowa ne a hanyarsa ta zuwa gida sai wasu ƴanbindiga a kan babura suka tare shi, suka ƙwace."

    Ƙoƙarin jin ta bakin kakakin rundunar ƴansandan jihar Kaduna, ASP Hassan Mansur bai kai ga nasara ba.

  3. Ba za mu rage farashin fetur ba sai tsohon kayanmu ya ƙare - IPMAN

    Fetur

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar dillalan man fetur ta Najeriya, IPMAN da kuma kamfanin mai na ƙasa wato NNPCL , sun ce za su ci gaba da sayar da man fetur a tsohon farashi har zuwa lokacin da tsohon kayan da suke da shi zai ƙare. Kamfanin na NNPCL dai ya ce a sabon farashin zai riƙa bai wa dillalan, man a kan naira 899 inda su kuma za su sayar a kan naira 935.

    Ƙungiyar dillalan man ta ce a yanzu haka tana ci gaba da tattaunawa da matatar Dangote domin ganin yadda za su soma ɗaukar man a sabon farashin, kamar Alhaji Salisu Ten-Ten, shugaban dillalan na shiyyar arewa maso yamma ya yi BBC bayani,

  4. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Talata daga nan sashen Hausa na BBC inda za mu riƙa kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙa shafukanmu na sadarwa domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da hotuna.

    Ku kasance tare da mu.