Nkunku na son sauya sheƙa, Arsenal na kwaɗayin Retegui

Asalin hoton, Getty Images
Wakilin ɗan wasan gaba a Chelsea Christopher Nkunku ya gabatarwa Barcelona tayi kan ɗan wasan asalin Faransa mai shekara 22. (Sport - in Spanish)
Kocin Manchester United Ruben Amorim daga Portugal na fuskantar matsin lamba kan ya dauki ɗan wasan gaba na Ingila Marcus Rashford mai shekara 27, koda kuwa rashin ɗan wasan zai iya haifar da rauni a daidaita matsayarsu kan cinikin 'yan wasa a watan Janairu. (ESPN)
Newcastle na iya duba tayi kan ɗan wasan Italiya mai shekara 24, Sandro Tonali a sabuwar kaka domin cimma dokokin cinikin 'yan wasa da riba, yayinda Juventus ke nuna kwaɗayinta. (Football Insider)
Bayern Munich na duba yiwuwar saye ɗan wasan Bundesliga a Borussia Dortmund, Jamie Gittens mai shekara 20. (Sky Germany)
Chelsea ta karbi tayi kan ɗan wasanta mai shekara 28, Ben Chilwell, wanda sau guda ya taka mata leda a wannan kakar. (Sun)
Arsenal ta tura wakilai domin sa ido kan ɗan wasan gaba a Atalanta mai shekara 25 asalin kasar Italiya, Mateo Retegui. (Talksport)
Rashin jituwa tsakanin kocin AC Milan, Paulo Fonseca da ɗan wasan Faransa mai tsaron baya, Theo Hernandez na iya sa ɗan wasan mai shekara 27 ya bar San Siro yayinda Real Madrid da Manchester United ke zawarcinsa. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Tottenham ta nuna kwaɗayinta kan ɗan wasan Atalanta da Ingila, Ben Godfrey mai shekara 26, a yarjejeniyar gajeren lokaci. (Football Insider)
Lille na iya katse kwantiragin ɗan wasan Faransa mai shekara 31 Samuel Umtiti, wanda tun watan Janairun 2024 bai yi wasa a saoda raunin da yake samu a gwiwa. (Fichajes - in Spanish), external
Duk da raɗe-raɗin da ake yaɗawa, ɗan wasan Liverpool Luis Diaz, mai shekara 27, na nan zama daram a Anfield, babu wani batun sauya sheka. (Sky Germany)










